Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Song-of-Solomon Chapter 1 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Song-of-Solomon 1) Waƙar Waƙoƙin Solomon. 2) Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi. 3) Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka! 4) Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka! 5) Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon. 6) Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa.’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina. 7) Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka? 8) Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya. 9) Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna. 10) ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja. 11) Za mu yi’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa. 12) Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi. 13) Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina. 14) Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi. 15) Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne. 16) Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce. 17) Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!