Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Job Chapter 23 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Job/23 1) Sa’an nan Ayuba ya amsa, 2) “Ko a yau, ina kuka mai zafi; hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi. 3) Da a ce na san inda zan same shi; da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama! 4) Zan kai damuwata wurinsa in yi gardama da shi. 5) Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini. 6) Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba. 7) Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa, kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada. 8) “Amma in na je gabas, ba ya wurin; in na je yamma, ba zan same shi ba. 9) Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa; sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa. 10) Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya. 11) Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba. 12) Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe. 13) “Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi? Yana yin abin da yake so. 14) Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini, kuma yana da sauran irinsu a ajiye. 15) Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa. 16) Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni. 17) Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!