Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Jeremiah Chapter 14 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Jeremiah/14 1) Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa, 2) “Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima. 3) Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe. 4) Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu. 5) Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa. 6) Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai suna haki kamar diloli; idanunsu sun kāsa gani saboda rashin makiyaya.” 7) Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi. 8) Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce? 9) Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato, kamar jarumi marar ƙarfin ceto? Kana a cikinmu, ya Ubangiji, da sunanka ake kiranmu; kada ka yashe mu! 10) Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.” 11) Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan. 12) Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.” 13) Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’” 14) Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. 15) Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su. 16) Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su. 17) “Ka yi musu wannan magana, “‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa. 18) In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’” 19) Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana. 20) Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi. 21) Saboda sunanka kada ka ƙi mu; kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka. Ka tuna da alkawarinka da mu kada ka tā da shi. 22) Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!