Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Genesis Chapter 10 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Genesis/10 1) Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet,’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi’ya’ya maza bayan ambaliyar. 2) ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras. 3) ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma. 4) ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. 5) (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.) 6) ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana. 7) ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan. 8) Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. 9) Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. 10) Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. 11) Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala 12) da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni. 13) Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, 14) Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa. 15) Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, 16) Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, 17) Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 18) Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu 19) har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha. 20) Waɗannan su ne’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu. 21) Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet,’ya’ya maza. Shem shi ne kakan’ya’yan Eber duka. 22) ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. 23) ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash. 24) Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber. 25) Aka haifa wa Eber’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan. 26) Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, 27) Hadoram, Uzal, Dikla, 28) Obal, Abimayel, Sheba, 29) Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan’ya’yan Yoktan maza ne. 30) Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu. 31) Waɗannan su ne’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu. 32) Waɗannan su ne zuriyar’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!