< मुकाशफ़ा 7 >
1 इसके बाद मैंने ज़मीन के चारों कोनों पर चार फ़रिश्ते खड़े देखे। वो ज़मीन की चारों हवाओं को थामे हुए थे, ताकि ज़मीन या समुन्दर या किसी दरख़्त पर हवा न चले।
Bayan wannan sai na ga mala'iku hudu suna tsaye bisa kusurwoyi hudu na duniya, suka rike iskoki hudu na duniya kamkam domin kada iska ta hura a kan duniya, a kan teku, ko wani itace.
2 फिर मैंने एक और फ़रिश्ते को, ज़िन्दा ख़ुदा की मुहर लिए हुए मशरिक़ से ऊपर की तरफ़ आते देखा; उसने उन चारों फ़रिश्तों से, जिन्हें ज़मीन और समुन्दर को तकलीफ़ पहुँचाने का इख़्तियार दिया गया था, ऊँची आवाज़ से पुकार कर कहा,
Sai na ga wani mala'ika na zuwa daga gabas, wanda yake da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya da mala'ikun nan hudu da aka basu dama su azabtar da duniya da teku:
3 “जब तक हम अपने ख़ुदा के बन्दों के माथे पर मुहर न कर लें, ज़मीन और समुन्दर और दरख़्तों को तकलीफ़ न पहुँचाना।”
“Kada ku azabtar da duniya, da teku, da itatuwa har sai mun sa hatimi bisa goshin bayin Allahnmu.”
4 और जिन पर मुहर की गई उनका शुमार सुना, कि बनी — इस्राईल के सब क़बीलों में से एक लाख चवालीस हज़ार पर मुहर की गई:
Sai naji yawan wadanda aka hatimce: 144, 000, wadanda aka hatimce daga kowacce kabilar mutanen Isra'ila:
5 यहुदाह के क़बीले में से बारह हज़ार पर मुहर की गई: रोबिन के क़बीले में से बारह हज़ार पर, जद के क़बीले में से बारह हज़ार पर,
dubu goma sha biyu aka hatimce daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad,
6 आशर के क़बीले में से बारह हज़ार पर, नफ़्ताली के क़बीले में से बारह हज़ार पर, मनस्सी के क़बीले में से बारह हज़ार पर,
dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa.
7 शमौन के क़बीले में से बारह हज़ार पर, लावी के क़बीले में से बारह हज़ार, इश्कार के क़बीले में से बारह हज़ार पर,
Dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka,
8 ज़बलून के क़बीले में से बारह हज़ार पर, युसूफ़ के क़बीले में से बारह हज़ार पर, बिनयामीन के क़बीले में से बारह हज़ार पर मुहर की गई।
dubu goma sha biyu daga kabilar zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, sai kuma dubu goma sha biyu daga kabilar Bilyaminu aka hatimce.
9 इन बातों के बाद जो मैंने निगाह की, तो क्या देखता हूँ कि हर एक क़ौम और क़बीला और उम्मत और अहल — ए — ज़बान की एक ऐसी बड़ी भीड़, जिसे कोई शुमार नहीं कर सकता, सफ़ेद जामे पहने और खजूर की डालियाँ अपने हाथों में लिए हुए तख़्त और बर्रे के आगे खड़ी है,
Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga wani babban taro wanda ba mai iya kirgawa daga kowacce al'umma, kabila, mutane da harsuna tsaye a gaban kursiyin da gaban Dan Ragon. Suna sanye da fararen tufafi da ganyen dabino a hannuwansu,
10 और बड़ी आवाज़ से चिल्ला कर कहती है, नजात हमारे ख़ुदा की तरफ़ से!“
kuma suna kira da murya mai karfi: “Ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune bisa kursiyi, da kuma Dan Ragon!”
11 और सब फ़रिश्ते उस तख़्त और बुज़ुर्गों और चारों जानदारों के पास खड़े है, फिर वो तख़्त के आगे मुँह के बल गिर पड़े और ख़ुदा को सिज्दा कर के
Dukan mala'iku suna tsaitsaye kewaye da kursiyin kuma kewaye da dattawan nan da kuma rayayyun halittun nan hudu, suka kwanta rib da ciki da fuskokinsu a gaban kursiyin. Suka yi sujada ga Allah,
12 कहा, आमीन! तारीफ़ और बड़ाई और हिक्मत और शुक्र और 'इज़्ज़त और क़ुदरत और ताक़त हमेशा से हमेशा हमारे ख़ुदा की हो! आमीन। (aiōn )
suna cewa, “Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!” (aiōn )
13 और बुज़ुर्गों में से एक ने मुझ से कहा, ये सफ़ेद जामे पहने हुए कौन हैं, और कहाँ से आए हैं?”
Sai daya daga cikin dattawan ya tambaye ni, “Su wanene wadannan, da suke sanye da fararen tufafi, kuma daga ina suka fito?”
14 मैंने उससे कहा, “ऐ मेरे ख़ुदावन्द, तू ही जानता है।” उसने मुझ से कहा, ये वही हैं; उन्होंने अपने जामे बर्रे के क़ुर्बानी के ख़ून से धो कर सफ़ेद किए हैं।
Sai nace masa, “Ya shugaba, “Ka sani,” sai ya ce mani, “Wadannan sune suka fito daga babban tsanani. Sun wanke tufafin su sun maida su farare cikin jinin Dan Ragon.
15 “इसी वजह से ये ख़ुदा के तख़्त के सामने हैं, और उसके मक़्दिस में रात दिन उसकी इबादत करते हैं, और जो तख़्त पर बैठा है, वो अपना ख़ेमा उनके ऊपर तानेगा।
Domin wannan dalili, suke gaban kursiyin Allah, kuma suna masa sujada dare da rana cikin haikalinsa. Shi wanda ke zaune bisa kursiyin zai zama runfa a bisan su.
16 इसके बाद न कभी उनको भूख लगेगी न प्यास और न धूप सताएगी न गर्मी।
Ba za su kara jin yunwa ba, ko kishin ruwa ba. Rana ba zata buge su ba, ko kowanne zafi mai kuna.
17 क्यूँकि जो बर्रा तख़्त के बीच में है, वो उनकी देखभाल करेगा, और उन्हें आब — ए — हयात के चश्मों के पास ले जाएगा और ख़ुदा उनकी आँखों के सब आँसू पोंछ देगा।”
Domin Dan Ragon dake tsakiyar kursiyin zai zama makiyayin su, kuma zai bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai, kuma Allah zai share dukan hawaye daga idanuwansu.”