< До римлян 12 >

1 Тож благаю вас, браття, через Боже милосердя, — повіддавайте ваші тіла на жертву живу, святу, приємну Богові, як розумну службу вашу,
Saboda haka, ina roƙonku,’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.
2 і не стосу́йтесь до віку цього, але перемініться відно́вою вашого розуму, щоб пізнати вам, що́ то є воля Божа, — добро, приємність та доскона́лість. (aiōn g165)
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke. (aiōn g165)
3 Через да́ну мені благода́ть кажу́ кожному з вас не ду́мати про себе більш, ніж належить ду́мати, але ду́мати скромно, у міру віри, як кожному Бог наділи́в.
Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.
4 Бо як в однім тілі маємо багато членів, а всі члени мають не однакове ді́яння,
Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,
5 так багато нас є одне тіло в Христі, а зосібна ми один о́дному члени.
haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.
6 І ми маємо різні да́ри, згідно з благода́ттю, да́ною нам: коли пророцтво — то виконуй його́ в міру віри,
Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa.
7 а коли служіння — будь на служі́ння, коли вчитель — на навча́ння,
In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar;
8 коли втіши́тель — на потіша́ння, хто подає — у простоті, хто голову́є — то з пильністю, хто милосе́рдствує — то з привітністю!
in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.
9 Любов нехай буде нелицемірна; нена́видьте зло та тулі́ться до доброго!
Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.
10 Любіть один о́дного братньою любов'ю; випереджа́йте один о́дного пошаною!
Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.
11 У ре́вності не лінуйтеся, духом палайте, служіть Господе́ві,
Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.
12 тіштесь надією, утиски терпіть, перебувайте в молитві,
Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
13 беріть у́діл у потребах святих, будьте гостинні до чужи́нців!
Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.
14 Благословляйте тих, хто вас переслідує; благословляйте, а не проклинайте!
Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
15 Тіштеся з тими, хто тішиться, і плачте з отими, хто плаче!
Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
16 Ду́майте між собою одна́ково; не величайтеся, але́ наслідуйте слухня́них; „не вважайте за мудрих себе!“
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.
17 Не платіть ніко́му злом за зло, дбайте про добре перед усіма́ людьми́!
Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.
18 Коли можливо, якщо це залежить від вас — живіть у мирі зо всіма́ людьми́!
Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.
19 Не мстіться самі, улю́блені, але дайте місце гніву Божому, бо написано: „Мені помста належить, Я відплачу́, говорить Господь“.
Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.
20 Отож, як твій ворог голодний, — нагодуй його; як він пра́гне, — напій його, бо, роблячи це, ти згорта́єш розпа́лене ву́гілля йому на голову.
A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”
21 Не будь переможений злом, але перемагай зло добром!
Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

< До римлян 12 >