< Ezgiler Ezgisi 3 >
1 Gece boyunca yatağımda Sevgilimi aradım, Aradım, ama bulamadım.
Dare farai a kan gadona na nemi wanda zuciyata take ƙauna; na neme shi amma ban same shi ba.
2 “Kalkıp kenti dolaşayım, Sokaklarda, meydanlarda sevgilimi arayayım” dedim, Aradım, ama bulamadım.
Zan tashi yanzu in zagaya gari, in ratsa titunansa da dandalinsa; zan nemi wanda zuciyata take ƙauna. Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba.
3 Kenti dolaşan bekçiler buldu beni, “Sevgilimi gördünüz mü?” diye sordum.
Masu tsaro suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce, “Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?”
4 Onlardan ayrılır ayrılmaz Sevgilimi buldum. Tuttum onu, bırakmadım; Annemin evine, Beni doğuran kadının odasına götürünceye dek.
Rabuwata da su ke nan sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, zuwa ɗakin wadda ta yi cikina.
5 Dişi ceylanlar, Yabanıl dişi geyikler üstüne Ant içiriyorum size, ey Yeruşalim kızları! Aşkımı ayıltmayasınız, uyandırmayasınız diye, Gönlü hoş olana dek.
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
6 Kimdir bu kırdan çıkan, Bir duman sütunu gibi, Tüccarın türlü türlü baharatıyla, Mür ve günnükle tütsülenmiş?
Wane ne wannan mai zuwa daga hamada kamar tunnuƙewar hayaƙi, cike da ƙanshin turaren mur da lubban da aka yi da kayan yajin’yan kasuwa?
7 İşte Süleyman'ın tahtırevanı! İsrailli yiğitlerden Altmış kişi eşlik ediyor ona.
Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, jarumawa sittin suke rakiya, zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila,
8 Hepsi kılıç kuşanmış, eğitilmiş savaşçı. Gecenin tehlikelerine karşı, Hepsinin kılıcı belinde.
dukansu suna saye da takobi dukansu ƙwararru ne a yaƙi, kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, a shirye don abubuwan bantsoro na dare.
9 Kral Süleyman tahtırevanı Lübnan ağaçlarından yaptı.
Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; ya yi shi da katako daga Lebanon.
10 Direklerini gümüşten, Tabanını altından yaptı. Koltuğu mor kumaşla kaplıydı. İçini sevgiyle döşemişti Yeruşalim kızları.
An yi sandunansa da azurfa, aka yi ƙasarsa da zinariya. An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya,’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna.
11 Dışarı çıkın, ey Siyon kızları! Düğününde, mutlu gününde Annesinin verdiği tacı giymiş Kral Süleyman'ı görün.
Fito, ku’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.