< Éxodo 2 >
1 Y un hombre de la casa de Leví tomó por esposa a una hija de Leví.
Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya,
2 Y ella engendró y dio a luz a un Hijo; y cuando vio que él era un niño hermoso, lo mantuvo en secreto durante tres meses.
ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku.
3 Y cuando ella ya no pudo mantenerlo en secreto, ella le hizo una canasta de tallos de plantas acuáticas, pegándola con tierra y brea para mantener el agua afuera; y colocando al bebé en él, lo puso entre las plantas al borde del Nilo.
Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin.
4 Y su hermana tomó su lugar a distancia para ver qué sería de él.
’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.
5 Y la hija de Faraón descendió al Nilo para tomar un baño, mientras sus mujeres caminaban a la orilla del río; y ella vio la canasta entre las plantas del río, y envió a su sirvienta para que se lo trajera.
Sai’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata.
6 Y al abrirlo, ella vio al niño, y él estaba llorando. Y ella tuvo compasión de él, y dijo: Este es uno de los hijos de los hebreos.
Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”
7 Entonces su hermana dijo a la hija de Faraón: ¿Puedo ir a buscarte a una de las hebreas para darle el pecho?
Sai’yar’uwarsa ta tambayi’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”
8 Y la hija de Faraón le dijo: Ve. Y la niña fue a buscar a la madre del niño.
Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron.
9 Y la hija de Faraón le dijo: Toma al niño y críalo, y yo te pagaré. Y la mujer tomó al niño y le dio leche de su pecho.
Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa.
10 Y cuando el niño era mayor, ella lo llevó a la hija de Faraón y él se convirtió en su hijo, y ella le dio el nombre de Moisés, porque, ella dijo, lo saqué del agua.
Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”
11 Cuando Moisés se hizo hombre, un día salió a su pueblo y vio lo duro que era su trabajo; y vio a un egipcio dando golpes a un hebreo, uno de su pueblo.
Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa.
12 Y volviéndose de aquí para allá, sin ver a nadie, mató al egipcio, cubriendo su cuerpo de arena.
Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi.
13 Y saliendo al otro día, vio a dos de los hebreos que peleaban, y dijo al que estaba equivocado: ¿Por qué peleas contra tu hermano?
Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
14 Y él dijo: ¿Quién te hizo gobernante y juez sobre nosotros? ¿Me vas a matar a mí como lo hiciste con el egipcio? Y Moisés tuvo miedo, y dijo: Está claro que el asunto ha salido a la luz.
Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”
15 Cuando Faraón tuvo noticias de esto, procuró matar a Moisés. Pero Moisés salió huyendo de Faraón a la tierra de Madián, y se sentó junto a un manantial de agua.
Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya.
16 Y el sacerdote de Madián tuvo siete hijas; y vinieron a buscar agua para el rebaño de su padre.
To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu.
17 Y los cuidadores de las ovejas subieron y las echaban de allí; pero Moisés se levantó y vino en su ayuda, y les dio de beber a las ovejas.
Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
18 Y cuando llegaron a Reuel su padre, él dijo: ¿Cómo es que has vuelto tan rápido hoy?
Da’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?”
19 Y ellas respondieron: Un egipcio vino en nuestra ayuda contra los cuidadores de ovejas, nos dio agua y se la dio al rebaño.
Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.”
20 Y dijo a sus hijas: ¿Dónde está? ¿Por qué has dejado ir al hombre? hazlo entrar y dale una comida.
Ya tambayi’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.”
21 Y Moisés estaba feliz de seguir viviendo con el hombre; y él dio su hija Séfora a Moisés.
Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da’yarsa Ziffora aure da Musa.
22 Y dio a luz un hijo, a quien nombró Gersón, porque dijo: He estado viviendo en tierra extraña.
Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.”
23 Y después de mucho tiempo, el rey de Egipto llegó a su fin; y los hijos de Israel lloraban en su dolor bajo el peso de su trabajo, y su clamor por ayuda llegó a oídos de Dios.
Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah.
24 Y al sonido de su lloro, vino a su mente el acuerdo que Dios había hecho con Abraham, Isaac y Jacob.
Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub.
25 Y los ojos de Dios se volvieron a los hijos de Israel y se dio cuenta de su condición.
Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su.