< 2 Corintios 12 >
1 Cierto no me es conveniente gloriarme; mas vendré a las visiones y a las revelaciones del Señor.
Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji.
2 Conozco un hombre en el Cristo, que hace catorce años (si en el cuerpo, no lo sé; si fuera del cuerpo, no lo sé: Dios lo sabe) fue arrebatado hasta el tercer cielo.
Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku.
3 Y conozco al tal hombre, (si en el cuerpo, o fuera del cuerpo, no lo sé: Dios lo sabe),
Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-
4 que fue arrebatado al paraíso, donde oyó palabras inefables que el hombre no puede decir.
an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi.
5 De éste tal me gloriaré, mas de mí mismo en nada me gloriaré, sino en mis flaquezas.
A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina.
6 Por lo cual si quisiere gloriarme (de estas cosas, ) no sería loco, porque diré la verdad; pero lo dejo, para que nadie piense de mí más de lo que en mí ve, u oye.
Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni.
7 Y para que la grandeza de las revelaciones no me exaltase descomedidamente, me es dado un aguijón en mi carne, un mensajero de Satanás que me abofetee, para que no me enaltezca sobremanera.
Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa.
8 Por lo cual tres veces he rogado al Señor, que se quite de mí.
Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan.
9 Y me ha dicho: Bástate mi gracia; porque (mi) potencia en la flaqueza se perfecciona. Por tanto, de buena gana me gloriaré de mis flaquezas, para que habite en mí la potencia de Cristo.
Amma ya ce mani, “Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika.” Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na.
10 Por lo cual me contento en las flaquezas, en las afrentas, en las necesidades, en las persecuciones, en las angustias por el Cristo; porque cuando soy flaco, entonces soy poderoso.
Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma.
11 He sido loco (en gloriarme); vosotros me constreñisteis; pues yo había de ser alabado de vosotros, porque en nada he sido menos que los grandiosos apóstoles, aunque nada soy.
Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne.
12 Con todo esto, las señales de apóstol han sido hechas entre vosotros en toda paciencia, en señales, y en prodigios, y en potencia.
Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka.
13 Porque ¿qué hay en que habéis sido menos que las otras Iglesias, sino en que yo mismo no os he sido carga? Perdonadme esta injuria.
Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin.
14 He aquí estoy aparejado para ir a vosotros la tercera vez, y no os seré gravoso; porque no busco vuestras cosas, sino a vosotros; porque no han de atesorar los hijos para los padres, sino los padres para los hijos.
Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi.
15 Pero yo de muy buena gana me desprenderé y seré totalmente desprendido por vuestras almas, aunque amándoos más, sea amado menos.
Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan?
16 Pero sea así, yo no os he agravado; sino que, como soy astuto, os he tomado por engaño.
Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara.
17 ¿Por ventura os he engañado por alguno de los que he enviado a vosotros?
Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku?
18 Rogué a Tito, y envié con él al hermano. ¿Os engañó por ventura Tito? ¿No hemos andado con un mismo Espíritu y por las mismas pisadas?
Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba?
19 ¿O pensáis aún que nos excusamos con vosotros? Delante de Dios en Cristo hablamos; mas todo, muy amados, por vuestra edificación.
Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi.
20 Porque temo que cuando llegare, no os halle tales como quiero, y yo sea hallado de vosotros cual no queréis; para que por ventura no haya entre vosotros contiendas, envidias, iras, disensiones, detracciones, murmuraciones, rumores, bandos;
Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi.
21 para que cuando volviere, no me humille Dios entre vosotros, y haya de llorar por muchos de los que antes habrán pecado, y no se han enmendado de la inmundicia y fornicación y deshonestidad que han cometido.
Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.