< Hechos 6 >
1 EN aquellos días, creciendo el número de los discípulos, hubo murmuración de los Griegos contra los Hebreos, de que sus viudas eran menospreciadas en el ministerio cotidiano.
A wadannan kwanaki, yawan almajiran ya ci gaba da ribanbanya, sai Yahudawan da suke zama a kasar Helanawa suka fara gunaguni game da Yahudawan Isra'ila, domin basu damu da gwamrayensu, wajen raba abinci da ake yi kullum.
2 Así que, los doce convocaron la multitud de los discípulos, y dijeron: No es justo que nosotros dejemos la palabra de Dios, y sirvamos á las mesas.
Manzannin nan sha biyu suka kira taron almajiran suka ce masu, ''Bai kamata mu bar maganar Allah mu shiga hidimar rabon abinci ba.
3 Buscad pues, hermanos, siete varones de vosotros de buen testimonio, llenos de Espíritu Santo y de sabiduría, los cuales pongamos en esta obra.
Don haka ku zabi 'yan'uwa maza daga cikinku, mutane bakwai wadanda a ke ganin su da daraja, cike da Ruhu da kuma hikima, wadanda za mu zaba suyi wannan hidima.
4 Y nosotros persistiremos en la oración, y en el ministerio de la palabra.
Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar.''
5 Y plugo el parecer á toda la multitud; y eligieron á Esteban, varón lleno de fe y de Espíritu Santo, y á Felipe, y á Prócoro, y á Nicanor, y á Timón, y á Parmenas, y á Nicolás, prosélito de Antioquía:
Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci.
6 A estos presentaron delante de los apóstoles, los cuales orando les pusieron las manos encima.
Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu.
7 Y crecía la palabra del Señor, y el número de los discípulos se multiplicaba mucho en Jerusalem: también una gran multitud de los sacerdotes obedecía á la fe.
Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya.
8 Empero Esteban, lleno de gracia y de potencia, hacía prodigios y milagros grandes en el pueblo.
Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a.
9 Levantáronse entonces unos de la sinagoga que se llama de los Libertinos, y Cireneos, y Alejandrinos, y de los de Cilicia, y de Asia, disputando con Esteban.
Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus.
10 Mas no podían resistir á la sabiduría y al Espíritu con que hablaba.
Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi.
11 Entonces sobornaron á unos que dijesen que le habían oído hablar palabras blasfemas contra Moisés y Dios.
Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, ''Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah.''
12 Y conmovieron al pueblo, y á los ancianos, y á los escribas; y arremetiendo le arrebataron, y [le] trajeron al concilio.
Sai suka zuga mutanen, har da dattawa da marubuta suka tunkari Istifanus, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa.
13 Y pusieron testigos falsos, que dijesen: Este hombre no cesa de hablar palabras blasfemas contra este lugar santo y la ley:
Suka kawo masu shaidar karya suka ce, ''Wannan mutumin har yanzu bai dena maganganun gaba akan wannan wuri mai tsarki da kuma shari'a ba.
14 Porque le hemos oído decir, que este Jesús de Nazaret destruirá este lugar, y mudará las ordenanzas que nos dió Moisés.
Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa.''
15 Entonces todos los que estaban sentados en el concilio, puestos los ojos en él, vieron su rostro como el rostro de un ángel.
Dukan wadanda suke zaune a majalisar suka zuba masa ido, sai suka ga fuskarsa kamar ta mala'ika.