< 1 Corintios 16 >

1 CUANTO á la colecta para los santos, haced vosotros también de la manera que ordené en las iglesias de Galacia.
Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi.
2 Cada primer día de la semana cada uno de vosotros aparte en su casa, guardando lo que por la bondad de Dios pudiere; para que cuando yo llegare, no se hagan entonces colectas.
A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba.
3 Y cuando habré llegado, los que aprobareis por cartas, á éstos enviaré que lleven vuestro beneficio á Jerusalem.
Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima.
4 Y si fuere digno el negocio de que yo también vaya, irán conmigo.
Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni.
5 Y á vosotros iré, cuando hubiere pasado por Macedonia, porque por Macedonia tengo de pasar:
Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya.
6 Y podrá ser que me quede con vosotros, ó invernaré también, para que vosotros me llevéis á donde hubiere de ir.
Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni.
7 Porque no os quiero ahora ver de paso; porque espero estar con vosotros algún tiempo, si el Señor lo permitiere.
Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda.
8 Empero estaré en Efeso hasta Pentecostés;
Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos.
9 Porque se me ha abierto puerta grande y eficaz, y muchos son los adversarios.
Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa.
10 Y si llegare Timoteo, mirad que esté con vosotros seguramente; porque la obra del Señor hace también como yo.
Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11 Por tanto, nadie le tenga en poco; antes, llevadlo en paz, para que venga á mí: porque lo espero con los hermanos.
Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa.
12 Acerca del hermano Apolos, mucho le he rogado que fuese á vosotros con los hermanos; mas en ninguna manera tuvo voluntad de ir por ahora; pero irá cuando tuviere oportunidad.
Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi.
13 Velad, estad firmes en la fe; portaos varonilmente, y esforzaos.
Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali.
14 Todas vuestras cosas sean hechas con caridad.
Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna.
15 Y os ruego, hermanos, (ya sabéis que la casa de Estéfanas es las primicias de Acaya, y que se han dedicado al ministerio de los santos, )
Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa,
16 Que vosotros os sujetéis á los tales, y á todos los que ayudan y trabajan.
kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu.
17 Huélgome de la venida de Estéfanas y de Fortunato y de Achâico: porque éstos suplieron lo que á vosotros faltaba.
Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku.
18 Porque recrearon mi espíritu y el vuestro: reconoced pues á los tales.
Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane.
19 Las iglesias de Asia os saludan. Os saludan mucho en el Señor Aquila y Priscila, con la iglesia que está en su casa.
Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji.
20 Os saludan todos los hermanos. Saludaos los unos á los otros con ósculo santo.
Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki.
21 La salutación de mí, Pablo, de mi mano.
Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna.
22 El que no amare al Señor Jesucristo, sea anatema. Maranatha.
Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo!
23 La gracia del Señor Jesucristo sea con vosotros.
Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku.
24 Mi amor en Cristo Jesús sea con todos vosotros. Amén. La primera á los Corintios fué enviada de Filipos con Estéfanas, y Fortunato, y Achâico, y Timoteo.
Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. [ Amin ].

< 1 Corintios 16 >