< Apocalipsis 12 >
1 Una gran señal apareció en el cielo: una mujer vestida con el sol y la luna debajo de sus pies, y en su cabeza una corona de 12 estrellas.
Aka ga wata babbar alama a sama: wata mace ta yi lullubi da rana, kuma wata na karkashin kafafunta; rawanin taurari goma sha biyu na bisa kanta.
2 Como estaba embarazada, gritaba con dolores de parto. Estaba atormentada por dar a luz.
Tana da ciki, tana kuma kuka don zafin nakuda - a cikin azabar haihuwa.
3 También se vio otra señal en el cielo: Ahí estaba un gran dragón rojo como fuego que tenía siete cabezas, diez cuernos, y siete diademas en sus cabezas.
Sai aka ga wata alama cikin sama: Duba! Akwai wani katon jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, sai kuma ga kambi guda bakwai bisa kawunansa.
4 Su cola arrastraba la tercera parte de las estrellas del cielo y las echó a la tierra. El dragón se paró delante de la mujer que estaba a punto de dar a luz, para devorar a su Hijo cuando diera a luz.
Wutsiyarsa ta share daya bisa uku na taurari a sama ta zubo su kasa. Diragon nan ya tsaya a gaban matar da ta kusan haihuwa, domin lokacin da ta haihu ya lankwame yaronta.
5 Dio a luz un Hijo varón, destinado a pastorear con vara de hierro a todas las naciones. Su Hijo fue arrebatado para Dios y para su trono.
Sai ta haifi da, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al'ummai da sandar karfe. Aka fizge yaron ta zuwa ga Allah da kursiyinsa,
6 La mujer huyó al desierto, donde tenía un lugar preparado por Dios, para que allí la sustenten durante 1.260 días.
matar kuwa ta gudu zuwa jeji inda Allah ya shirya mata domin a iya lura da ita kwanaki 1, 260.
7 Hubo una batalla en el cielo: Miguel y sus ángeles luchaban contra el dragón. Luchó el dragón y sus ángeles,
A lokacin sai yaki ya tashi a sama. Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da diragon, sai diragon da nasa mala'iku suka yake su su ma.
8 pero no prevaleció, ni se halló lugar para ellos en el cielo.
Amma diragon ba shi da isashen karfin da zai ci nasara. Don haka, shi da mala'ikunsa ba su kara samun wuri a sama ba.
9 Fue echado el gran dragón, la serpiente antigua, el llamado diablo y Satanás, el cual engaña al mundo entero. Fue lanzado a la tierra, y sus ángeles fueron echados con él.
Sai aka jefa katon diragon nan tare da mala'ikunsa kasa, wato tsohon macijin nan da ake kira Iblis ko Shaidan wanda ke yaudarar dukan duniya.
10 Entonces escuché una gran voz en el cielo que decía: ¡Ahora llegó la salvación, el poder y el reino de nuestro Dios, y la soberanía de su Cristo, porque fue echado el acusador de nuestros hermanos, el que los acusaba de día y de noche delante de nuestro Dios!
Sai na ji wata murya mai kara a sama: “Yanzu ceto ya zo, karfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa. Gama an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a kasa - shi da yake sarar su a gaban Allah dare da rana.
11 Ellos lo vencieron por medio de la sangre del Cordero y por la palabra de su testimonio. No apreciaron su vida aun frente a [la] muerte.
Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa.
12 Por tanto ¡alégrense, cielos, y los que moran en ellos! ¡Ay de la tierra y del mar, porque el diablo bajó a ustedes con gran furor al saber que tiene poco tiempo!
Don haka, yi farinciki, ya ku sammai da duk mazauna da ke cikinsu. Amma kaito ga duniya da teku saboda iblis ya sauko gare ku. Yana cike da mummunan fushi, domin ya san lokacin sa ya rage kadan.
13 Cuando el dragón vio que fue arrojado a la tierra, persiguió a la mujer que dio a luz al Varón.
Da diragon ya ga an jefar da shi kasa, sai ya fafari matar nan da ta haifi da namiji.
14 Pero a la mujer se [le] dieron las dos alas de la gran águila para que volara a su lugar en el desierto, donde es sustentada por tiempo, tiempos y medio tiempo, [lejos] de la presencia de la serpiente.
Amma aka ba matar nan fukafukai biyu na babbar gaggafa domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a jeji. A wannan wuri ne za a lura da ita na dan lokaci, da lokatai, da rabin lokaci - a lokacin da babu macijin.
15 La serpiente arrojó agua de su boca como un río tras la mujer para que fuera arrastrada por un río.
Macijin ya kwararo ruwa daga bakin sa kamar kogi, don ya kawo ambaliyar da zai kwashe ta.
16 Pero la tierra ayudó a la mujer, pues la tierra abrió su boca y tragó el río que el dragón arrojó de su boca.
Amma kasa ta taimaki matar. Kasa ta bude bakinta ta hadiye kogin da diragon ya kwararo daga bakinsa.
17 Entonces el dragón se enfureció contra la mujer, e hizo [la] guerra contra los demás de su descendencia, los cuales guardan los Mandamientos de Dios y tienen el testimonio de Jesús.
Sai diragon ya fusata da matar, sai ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu.