< San Lucas 4 >

1 Jesús regresó del Jordán lleno del Espíritu Santo y fue impulsado por el Espíritu a una región deshabitada
Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji
2 por 40 días para que fuera tentado por el diablo. Nada comió en aquellos días. Cuando se acabaron tuvo hambre.
kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin.
3 Entonces el diablo le dijo: Ya que eres Hijo de Dios, dí a esta piedra que se convierta en pan.
Shaidan ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa.”
4 Jesús le respondió: Está escrito: No solo de pan vivirá el hombre.
Yesu ya amsa masa, “A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'”
5 Lo subió y le mostró en un momento todos los reinos de la tierra habitada.
Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci.
6 Y el diablo le dijo: Te daré toda esta autoridad y el esplendor de ellos, pues me fue entregada, y a quien quiera se la doy.
Shaidan ya ce masa, “Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama.
7 Si Tú te postras ante mí, será toda tuya.
Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka.”
8 Jesús respondió: Está escrito: Ante el Señor tu Dios te postrarás y a Él solo servirás.
Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa.”
9 Entonces lo llevó a Jerusalén, lo puso en pie sobre el pináculo del Templo y le dijo: Ya que eres Hijo de Dios, lánzate de aquí abajo,
Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan.
10 porque está escrito: A sus ángeles mandará para que te guarden.
Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,'
11 Y: En [las] manos te sostendrán para que tu pie no tropiece en piedra.
kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.”
12 Jesús le respondió: Está dicho: No tentarás al Señor tu Dios.
Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'”
13 Y cuando acabó toda tentación, el diablo se retiró de Él hasta un tiempo oportuno.
Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci.
14 Jesús regresó a Galilea con el poder del Espíritu, y [la] noticia con respecto a Él salió por toda la región alrededor.
Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin.
15 Enseñaba en las congregaciones de ellos y era alabado por todos.
Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
16 Fue a Nazaret, donde fue criado. El día sábado entró en la congregación según la costumbre y se levantó a leer.
Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
17 Se le dio un rollo del profeta Isaías. Lo desenvolvió y halló el lugar donde está escrito:
An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
18 [El] Espíritu del Señor está sobre Mí, porque me ungió para anunciar Buenas Noticias a [los] pobres. Me envió a proclamar libertad a cautivos, y restauración de vista a ciegos, a enviar en libertad a oprimidos,
“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
19 A proclamar el año aceptable del Señor.
in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
20 Envolvió el rollo, lo devolvió al asistente y se sentó. Los ojos de todos en la congregación estaban fijos en Él.
Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
21 Y les dijo: Hoy se cumplió esta Escritura en sus oídos.
Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”
22 Todos daban testimonio de Él y se maravillaban de las palabras de gracia que salían de su boca. Se preguntaban: ¿No es Éste [el] hijo de José?
Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?”
23 Y les respondió: Sin duda ustedes me dirán este refrán: Médico, cúrate a ti mismo. Todas las cosas que oímos que se hicieron en Cafarnaúm, hazlas también aquí en tu tierra.
Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'”
24 En verdad les digo que ningún profeta es bienvenido en su tierra.
Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa.
25 Ciertamente les digo que muchas viudas había en Israel en los días de Elías, cuando el cielo fue cerrado por tres años y seis meses, mientras hubo una gran hambruna en toda la tierra.
Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar.
26 Pero a ninguna de ellas fue enviado Elías, sino a una mujer viuda en Sarepta de Sidón.
Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon.
27 Muchos leprosos había en Israel en [el ]tiempo del profeta Eliseo, y ninguno de ellos fue limpiado, sino Naamán el sirio.
Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai.
28 Al oír esto todos en la congregación se llenaron de ira.
Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka.
29 Se levantaron, lo sacaron fuera de la ciudad y lo llevaron para despeñarlo desde [la] cumbre de la montaña sobre la cual fue edificada la ciudad de ellos.
Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa.
30 Pero Él pasó por en medio de ellos y salió.
Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa.
31 Descendió a la ciudad de Cafarnaúm en Galilea y los sábados les enseñaba.
Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a.
32 Se asombraban de su enseñanza, porque su Palabra era con autoridad.
Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko.
33 En la congregación estaba un hombre que tenía un espíritu demoníaco impuro, quien clamó a gran voz:
A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya,
34 ¡Ah! ¿Qué [nos pasa] a nosotros y a Ti, Jesús nazareno? ¿Viniste a destruirnos? ¡Sé Quién eres: El Santo de Dios!
“Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!”
35 Jesús lo reprendió: ¡Enmudece y sal de él! Y cuando lo lanzó en medio, sin hacerle daño el demonio salió de él.
Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba.
36 Todos se asombraron y discutían entre ellos: ¿Qué Palabra es ésta, que con autoridad y poder manda a los espíritus impuros, y salen?
Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, “Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita.”
37 Su fama se difundía por todo lugar de la región circunvecina.
Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin.
38 Cuando salió de la congregación, entró en la casa de Simón. La suegra de Simón estaba atormentada por una gran fiebre y le rogaron por ella.
Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta.
39 Se inclinó hacia ella, reprendió la fiebre y la sanó. De inmediato, se levantó y les servía.
Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima.
40 Cuando el sol bajaba, todos los que tenían enfermos de diversas dolencias los llevaban a Él. Imponía las manos sobre cada uno de ellos y los sanaba.
Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su.
41 También salían demonios de muchos que gritaban: ¡Tú eres el Hijo de Dios! Pero los reprendía y no les permitía hablar esto, porque sabían que Él era el Cristo.
Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu.
42 Cuando amaneció, salió a un lugar solitario, pero la multitud lo buscaba. Fueron a Él y lo detenían para que no se alejara de ellos.
Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su.
43 Pero Él les dijo: Me es necesario proclamar las Buenas Noticias del reino de Dios también a las otras ciudades, pues para esto fui enviado.
Amma ya ce masu, “Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan.”
44 Y predicaba en las congregaciones de Judea.
Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.

< San Lucas 4 >