< Juan 5 >

1 Después de esto Jesús subió a Jerusalén a una fiesta de los judíos.
Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima.
2 Junto a la puerta de La Oveja en Jerusalén, había un estanque llamado en hebreo Betzata que tenía cinco patios cubiertos
To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar.
3 donde muchos enfermos, ciegos, cojos y paralíticos estaban tendidos.
Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin [suna jira a dama ruwan].
4
Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita.
5 Allí estaba un hombre que tenía 38 años enfermo.
Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas.
6 Cuando Jesús lo vio tendido y supo cuánto tiempo tenía enfermo, le preguntó: ¿Quieres ser sano?
Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, “Ko kana so ka warke?”
7 El enfermo le respondió: Señor, no tengo alguien que me baje al estanque cuando se agita el agua. Mientras voy, otro baja antes de mí.
Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, “Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni.”
8 Jesús le dijo: ¡Levántate, alza tu camilla y anda!
Yesu ya ce masa,” Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi.”
9 De inmediato el hombre fue sanado, alzó su camilla y andaba. Ese día era sábado.
Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce.
10 Entonces los judíos decían al que fue sanado: [Hoy] es sábado. No es legal que cargues tu camilla.
Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba.”
11 Pero él les respondió: El que me sanó, me dijo: Alza tu camilla y anda.
Sai ya amsa ya ce, “Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi.”
12 Le preguntaron: ¿Quién te dijo: Alza y anda?
Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?”
13 Pero el hombre no sabía quien lo sanó, porque Jesús se apartó de [la] multitud que estaba en el lugar.
Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
14 Después de esto Jesús lo halló en el Templo y le dijo: Fuiste sanado. Ya no peques más para que no te venga algo peor.
Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”
15 El hombre fue e informó a los judíos que Jesús lo sanó.
Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16 Por esto los judíos perseguían a Jesús, porque hacía esto el sábado.
To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
17 Pero Él les decía: Mi Padre hasta ahora trabaja y Yo también.
Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”
18 Por esto los judíos más procuraban matarlo, porque no solo quebrantaba el sábado, sino también llamaba a Dios su propio Padre y se igualaba a Dios.
Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
19 Jesús declaró: En verdad, en verdad les digo: El Hijo nada puede hacer por iniciativa propia, sino lo que ve que el Padre hace. Lo que el Padre hace, también lo hace el Hijo.
Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
20 Porque el Padre ama al Hijo y le muestra todo lo que Él hace. Y mayores obras le mostrará para que ustedes se maravillen.
Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki.
21 Porque como el Padre resucita a los muertos y les da vida, así también el Hijo da vida a los que quiere.
Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa.
22 Porque ni aun el Padre juzga a alguno, sino todo el juicio encomendó al Hijo,
Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
23 para que todos honren al Hijo como honran al Padre. El que no honra al Hijo, no honra al Padre Quien lo envió.
domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
24 En verdad, en verdad les digo: El que oye mi Palabra y cree al que me envió, tiene vida eterna. No va a juicio, sino pasa de la muerte a la vida. (aiōnios g166)
Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai. (aiōnios g166)
25 En verdad, en verdad les digo: Viene una hora y ya llegó, cuando los muertos oirán la voz del Hijo de Dios, y los que [la] oigan vivirán.
Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.
26 Porque como el Padre tiene vida en Él mismo, así también concedió al Hijo que tuviera vida en Él mismo.
Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa.
27 Le dio autoridad para juzgar, porque es el Hijo del Hombre.
Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum.
28 No se maravillen de esto, porque viene la hora cuando todos los que están en los sepulcros oirán su voz.
Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa,
29 Los que hicieron lo bueno saldrán a resurrección de vida, pero los que hicieron lo malo, a resurrección de juicio.
su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci.
30 Yo nada puedo hacer por iniciativa propia. Como oigo, juzgo. Mi juicio es justo, porque no busco mi voluntad, sino la voluntad de Quien me envió.
Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
31 Si Yo doy testimonio con respecto a Mí mismo, mi testimonio no es verdadero.
Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba.
32 Otro es quien da testimonio de Mí, y sé que su testimonio es verdadero.
Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce.
33 Ustedes enviaron [mensajeros] a Juan, y [él] dio testimonio de la Verdad.
Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya.
34 Pero Yo no recibo el testimonio de parte de un hombre. Digo esto para que ustedes sean salvos.
Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto.
35 Aquél era la antorcha que ardía y alumbraba, y ustedes quisieron regocijarse en su luz por un tiempo.
Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan.
36 Pero Yo tengo un testimonio mayor que el de Juan, porque hago las obras que el Padre me mandó que hiciera, las cuales dan testimonio de que el Padre me envió.
Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni.
37 El Padre que me envió también dio testimonio de Mí. Ustedes jamás oyeron su voz, ni vieron su apariencia,
Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa.
38 ni su Palabra permanece en ustedes, porque ustedes no creen en el que Él envió.
Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
39 [Ustedes] escudriñan las Escrituras porque les parece que allí tienen vida eterna. Ellas son las que dan testimonio de Mí. (aiōnios g166)
Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. (aiōnios g166)
40 ¡Y ustedes no quieren venir a Mí para que tengan vida!
kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai.
41 No recibo alabanzas de hombres.
Ba na karbar yabo daga wurin mutane,
42 Pero sé que ustedes no tienen el amor de Dios.
amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku.
43 Yo vine en Nombre de mi Padre, y no me reciben. Si otro viene en su propio nombre, lo recibirían.
Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi.
44 ¿Cómo pueden creer ustedes quienes reciben honor los unos de los otros, y no buscan el honor del único Dios?
Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah?
45 No piensen que Yo los acusaré delante del Padre. Los acusa Moisés, en quien ustedes esperan.
Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa.
46 Porque si creyeran a Moisés, me creerían a Mí, porque él escribió con respecto a Mí.
Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni.
47 Pero si no creen sus escritos, ¿cómo creerán mis Palabras?
Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

< Juan 5 >