< Deuteronomio 4 >

1 Ahora pues, oh Israel, escucha los Estatutos y Ordenanzas que les enseño para que los practiquen a fin de que vivan y entren a tomar posesión de la tierra que Yavé, el ʼElohim de sus antepasados, les da.
To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku.
2 Nada añadirán a la Palabra que yo les mando ni de ella quitarán, para que guarden los Mandamientos de Yavé su ʼElohim que yo les ordeno.
Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku.
3 Los ojos de ustedes vieron lo que Yavé hizo en el caso de Baal-peor, cómo Yavé su ʼElohim destruyó de entre ustedes a todos los hombres que siguieron a Baal-peor.
Da idanunku, kun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-Feyor. Yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka waɗansu daga cikinku waɗanda suka yi wa Ba’al-Feyor sujada,
4 Pero ustedes, que se aferraron a Yavé su ʼElohim están todos vivos hoy.
Amma ku da kuka manne ga Ubangiji Allahnku, kuna da rai har wa yau.
5 Miren, yo les enseñé Estatutos y Ordenanzas, tal como Yavé mi ʼElohim me mandó, para que hagan así en la tierra a donde van a entrar a poseerla.
Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki.
6 Obsérvenlos y practíquenlos, pues esta es su sabiduría y su entendimiento a la vista de las naciones, las cuales oirán todos estos Estatutos y dirán: ¡En verdad esta gran nación es un pueblo sabio y entendido!
Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al’ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa’ad da al’ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, “Ba shakka, wannan babbar al’umma tana da hikima da ganewa.”
7 Pues ¿cuál nación hay tan grande que tenga ʼelohim tan cerca de ella, como Yavé nuestro ʼElohim está siempre cuando lo invocamos?
Wace al’umma ce mai girma haka wadda allolinta take kusa da su yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu a duk sa’ad da muka yi addu’a gare shi?
8 ¿Y cuál nación hay tan grande que tenga Estatutos y Ordenanzas tan justos como toda esta Ley que hoy presento ante ustedes?
Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?
9 Por tanto, guárdate y guarda tu alma con diligencia. No olvides las cosas que vieron tus ojos, ni se aparten de tu corazón en todos los días de tu vida. Las enseñarás a tus hijos y a tus nietos.
Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga’ya’yanku, da’ya’yan’ya’yanku.
10 El día cuando estuviste delante de Yavé tu ʼElohim en Horeb, cuando Yavé me dijo: Congrégame al pueblo y haré que oigan mis Palabras para que aprendan a temerme todos los días que vivan sobre esta tierra, y las enseñen a sus hijos.
Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga’ya’yansu.”
11 Se acercaron y permanecieron al pie de la montaña mientras la montaña ardía en fuego hasta el centro del cielo, en medio de oscuridad, nubes y densa niebla.
Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutse yayinda yana cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma baƙin gizagizai da kuma baƙin duhu.
12 Yavé les habló desde en medio del fuego. Ustedes oían el sonido de palabras, pero no percibían figura alguna, sino una voz.
Sai Ubangiji ya yi magana daga wutar. Kuka ji furcin kalmomin, amma ba ku ga siffar kome ba, sai dai murya kaɗai kuka ji.
13 Él mismo les anunció su Pacto, el cual les mandó observar: los Diez Mandamientos que escribió sobre dos tablas de piedra.
Ya furta alkawarinsa gare ku, Dokoki Goma, waɗanda ya umarce ku ku bi, ya kuma rubuta su a alluna biyu.
14 En aquel tiempo Yavé me mandó enseñarles los Estatutos y Ordenanzas para que los practiquen en la tierra a donde pasan para heredarla.
Sa’an nan Ubangiji ya umarce ni a wannan lokaci, in koya muku ƙa’idodi da dokokin da za ku bi a ƙasar da kuke hayewa Urdun don mallake.
15 Así que guárdense cuidadosamente, ya que ninguna forma vieron el día cuando Yavé les habló en Horeb desde en medio del fuego,
Ba ku ga wata siffa a ranar da Ubangiji ya yi magana da ku a Horeb daga wuta ba. Saboda haka ku lura da kanku sosai,
16 no sea que se corrompan y se hagan escultura de imagen en la forma de cualquier figura con semejanza de hombre o de mujer,
don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace,
17 de bestia que está en la tierra, de ave que vuela por el cielo,
ko a kamannin wata dabba a duniya, ko na wani tsuntsun da yake tashi a sama,
18 de reptil que se arrastra por el suelo, o de pez que nada en las aguas debajo de la tierra.
ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi.
19 No sea que, al levantar tus ojos al cielo y al ver el sol, la luna y las estrellas, toda la hueste del cielo, te desvíes y te postres ante ellos y les rindas culto. Porque Yavé tu ʼElohim los concedió a todos los pueblos debajo de todo el cielo.
Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama.
20 Yavé los tomó a ustedes y los sacó del horno de hierro de Egipto para que sean el pueblo de su herencia, como son hoy.
Amma ku, Ubangiji ya ɗauke ku, ya fid da ku daga matuya mai narken ƙarfe, wato, daga Masar, domin ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.
21 Yavé se mostró enojado contra mí por causa de ustedes, y juró que no pasaría el Jordán ni entraría en la buena tierra que Yavé su ʼElohim les da como heredad.
Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, ya kuma yi rantsuwa cewa ba zan haye Urdun, in shiga ƙasan nan mai kyau da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo ba.
22 Así que yo moriré en esta tierra. No pasaré el Jordán, pero ustedes pasarán y poseerán esa buena tierra.
Zan mutu a wannan ƙasa; ba zan haye Urdun ba; amma kuna gab da ƙetarewa, ku mallaki wannan ƙasa mai kyau.
23 Por tanto, guárdense para que no olviden el Pacto que Yavé su ʼElohim hizo con ustedes, y se hagan escultura, imagen de todo lo que les prohibió Yavé su ʼElohim.
Ku yi hankali kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku; kada fa ku yi wa kanku gunki a kamannin wani abin da Ubangiji Allahnku ya hana.
24 Porque Yavé su ʼElohim es fuego consumidor, ʼElohim celoso.
Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai ƙuna, Allah ne mai kishi.
25 Cuando engendren hijos y nietos y envejezcan en la tierra, si se depravan, hacen escultura, imagen de cualquier cosa y hacen lo malo ante Yavé su ʼElohim y lo irritan,
Bayan kun haifi’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi.
26 hoy yo llamo al cielo y la tierra como testigos contra ustedes con respecto a que pronto perecerán en la tierra hacia la cual cruzan el Jordán para poseerla. No prolongarán sus días en ella, sino serán absolutamente destruidos.
Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf.
27 Yavé los esparcirá entre los pueblos, y serán pocos en número entre las naciones a las cuales Yavé los llevará.
Ubangiji zai watsar da ku a cikin mutane, ɗan kaɗan ne kaɗai za su ragu a cikin al’umman da Ubangiji zai kai ku.
28 Allí servirán a ʼelohim hechos por manos humanas, de palo y de piedra, que no ven, ni oyen, ni comen, ni olfatean.
A can za ku bauta wa allolin da mutum ya yi, na itace da dutse da ba sa gani, ba sa ji, ba sa ci, ba kuma iya sansanawa.
29 Pero desde allí buscarás a Yavé tu ʼElohim y lo hallarás, si lo buscas con todo tu corazón y toda tu alma.
Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi.
30 Cuando estés en angustia y todas estas cosas lleguen sobre ti en los últimos días, entonces regresarás a Yavé tu ʼElohim y escucharás su voz.
Sa’ad da kuke cikin wahala saboda waɗannan abubuwan da suka same ku nan gaba, to, sai ku juyo ga Ubangiji Allahnku, ku kuma yi masa biyayya.
31 Porque Yavé tu ʼElohim es misericordioso, no te abandonará, ni te destruirá, ni olvidará el Pacto que les juró a tus antepasados.
Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba.
32 Pues pregunta ahora con respecto a los días pasados, desde el día cuando ʼElohim creó al hombre sobre la tierra y desde un extremo del cielo hasta el otro: ¿Sucedió alguna vez o se oyó jamás cualquier cosa como ésta?
Ku bincika dukan tarihi mana, tun daga lokacin da Allah ya halicci mutane a cikin duniya har yă zuwa yanzu; ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?
33 ¿Alguna vez otro pueblo oyó la voz de ʼElohim que habla en medio del fuego, como tú la oíste y seguiste vivo?
Akwai waɗansu mutanen da suka taɓa jin muryar Allah yana magana daga wuta, kamar yadda kuka ji har suka rayu?
34 ¿O intentó jamás un ʼelohim venir a tomar para él una nación de entre otra, con pruebas, señales y prodigios, con guerra, mano poderosa y brazo extendido, y con grandes portentos como todo lo que hizo con ustedes Yavé su ʼElohim delante de sus ojos en Egipto?
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?
35 A ti te fue mostrado para que sepas que Yavé es ʼElohim, y no hay otro fuera de Él.
An nuna muku dukan waɗannan abubuwa saboda ku san cewa Ubangiji, shi ne Allah; ban da shi, babu wani.
36 Desde el cielo te permitió oír su voz para instruirte y sobre la tierra te permitió ver su gran fuego. Oíste sus palabras desde en medio del fuego.
Daga sama ya sa kuka ji muryarsa, don yă hore ku. A duniya ya nuna muku wutarsa mai girma, kuka kuma ji kalmominsa daga wuta.
37 Porque amó a tus antepasados y escogió a su descendencia después de ellos, ʼElohim personalmente te sacó de Egipto por medio de su gran poder,
Domin ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓi zuriyarsu a bayansu, ya fitar da ku daga Masar ta wurin kasancewarsa da kuma ƙarfinsa mai girma,
38 y expulsó de delante de ti a naciones grandes y más poderosas que tú para introducirte y darte en heredad la tierra de ellos, como sucede hoy.
don yă fitar da ku a gaban al’ummai da suka fi ku girma da kuma ƙarfi, ya kawo ku cikin ƙasarsu, don yă ba ku ita ta zama gādonku, kamar yadda yake a yau.
39 Por tanto, reconoce hoy y reflexiona en tu corazón que Yavé es ʼElohim arriba en el cielo y abajo en la tierra, y que no hay otro.
Ku sani, ku kuma riƙe a zuciya a wannan rana, cewa Ubangiji shi ne Allah a sama da kuma a ƙasa. Babu wani kuma.
40 Guarda, pues, sus Estatutos y Mandamientos que yo te ordeno hoy para que te vaya bien, a ti y a tus hijos, y prolongues tus días sobre la tierra que Yavé tu ʼElohim te da para siempre.
Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.
41 Entonces Moisés apartó tres ciudades al otro lado del Jordán, hacia el nacimiento del sol,
Sa’an nan Musa ya keɓe birane uku gabas da Urdun,
42 para que huya allí el homicida que mate a su prójimo sin intención, y sin aborrecerlo antes. Al huir a cualquiera de estas ciudades podrá salvar su vida.
waɗanda duk wanda ya yi kisankai, in ba da gangan ba ne ya kashe maƙwabcinsa, wanda babu ƙiyayya tsakaninsu a dā, zai iya gudu zuwa. Zai iya gudu zuwa cikin ɗaya daga waɗannan birane, yă tsira da ransa.
43 a Beser en la llanura del desierto, para los rubenitas, a Ramot en Galaad para los gaditas, y a Golán en Basán para los de Manasés.
Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.
44 Esta es la Ley que Moisés expuso ante los hijos de Israel.
Wannan ita ce dokar da Musa ya sa a gaban Isra’ilawa.
45 Estos son los Testimonios, Estatutos y Ordenanzas que Moisés promulgó a los hijos de Israel cuando salieron de Egipto,
Waɗannan su ne farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Musa ya ba su, sa’ad da suka fito daga Masar.
46 al otro lado del Jordán, en el valle que está frente a Bet-peor, en la tierra de Sehón, rey de los amorreos, que habitaba en Hesbón, al cual Moisés y los hijos de Israel derrotaron después que salieron de Egipto.
Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar.
47 Poseyeron esta tierra, así como la tierra de Og, rey de Basán, dos reyes amorreos que estaban al otro lado del Jordán, hacia el oriente,
Suka mallaki ƙasarsa da kuma ƙasar Og sarkin Bashan, sarakuna biyu na Amoriyawa, gabas da Urdun.
48 desde Aroer, que está junto a la ribera del arroyo Arnón, hasta la Montaña de Sion, que es Hermón,
Wannan ƙasa ta tashi daga Arower a kewayen Kwarin Arnon zuwa Dutsen Siyon (wato, Hermon),
49 con todo el Arabá al otro lado del Jordán, hacia el oriente, hasta el mar del Arabá, al pie de las laderas de la montaña Pisga.
ya kuma haɗa da dukan Araba gabas da Urdun, har zuwa tekun Araba a gindin gangaren Fisga.

< Deuteronomio 4 >