< Colosenses 4 >
1 Los señores traten con justicia y equidad a sus esclavos. Sepan que también ustedes tienen [al] Señor en [el] cielo.
Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama.
2 Perseveren en la conversación con Dios y velen en ella con acción de gracias.
Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya.
3 Al mismo tiempo hablen con Dios también por nosotros, para que Dios nos abra una puerta de proclamación a fin de anunciar el misterio de Cristo, por el cual fui encadenado,
Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka.
4 para que lo proclame como debo hacerlo.
Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada.
5 Vivan con sabiduría en relación con los de afuera y aprovechen bien el tiempo.
Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci.
6 La palabra de ustedes sea siempre con gracia, sazonada con sal para que sepan cómo les conviene responder.
Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum.
7 Todas las cosas con respecto a mí se las informará Tíquico, el hermano amado, fiel ministro y consiervo en [el] Señor,
Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji.
8 a quien les envié para que conozcan nuestra situación y consuele sus corazones.
Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku.
9 [También les envié] a Onésimo, el fiel y amado hermano, quien es de ustedes. [Ellos] les informarán todas las cosas de aquí.
Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan.
10 Aristarco, mi compañero de prisión, los saluda y Marcos, el primo de Bernabé, con respecto a quien les dí mandamientos. Si los visita, recíbanlo.
Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi),
11 [También los saluda] Jesús, el llamado Justo. Ellos son colaboradores conmigo en el reino de Dios y me consolaron. Son judíos.
da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni.
12 Los saluda Epafras, quien es de ustedes y esclavo de Cristo, y se esfuerza siempre por ustedes en toda [la] voluntad de Dios.
Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah.
13 Porque doy testimonio de que él tiene mucha aflicción por ustedes, y por los que están en Laodicea y en Hierápolis.
Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis.
14 Los saluda Lucas, el médico amado, y Demas.
Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku.
15 Saluden a los hermanos que están en Laodicea, a Ninfa y a la iglesia de la casa de ella.
Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta.
16 Cuando esta epístola sea leída por ustedes, permitan que también se lea en la iglesia de Laodicea, y que ustedes también lean la de Laodicea.
Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya.
17 Digan a Arquipo: Considera el ministerio que recibiste del Señor, para que lo cumplas.
Ku gaya wa Arkibas, “Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi.”
18 El saludo de mi mano, de Pablo. Recuerden mis cadenas. La gracia sea con ustedes.
Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.