< 1 Timoteo 5 >

1 No reprendas al anciano, sino exhórtalo como a un padre, a los más jóvenes, como a hermanos,
Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa.
2 a las ancianas, como a madres, a las más jóvenes, como a hermanas, con toda pureza.
Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki.
3 Honra a [las ]viudas, las realmente viudas.
Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske.
4 Si alguna viuda tiene hijos o nietos, aprendan primero a mostrar piedad hacia su propia familia, y a dar recompensa a los progenitores, porque esto es agradable delante de Dios.
Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka.
5 Sin embargo, [honra a] la que es realmente viuda y quedó sola, [que] fijó su esperanza en Dios, y persevera en las súplicas y en las conversaciones con Dios de noche y de día.
Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana.
6 Pero la que vive entregada a los placeres vanos, aunque vive, murió.
Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye.
7 Manda también estas cosas para que sean irreprochables,
Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi.
8 porque si alguno no provee para los suyos, y especialmente para los de su familia, negó la fe y es peor que un incrédulo.
Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi.
9 Sea incluida en la lista [la] viuda no menor de 60 años que fue esposa de un solo esposo,
Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya.
10 aprobada en buenas obras: si crió hijos, si mostró hospitalidad, si lavó [los ]pies de santos, si socorrió a afligidos y si siguió de cerca toda buena obra.
A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki.
11 Pero no incluyas viudas más jóvenes porque cuando sean impulsadas por deseos que están en conflicto con el afecto a Cristo, quieren casarse
Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure.
12 y tienen acusación. Quebrantaron la primera promesa.
Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari.
13 Al mismo tiempo también aprenden a ser ociosas y vagan de casa en casa. Y no solo ociosas, sino también chismosas y entremetidas, pues hablan las cosas que no deben.
Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba.
14 Por tanto deseo que las más jóvenes se casen, críen hijos, manejen sus casas y no den al adversario ocasión de reproche.
Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta.
15 Porque algunas ya se extraviaron tras Satanás.
Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan.
16 Si algún creyente tiene viudas, manténgalas, y no se cargue a la iglesia, a fin de que ayude a las que realmente son viudas.
Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske.
17 Los ancianos que gobiernan bien sean considerados dignos de doble honor, especialmente los que trabajan arduamente en predicación y enseñanza.
Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa.
18 Porque la Escritura dice: No pondrás bozal al buey que trilla. Y: Digno es el trabajador de su pago.
Gama nassi ya ce, “Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi,” kuma “Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa.”
19 Contra un anciano no aceptes acusación, excepto delante de dos o tres testigos.
Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku.
20 Reprende delante de todos a los que pecan, para que también los demás tengan temor.
Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro.
21 Declaro solemnemente delante de Dios, de Cristo Jesús y de los ángeles escogidos que observes estas cosas sin prejuicio, sin hacer acepción de personas.
Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci.
22 No impongas [las ]manos a alguno apresuradamente, ni participes en pecados ajenos. Consérvate puro.
Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta.
23 Ya no bebas agua, sino toma un poco de vino por causa de tus frecuentes enfermedades del estómago.
Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka.
24 Los pecados de algunos hombres son evidentes antes que lleguen al juicio, pero a otros [los pecados los] siguen.
Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya.
25 Del mismo modo las buenas obras son evidentes, y las malas no se pueden esconder.
Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.

< 1 Timoteo 5 >