< Apocalipsis 19 >

1 Después de estas cosas oí algo así como una fuerte voz de una gran multitud en el cielo, que decía: “¡Aleluya! La salvación, el poder y la gloria pertenecen a nuestro Dios;
Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,
2 porque sus juicios son verdaderos y justos. Porque él ha juzgado a la gran prostituta que corrompió la tierra con su inmoralidad sexual, y ha vengado la sangre de sus siervos de su mano.”
gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.”
3 Un segundo dijo: “¡Aleluya! Su humo sube por los siglos de los siglos”. (aiōn g165)
Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” (aiōn g165)
4 Los veinticuatro ancianos y los cuatro seres vivientes se postraron y adoraron al Dios que está sentado en el trono, diciendo: “¡Amén! Aleluya!”
Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!”
5 Una voz salió del trono, diciendo: “¡Alabad a nuestro Dios, todos sus siervos, los que le teméis, los pequeños y los grandes!”
Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”
6 Oí algo como la voz de una gran multitud, y como la voz de muchas aguas, y como la voz de poderosos truenos, que decían: “¡Aleluya! ¡Porque el Señor nuestro Dios, el Todopoderoso, reina!
Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
7 Alegrémonos y regocijémonos, y démosle la gloria. Porque han llegado las bodas del Cordero, y su esposa se ha preparado”.
Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.
8 Se le dio que se vistiera de lino fino, brillante y puro, porque el lino fino son las acciones justas de los santos.
Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)
9 Me dijo: “Escribe: ‘Bienaventurados los invitados a la cena de las bodas del Cordero’”. Me dijo: “Estas son verdaderas palabras de Dios”.
Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”
10 Me postré ante sus pies para adorarle. Él me dijo: “¡Mira! ¡No lo hagas! Soy consiervo tuyo y de tus hermanos que tienen el testimonio de Jesús. Adora a Dios, porque el testimonio de Jesús es el Espíritu de Profecía”.
Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
11 Vi el cielo abierto, y he aquí un caballo blanco, y el que lo montaba se llamaba Fiel y Verdadero. Con justicia juzga y hace la guerra.
Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
12 Sus ojos son una llama de fuego, y en su cabeza hay muchas coronas. Tiene nombres escritos y un nombre escrito que nadie conoce sino él mismo.
Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.
13 Está revestido de un manto salpicado de sangre. Su nombre se llama “La Palabra de Dios”.
Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.
14 Los ejércitos que están en el cielo, vestidos de lino blanco, puro y fino, lo siguen en caballos blancos.
Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.
15 De su boca sale una espada afilada y de doble filo para herir con ella a las naciones. Las gobernará con vara de hierro. Él pisa el lagar del furor de la ira de Dios, el Todopoderoso.
Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.
16 Tiene en su manto y en su muslo un nombre escrito: “REY DE REYES Y SEÑOR DE SEÑORES”.
A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
17 Vi a un ángel de pie en el sol. Gritó con gran voz, diciendo a todas las aves que vuelan en el cielo: “¡Venid! Reúnanse en la gran cena de Dios,
Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,
18 para que coman la carne de los reyes, la carne de los capitanes, la carne de los poderosos, la carne de los caballos y de los que se sientan en ellos, y la carne de todos los hombres, libres y esclavos, pequeños y grandes.”
don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane,’yantacce da bawa, babba da yaro.”
19 Vi a la bestia, a los reyes de la tierra y a sus ejércitos reunidos para hacer la guerra contra el que estaba sentado sobre el caballo y contra su ejército.
Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.
20 La bestia fue apresada, y con ella el falso profeta que realizaba las señales a su vista, con las que engañaba a los que habían recibido la marca de la bestia y a los que adoraban su imagen. Estos dos fueron arrojados vivos al lago de fuego que arde con azufre. (Limnē Pyr g3041 g4442)
Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. (Limnē Pyr g3041 g4442)
21 Los demás fueron muertos con la espada del que estaba sentado en el caballo, la espada que salía de su boca. Y todas las aves se llenaron de su carne.
Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.

< Apocalipsis 19 >