< Isaías 37 >

1 Cuando el rey Ezequías lo oyó, se rasgó las vestiduras, se cubrió de cilicio y entró en la casa de Yahvé.
Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji.
2 Envió a Eliaquim, que estaba a cargo de la casa, y a Sebna, el escriba, y a los ancianos de los sacerdotes, cubiertos de cilicio, a ver al profeta Isaías, hijo de Amoz.
Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.
3 Le dijeron: “Ezequías dice: ‘Hoy es un día de angustia, de reprimenda y de rechazo; porque los niños han llegado al parto, y no hay fuerzas para dar a luz.
Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu.
4 Puede ser que Yahvé vuestro Dios escuche las palabras de Rabsaces, a quien el rey de Asiria, su amo, ha enviado para desafiar al Dios vivo, y reprenda las palabras que Yahvé vuestro Dios ha escuchado. Por lo tanto, levanta tu oración por el remanente que queda’”.
Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”
5 Entonces los servidores del rey Ezequías vinieron a Isaías.
Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,
6 Isaías les dijo: “Díganle a su amo: “No temas las palabras que has oído, con las que los siervos del rey de Asiria me han blasfemado.
sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo.
7 He aquí que yo pondré un espíritu en él y oirá noticias, y volverá a su tierra. Haré que caiga a espada en su propia tierra”.
Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’”
8 Volvió, pues, Rabsaces, y encontró al rey de Asiria guerreando contra Libna, pues había oído que había salido de Laquis.
Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.
9 Oyó noticias sobre Tirhakah, rey de Etiopía: “Ha salido a luchar contra ti”. Cuando lo oyó, envió mensajeros a Ezequías, diciéndole:
To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana.
10 “Así hablarás a Ezequías, rey de Judá, diciéndole: “No dejes que tu Dios, en quien confías, te engañe diciendo: “Jerusalén no será entregada en manos del rey de Asiria.”
“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’
11 He aquí que has oído lo que los reyes de Asiria han hecho a todas las tierras, destruyéndolas por completo. ¿Serás liberado?
Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne?
12 ¿Los dioses de las naciones han librado a los que mis padres destruyeron, a Gozán, a Harán, a Rezef y a los hijos de Edén que estaban en Telasar?
Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar?
13 ¿Dónde está el rey de Hamat, y el rey de Arpad, y el rey de la ciudad de Sefarvaim, de Hena y de Ivva?”
Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”
14 Ezequías recibió la carta de manos de los mensajeros y la leyó. Entonces Ezequías subió a la casa de Yahvé y la extendió ante Yahvé.
Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji.
15 Ezequías oró a Yahvé, diciendo:
Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce,
16 “Yahvé de los Ejércitos, el Dios de Israel, que está entronizado entre los querubines, tú eres el Dios, sólo tú, de todos los reinos de la tierra. Tú has hecho el cielo y la tierra.
“Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya.
17 Vuelve tu oído, Yahvé, y escucha. Abre tus ojos, Yahvé, y mira. Escucha todas las palabras de Senaquerib, que ha enviado a desafiar al Dios vivo.
Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.
18 En verdad, Yahvé, los reyes de Asiria han destruido todos los países y sus tierras,
“Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango.
19 y han echado al fuego a sus dioses, pues no eran dioses, sino obra de manos de hombres, madera y piedra; por eso los han destruido.
Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa.
20 Ahora, pues, Yahvé, nuestro Dios, sálvanos de su mano, para que todos los reinos de la tierra sepan que tú eres Yahvé, tú solo”.
Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”
21 Entonces Isaías, hijo de Amoz, envió a decir a Ezequías: “Yahvé, el Dios de Israel, dice: ‘Por haberme rogado contra Senaquerib, rey de Asiria,
Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya,
22 esta es la palabra que Yahvé ha dicho sobre él: La virgen hija de Sión te ha despreciado y te ha ridiculizado. La hija de Jerusalén ha sacudido la cabeza ante ti.
ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona ta rena tana kuma maka ba’a. Diyar Urushalima tana kada kai yayinda kake gudu.
23 ¿A quién has desafiado y blasfemado? ¿Contra quién has alzado tu voz y levantado tus ojos en alto? Contra el Santo de Israel.
Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
24 Por medio de tus siervos, has desafiado al Señor y has dicho: “Con la multitud de mis carros he subido a la altura de los montes, a lo más recóndito del Líbano. Cortaré sus altos cedros y sus selectos cipreses. Entraré en su altura más lejana, en el bosque de su campo fructífero.
Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
25 He cavado y bebido agua, y con la planta de mis pies secaré todos los ríos de Egipto.”
Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.’
26 “‘¿No has oído cómo lo he hecho hace mucho tiempo, y lo he formado en tiempos antiguos? Ahora he hecho que sea tuya la destrucción de las ciudades fortificadas, convirtiéndolas en montones ruinosos.
“Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai.
27 Por eso sus habitantes tenían poco poder. Estaban consternados y confundidos. Eran como la hierba del campo, y como la hierba verde, como la hierba de los tejados, y como un campo antes de que haya crecido su cosecha.
Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.
28 Pero yo sé que te sientas, que sales, que entras y que te enfureces contra mí.
“Amma na san inda kake zama da sa’ad da kakan fita ka kuma koma da yadda ka harzuƙa gāba da ni.
29 A causa de tu furia contra mí, y porque tu arrogancia ha subido a mis oídos, pondré mi garfio en tu nariz y mi freno en tus labios, y te haré volver por el camino por el que viniste.
Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo.
30 “‘Esta será la señal para vosotros: Este año comeréis lo que crece por sí mismo, y el segundo año lo que brota de él; y el tercer año sembraréis y segaréis y plantaréis viñas, y comeréis su fruto.
“Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa, shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan. Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba, za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci’ya’yansu.
31 El remanente que se ha escapado de la casa de Judá volverá a echar raíces hacia abajo y a dar fruto hacia arriba.
Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da’ya’ya a bisa.
32 Porque de Jerusalén saldrá un remanente, y los sobrevivientes escaparán del monte Sión. El celo de Yahvé de los Ejércitos realizará esto”.
Gama daga Urushalima raguwa za tă fito, kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki zai cika wannan.
33 “Por eso dice el Señor acerca del rey de Asiria: ‘No vendrá a esta ciudad, ni disparará una flecha en ella, ni se presentará ante ella con escudo, ni levantará un montículo contra ella.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba ya harbe kibiya a nan. Ba zai zo gabansa da garkuwa ba ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.
34 Volverá por donde vino, y no vendrá a esta ciudad’, dice el Señor.
Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji.
35 ‘Porque yo defenderé esta ciudad para salvarla, por mí y por mi siervo David’”.
“Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”
36 Entonces el ángel de Yahvé salió e hirió a ciento ochenta y cinco mil hombres en el campamento de los asirios. Cuando los hombres se levantaron de madrugada, he aquí que todos ellos eran cadáveres.
Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance!
37 Entonces Senaquerib, rey de Asiria, se marchó, volvió a Nínive y se quedó allí.
Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.
38 Mientras adoraba en la casa de Nisroc, su dios, Adramelec y Sharezer, sus hijos, lo hirieron con la espada, y escaparon a la tierra de Ararat. Su hijo Esar Haddón reinó en su lugar.
Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok,’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

< Isaías 37 >