< Génesis 44 >

1 Después dio José al mayordomo de su casa esta orden: “Llena de provisiones los costales de estos hombres cuanto puedan llevar y pon el dinero de cada uno en la boca de su costal.
Yusuf kuwa ya ba wa mai yin masa hidima a gida, waɗannan umarnai cewa, “Cika buhunan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin buhunsa.
2 Pon también mi copa, la copa de plata, en la boca del costal del menor, juntamente con el dinero de su trigo.” Y él hizo según la orden que José había dado.
Sa’an nan ka sa kwaf nawa, wannan na azurfa a bakin buhun autan, tare da kuɗinsa na hatsi.” Sai mai hidimar ya yi kamar yadda Yusuf ya umarta.
3 Al rayar el alba se despidieron los hombres con sus asnos.
Da gari ya waye, sai aka sallami mutanen tare da jakunansu.
4 Pero apenas habían salido de la ciudad, hallándose aún a poca distancia de ella, dijo José al mayordomo de su casa: “Levántate y corre tras esas gentes, y cuando los alcances, les dirás: “¿Por qué habéis devuelto mal por bien?
Ba su yi nisa da birnin ba sa’ad da Yusuf ya ce wa mai yin masa hidima, “Tashi, ka bi waɗannan mutane nan da nan, in ka same su, ka ce musu, ‘Me ya sa kuka sāka alheri da mugunta?
5 ¿No es esta (la copa) en que bebe mi señor, y por medio de la cual suele adivinar? Habéis obrado mal en lo que hicisteis.”
Ba da wannan kwaf ne maigidana yake sha daga ciki yana kuma yin amfani da shi don duba? Wannan mugun abu ne da kuka yi.’”
6 Y él, habiéndolos alcanzado, les repitió estas mismas palabras.
Sa’ad da ya same su, sai ya maimaita waɗannan kalmomi gare su.
7 Contestáronle: “¿Por qué dice mi señor tal cosa? Lejos de tus siervos hacer algo semejante.
Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu!
8 He aquí que hemos vuelto a traerte desde el país de Canaán el dinero que hallamos en la boca de nuestros costales; ¿cómo íbamos a robar de la casa de tu señor plata u oro?
Mun ma dawo maka da kuɗin da muka samu a cikin bakunan buhunanmu daga ƙasar Kan’ana. Saboda haka me zai sa mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?
9 Aquel de tus siervos en cuyo poder fuere hallada, muera, y en cuanto a nosotros seremos siervos de mi señor.”
In aka sami wani daga cikin bayinka da shi, zai mutu; sai sauran su zama bayin mai girma.”
10 Sea así como decís, respondió él. Aquel en cuyo poder fuere hallado será mi siervo; mas vosotros quedaréis sin culpa.”
Sai ya ce, “To, shi ke nan, bari yă zama yadda kuka faɗa. Duk wanda aka same shi da kwaf na azurfan zai zama bawana, sauran kuwa za su’yantu daga zargin.”
11 Con esto se apresuraron a bajar cada uno su costal a tierra; y abrió cada cual su costal.
Da sauri kowannensu ya sauko da buhunsa ƙasa, ya buɗe.
12 Y él (los) registró, empezando por el mayor, y acabando por el menor, y fue hallada la copa en el costal de Benjamín.
Sa’an nan mai hidimar ya fara bincike, farawa daga babba, ya ƙare a ƙaramin. Aka kuwa sami kwaf ɗin a buhun Benyamin.
13 Rasgaron entonces sus vestidos, y cargando cada uno su asno, volvieron a la ciudad.
Ganin wannan sai suka kyakkece rigunansu. Sa’an nan suka jibga wa jakunansu kaya, suka koma birni.
14 Así llegó Judá con sus hermanos a la casa de José —este se hallaba todavía allí— y se echaron delante de él a tierra.
Yusuf yana nan har yanzu a gida sa’ad da Yahuda da’yan’uwansa suka shiga, suka fāɗi rub da ciki a ƙasa a gabansa.
15 Díjoles José: “¿Qué es lo que habéis hecho? ¿No sabíais que un hombre como yo sabe adivinar?”
Yusuf ya ce musu, “Mene ne wannan da kuka yi? Ba ku san cewa mutum kamar ni yana iya gane abubuwa ta wurin duba ba?”
16 A lo cual respondió Judá: “¿Qué podemos decir a mi señor? ¿Qué vamos a hablar, o cómo nos justificaremos? Dios ha descubierto la iniquidad de tus siervos. Henos aquí, siervos somos de mi señor, tanto nosotros como aquel en cuyo poder fue hallada la copa.”
Yahuda ya amsa ya ce, “Me za mu ce wa ranka yă daɗe? Yaya kuma za mu wanke kanmu daga wannan zargi? Allah ya tona laifin bayinka. Ga mu, za mu zama bayinka, da mu da wanda aka sami kwaf ɗin a hannunsa.”
17 “Lejos de mí hacer tal cosa, contestó José. El hombre en cuyo poder fue hallada la copa, ese será siervo mío; vosotros, empero, subid en paz a casa de vuestro padre.”
Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.”
18 Entonces Judá se acercó a él, y dijo: “Por favor, señor mío, permite que tu siervo diga una palabra a oídos de mi señor, y no se encienda tu ira contra tu siervo; porque tú eres igual al Faraón.
Sai Yahuda ya haura zuwa wurinsa ya ce, “Ranka yă daɗe, roƙo nake, bari bawanka yă yi magana da ranka yă daɗe. Kada ka yi fushi da bawanka, ko da yake daidai kake da Fir’auna kansa.
19 Mi señor preguntó a sus siervos, diciendo: ‘¿Tenéis padre o hermano?’
Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’
20 Respondimos a mi señor: ‘Sí, tenemos un padre anciano, y un niño de su vejez, que es el menor y cuyo hermano murió, de modo que él solo le ha quedado de su madre, y su padre le ama’.
Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
21 Tú dijiste entonces a tus siervos: ‘Traédmelo, para que ponga mis ojos sobre él’.
“Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’
22 Mas nosotros respondimos a mi señor: ‘El joven no puede dejar a su padre; porque si lo dejare, su padre morirá’.
Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’
23 Pero tú dijiste a tus siervos: ‘Si no baja con vosotros vuestro hermano menor, no volveréis a ver mi rostro’.
Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’
24 Subimos, pues a casa de tu siervo, mi padre, y le contamos las palabras de mi señor.
Sa’ad da muka koma wurin bawanka mahaifinmu, sai muka faɗa masa abin da ranka yă daɗe ya ce.
25 Y cuando dijo nuestro padre: ‘Volved a comprarnos algo para comer’,
“Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’
26 contestamos nosotros: ‘No podemos bajar. Pero si nuestro hermano menor va con nosotros, bajaremos; pues no podremos ver el rostro de aquel hombre, a no ser que vaya con nosotros nuestro hermano menor’.
Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’
27 Entonces nos dijo tu siervo, mi padre: ‘Vosotros sabéis que mi esposa me dio dos hijos.
“Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini’ya’ya biyu maza.
28 El uno desapareció de mi presencia, y yo dije: Sin duda ha sido devorado, y hasta ahora no le he visto más.
Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni.
29 Si lleváis también a este de mi presencia, y le sucede alguna desgracia, haréis descender con dolor mis canas al sepulcro’. (Sheol h7585)
In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’ (Sheol h7585)
30 Ahora, pues, si yo llego a tu siervo mi padre, y no está con nosotros el joven, de cuya vida depende la suya,
“Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin,
31 sucederá que al ver que el joven no existe, morirá; y así tus siervos harán descender con dolor al sepulcro las canas de tu siervo, nuestro padre. (Sheol h7585)
ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. (Sheol h7585)
32 Porque tu siervo se hizo responsable por el joven ante mi padre, diciendo: ‘Si no te lo vuelvo a traer, seré para siempre reo de pecado contra mi padre’.
Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’
33 Te ruego, pues, que tu siervo quede en lugar del joven por esclavo de mi señor, a fin de que el joven pueda volver con sus hermanos.
“To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da’yan’uwansa.
34 Pues ¿cómo podré yo subir a casa de mi padre, sin que el joven esté conmigo? ¡No vea yo el mal que vendrá sobre mi padre!”
Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”

< Génesis 44 >