< Matej 26 >

1 In zgodí se, ko je Jezus vse te besede končal, reče učencem svojim:
Yayin da Yesu ya gama fadi masu wadannan maganganu, sai ya cewa almajiransa,
2 Véste, da bo črez dva dní velika noč, in sin človečji bo izdan, da ga križajo.
“Kun sani sauran kwana biyu idin ketarewa ya zo, kuma za'a bada Dan mutum domin a gicciye shi.
3 Tedaj se zberó véliki duhovni in pismarji in starešine naroda na dvoru vélikega duhovna, kteremu je bilo ime Kajfa.
Sa'annan manyan firistoci da dattawan jama'a suka taru a fadar babban firist, mai suna Kayafa.
4 In posvetujejo se, da bi Jezusa z zvijačo vjeli in umorili.
Suka shirya yadda zasu kama Yesu a boye su kuma kashe shi.
5 Govorili so pa: Ne na praznik, da se narod ne spunta.
Amma suna cewa, “Ba a lokacin idin ba, domin kada tarzoma ta tashi daga cikin mutane.”
6 Ko je bil pa Jezus v Betaniji v hiši Simona gobavca,
Sa'adda Yesu yake Baita'anya a gidan Saminu Kuturu,
7 Pristopi k njemu žena, ktera je imela sklenico dragocene mire, in jo izlije na glavo njegovo, ko je sedel za mizo.
daidai lokacin da ya zauna a gefen teburin cin abinci, sai wata mata ta shigo da kwalbar mai, mai tsada, ta zuba wa Yesu a kansa.
8 Ko pa učenci njegovi to vidijo, razhudé se, govoreč: Čemu ta potrata?
Amma da almajiransa suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Ina dalilin yin irin wannan asara?
9 Ta mira namreč bi se bila mogla za mnogo prodati, in dati se ubogim.
Ai da an sayar da wannan mai da kudi mai yawa a rabawa talakawa.”
10 Ko pa Jezus to spazi, reče jim: Kaj delate ženi skrbí? kajti dobro delo je storila na meni.
Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, “Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina.
11 Uboge namreč imate vselej s seboj; mene pa nimate vselej.
Kuna da talakawa tare da ku koyaushe, amma ni ba zan kasance da ku ba koyaushe.
12 Kajti da je izlila to miro na telo moje, storila je to za pokop moj.
Don a sa'adda ta zuba man nan a jikina, ta yi haka ne don jana'iza ta.
13 Resnično vam pravim: Kjerkoli po vsem svetu se bo oznanjal ta evangelj, povedalo se bo tudi to, kar je ona storila, njej v spomin.
Hakika Ina gaya maku, duk inda za ayi wannan bishara a dukan duniya, abin da matar nan tayi za'a rika ambatar da shi don tunawa da ita.”
14 Tedaj odide eden od dvanajsterih, kteremu je bilo ime Juda Iškarijan, k vélikim duhovnom,
Sai daya daga cikin sha biyun, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya tafi wurin manyan firistocin,
15 In reče: Kaj mi hočete dati, in jaz vam ga bom izdal? Oni mu pa obrekó trideset srebrnikov.
yace, ''Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?” Suka auna masa azurfa talatin.
16 In odtlej je iskal priložnosti, da ga izdá.
Daga wannan lokacin yayi ta neman zarafi da zai bada shi a wurinsu.
17 Prvi dan presnih kruhov pa pristopijo učenci k Jezusu in mu rekó: Kje hočeš, da ti pripravimo, da boš jedel velikonočno jagnje?
To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?”
18 On pa reče: Pojdite v mesto k temu in temu, in recite mu: Učenik pravi: Čas moj je blizu; pri tebi bom jedel velikonočno jagnje z učenci svojimi.
Yace, “Ku shiga cikin birnin zaku sami wani mutum sai kuce masa, 'Mallam yace, “lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina.”'''
19 In učenci storé, kakor jim je Jezus ukazal, in pripravijo velikonočno jagnje.
Almajiran suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su, suka shirya abincin idin ketarewar.
20 Ko se je pa zvečerilo, sede za mizo z učenci svojimi.
Da yamma ta yi, sai ya zauna domin ya ci tare da almajiransa goma sha biyu.
21 In ko so jedli, reče: Resnično vam pravim, da me bo eden izmed vas izdal.
Sa'adda suke ci, yace, “Hakika ina gaya maku, daya daga cikin ku zai bada ni.”
22 In zeló jim se užali, in začnó mu praviti vsak od njih: Ali sem jaz, Gospod?
Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, ''Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?”
23 On pa odgovorí in reče: Ta, ki je omočil z menoj rokó v skledo, ta me bo izdal.
Sai ya amsa, “Wanda ke sa hannu tare da ni cikin kwano daya shi ne zai bada ni.
24 Sin človečji sicer gre, kakor je pisano za-nj; ali gorjé tistemu človeku, kteri sina človečjega izdaja, Bolje bi mu bilo, da se ne bi bil tisti človek rodil.
Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba.”
25 Juda izdajalec njegov pa odgovorí in reče: Ali sem jaz, rabi? Reče mu: Ti si rekel.
Yahuza da zai bada shi yace, “Mallam ko ni ne?” Yace masa, “Ka fada da kanka.”
26 Ko so pa jedli, vzeme Jezus kruh, in blagoslovivši, prelomi, in dajal je učencem svojim, govoreč: Vzemite, jejte; to je telo moje.
Yayin da suke ci, sai Yesu ya dauki gurasa, ya sa albarka, ya karya. Ya ba almajiran yace, “Ku karba, ku ci, wannan jiki nane.”
27 In vzemši kelih, zahvali, in dá jim, govoreč: Pijte iž njega vsi;
Sai ya dauki kokon yayi godiya, Ya ba su yace, “Ku sha, dukanku.
28 Kajti to je kri moja novega zakona, ktera se prelija za mnoge v odpuščanje grehov.
“Gama wannan jinina ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa.
29 Pravim vam pa, da odslej ne bom pil od tega trtnega rodú, do tistega dné, ko ga bom pil z vami novega v kraljestvu očeta svojega.
Amma ina gaya maku, ba zan kara shan ruwan inabin nan ba, sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a cikin mulkin Ubana.”
30 In ko so odpeli, odidejo na oljsko goro.
Da suka raira waka, sai suka ka tafi dutsen zaitun.
31 Tedaj jim reče Jezus: Vsi vi se boste pohujšali to noč od mene. Kajti pisano je: "Pastirja bom udaril, in razkropile se bodo ovce črede."
Sai Yesu yace masu, “Dukan ku zaku yi tuntube a wannan dare sabili da ni, gama a rubuce yake, ''Zan bugi makiyayin, garken tumakin kuma za su watse.'
32 Po vstajanji svojem pa pojdem pred vami v Galilejo.
Amma bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa Galili.”
33 Peter pa odgovorí in mu reče: Če se tudi vsi od tebe pohujšajo, jaz se ne bom nikoli pohujšal.
Amma Bitrus yace masa, “Ko dama duka zasu fadi sabili da kai, ni kam bazan fadi ba.”
34 Jezus mu reče: Resnično ti pravim, da to noč, predno bo petelin zapel, zatajil me boš trikrat.
Yesu yace masa, ''Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku.”
35 Peter mu pravi: In ko bi moral s teboj umreti, ne bom te zatajil. Tako tudi vsi učenci rekó.
Bitrus yace masa, koda zan mutu tare da kai, bazan yi musunka ba.” Sai sauran almajiran suma suka fadi haka.
36 Tedaj pride ž njimi Jezus v vas imenovano Getsemane, in reče učencem: Usedite se tu dotlej, da grem in tam molim.
Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, ''Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a.”
37 In vzemši Petra in Zebedejeva dva sina, začne žalovati in obupovati.
Ya dauki Bitrus da kuma 'ya'ya biyu na Zabadi tare da shi, sai ya fara damuwa da juyayi.
38 Tedaj jim reče: Žalostna je duša moja do smrti; ostanite tu, in čujte z menoj.
Sai yace masu, “Raina na cikin damuwa sosai har ga mutuwa. Ku kasance anan kuna tsaro tare da ni.”
39 In odšedši malo dalje, pade na obraz svoj, in molil je, govoreč: Oče moj! če je mogoče, odide naj ta kelih od mene; ali ne kakor hočem jaz, nego kakor ti.
Ya dan taka zuwa gaba kadan, sai ya fadi a fuskarsa, yayi addu'a. Yace, “Ya Ubana, in zai yiwu, bari kokon nan ya wuce ni. Duk da haka, ba nufina za'a bi ba, amma naka nufin.”
40 In prišedši k učencem, najde jih, da spé; ter reče Petru: Tako niste mogli ene ure z menoj prečuti?
Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, “Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya?
41 Čujte in molite, da ne zajdete v izkušnjavo; duh je sicer krepek, ali telo je slabo.
Ku yi tsaro kuma, kuyi addu'a domin kada ku fada cikin jaraba. Ruhu dai ya yarda amma, jiki ba karfi.”
42 Zopet odide drugoč; in molil je, govoreč: Oče moj! ako ne more ta kelih oditi od mene, če ga ne pijem, zgódi se volja tvoja.
Sai ya koma karo na biyu yayi addu'a, Yace, “Ya Ubana, in wannan kokon ba zai wuce ba sai na sha shi, bari nufinka ya kasance.”
43 In prišedši, najde jih zopet, da spé; bile so jim namreč oči otežale.
Ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi.
44 In pustivši jih, odide zopet; in molil je v tretje, govoreč iste besede.
Sai ya sake barinsu ya tafi. Ya koma karo na uku yana addu'a yana fadin kalmomi iri daya.
45 Tedaj pride k učencem svojim, in reče jim: Spite dalje in počivajte! Glej, ura se je približala, in sin človečji se izdaja grešnikom v roke.
Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, “Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi.
46 Vstanite, pojdimo! Glej, izdajalec moj se je približal.
Ku tashi mu tafi. Duba, wanda zai badani ya kusato.”
47 In ko je še govoril, glej, pride Juda, eden od dvanajsterih, in ž njim mnogo ljudstva z meči in koli, od vélikih duhovnov in starešin naroda.
Sa'adda yana cikin magana Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya zo. Babban taro ya zo tare da shi daga wurin manyan firistoci da dattawan jama'a. Suna rike da takubba da kulake.
48 Izdajalec njegov jim je pa dal znamenje, govoreč: Kogar bom poljubil, ta je; primite ga.
To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, ''Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi.''
49 In precej pristopi k Jezusu, in reče: Zdrav bodi, rabi! in ga poljubi.
Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, “Gaisuwa, Mallam!” sai ya sumbace shi.
50 Jezus mu pa reče: Prijatelj! po kaj si prišel? Tedaj pristopijo in položé roke svoje na Jezusa in ga vjemó.
Yesu kuwa yace masa, “Aboki, kayi abin da ya kawo ka.” Sai suka iso suka sa hannuwansu kan Yesu suka kama shi.
51 In glej, eden tistih, kteri so bili z Jezusom, stegne roko svojo in izdere meč svoj, in udari hlapca vélikega duhovna in mu odseka uho.
Nan take, daya daga cikin wadanda suke tare da Yesu ya mika hannunsa, ya zare takobinsa, ya sare wa bawan babban firist din kunne.
52 Tedaj mu velí Jezus: Vtakni meč svoj na mesto njegovo; kajti vsi, kteri primejo za meč, poginili bodo z mečem.
Sai Yesu yace, masa, “Ka maida takobinka cikin kubensa, domin duk wadanda suka dauki takobi su ma ta wurin takobi za su hallaka.
53 Ali misliš li, da ne morem sedaj očeta svojega prositi, in poslal bi mi več nego dvanajst legijonov angeljev?
Ko kana tunanin ba zan iya kiran Ubana ba, ya kuma aiko da rundunar Mala'iku fiye da goma sha biyu?
54 Kako bi se pa izpolnila pisma, da mora tako biti?
Amma to tayaya za'a cika nassi, cewa dole wannan ya faru?''
55 V ta čas reče Jezus ljudstvu: Kakor na razbojnika ste izšli na me z meči in koli? Vsak dan sem sedel pri vas, učeč v tempeljnu, in niste me zgrabili.
A wannan lokacin Yesu yace wa taron, “Kun zo da takubba da kulake ku kama ni kamar dan fashi? Ina zaune kowace rana a haikali ina koyarwa, amma baku kama ni ba.
56 Ali vse to se je zgodilo, da se izpolnijo pisma prerokov. Tedaj ga vsi učenci pusté, in pobegnejo.
Amma duk wannan ya faru ne don a cika abinda annabawa suka rubuta.” Bayan haka sai dukkan almajiran suka bar shi suka gudu.
57 A tisti, kteri so Jezusa vjeli, odpeljejo ga k vélikemu duhovnu Kajfu, kjer so se pismarji in starešine zbrali.
Wadanda suka kama Yesu, suka kai shi wurin Kayafa babban firist, inda marubuta da duttawan jama'a suka taru.
58 A Peter je šel oddaleč za njim, noter do dvora vélikega duhovna; in stopivši noter, sede k hlapcem, da vidi konec.
Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har zuwa farfajiyar babban firist din. Ya shiga ya zauna da masu tsaro domin ya ga abinda zai faru.
59 Véliki duhovni in pismarji in ves zbor so pa iskali lažnjive priče zoper Jezusa, da bi ga umorili.
A wannan lokaci manyan firistoci da duk 'yan majalisar suka fara neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi.
60 In ne najdejo je. In da si ravno pristopi mnogo lažnjivih prič, ne najdejo. Naposled pa pristopite dve priči,
Amma ba su samu ko daya ba, ko dayake an samu shaidun karya dayawa da suka gabata. Amma daga baya sai wasu su biyu suka fito
61 In rečete: Ta je rekel: Jaz morem tempelj Božji podreti, in v treh dnéh sezidati ga.
sukace ''Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.'''
62 In véliki duhoven vstane in mu reče: Ne odgovarjaš li ničesar? Kaj pričajo ti zoper tebe?
Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, “Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?”
63 Jezus je pa molčal. In véliki duhoven odgovorí in mu reče: Zaklinjam te pri živem Bogu, da nam povej, če si ti Kristus sin Božji?
Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, “Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah.''
64 Jezus mu reče: Ti si rekel. Ali pravim vam: Odslej boste videli sina človečjega, da sedí na desnici moči, in gre na nebeških oblakih.
Yesu ya amsa masa, “Ka fada da bakin ka. Amma ina gaya maka, daga yanzu zaka ga Dan mutun na zaune a hannun dama na iko, ya na zuwa akan gizagizai na sama.”
65 Tedaj raztrga véliki duhoven oblačila svoja, govoreč: Boga je preklel; kaj nam je še treba prič? Glej, ravnokar ste slišali kletvino njegovo.
Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, “Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon.
66 Kaj se vam zdí? Oni pa odgovoré in rekó: Smrti je vreden.
Menene tunaninku?” Suka amsa sukace, “Ya cancanci mutuwa.”
67 Tedaj mu pljunejo v obraz, in bijejo ga za uho; a drugi ga bijejo s pestmi,
Sai suka tofa masa yawu a fuska, suka kuma yi masa duka, suka kuma mammare shi da tafin hannuwansu,
68 Govoreč: Prerokuj nam, Kristus! kdo je, ki te je udaril?
sukace, ''Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka.
69 Peter je pa sedel zunej na dvoru. Pa pristopi k njemu ena dekla, in reče: Tudi ti i bil z Jezusom Galilejcem.
To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, “Kaima kana tare da Yesu na Galili.”
70 On na tají pred vsemi, govoreč: Ne vém, kaj praviš.
Amma ya yi musun haka a gaban su duka, yace, “Ban ma san abinda kike magana akai ba.”
71 Ko pa izide k vratom, ugleda ga druga, in reče tistim, kteri so bili tam: Tudi ta je bil z Jezusom Nazarečanom.
Da ya fita zuwa bakin kofa, nan ma wata yarinyar baiwa ta gan shi tace wa wadanda suke wurin, “Wannan mutumin ma yana tare da Yesu Banazare.”
72 In zopet tají s prisego: Ne poznam tega človeka.
Sai yayi musun haka kuma, har da rantsuwa, yace, “Ban san mutumin nan ba.”
73 Malo potem pa pristopijo tisti, kteri so stali, in rekó Petru: Resnično, tudi ti si izmed njih; saj te tudi govorica tvoja izdaja.
Bayan dan lokaci kadan wadanda suke a tsaye suka zo wurin Bitrus suka ce masa, “Hakika kai daya daga cikin su ne, gama harshen ka ya tonaka.”
74 Tedaj se začne rotiti in kleti: Ne poznam tega človeka. In precej zapoje petelin.
Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, ''Ban san wannan mutumin ba,” nan da nan zakara yayi cara.
75 In Peter se spomene Jezusove besede, ktero mu je rekel: Predno bo petelin zapel, zatajil me boš trikrat. Ter izide in se britko razjoka.
Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya fada, “Kafin carar zakara zaka yi musun sani na sau uku.” Sai ya fita waje yayi kuka mai zafi.''

< Matej 26 >