< Efežanom 4 >

1 Opominjam vas torej jaz, jetnik v Gospodu, da se vedete spodobno poklicu, v katerega ste poklicani,
Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku.
2 Z vso ponižnostjo in krotkostjo, s potrpežljivostjo prenašajoč se med seboj v ljubezni,
Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna.
3 Skrbno prizadevajoč si ohraniti edinost Duha v vezí mirú.
Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama.
4 Eno telo in en Duh, kakor ste tudi poklicani v enem upanji poklica svojega;
Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya.
5 En Gospod, ena vera, en krst;
Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya.
6 En Bog in oče vseh, ki je nad vsemi in po vseh in v vseh vas.
Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka.
7 Vsakemu pa izmed nas dala se je milost po meri darú Kristusovega.
Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu.
8 Zato pravi: "Šel je kvišku ter pripeljal vjetnike, in dal je dar ljudém."
Kamar yadda nassi ya ce, “Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye.
9 (Tisto pa: "šel je kvišku", kaj je druzega, nego da je tudi šel prej dol v spodnje dele zemlje?
Menene ma'anar, “Ya hau?” Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa.
10 On, ki je šel dol, je tisti, ki je šel tudi gor nad vsa nebesa, da bi vse izpolnil.)
Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa.
11 In on je dal ene za aposteljne, ene za preroke, ene za evangeliste, ene za pastirje in učenike,
Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa.
12 V pripravo svetih, za delo službe, za zdelovanje telesa Kristusovega;
Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu.
13 Dokler dospemo vsi do edinosti vere in spoznanja sinú Božjega, do moža doraslega, do mere starosti polnosti Kristusove;
Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu.
14 Da ne bodemo več deca, in nas ne bode sem ter tja metala in gonila vsaka sapa nauka v zvijačnosti človeški, v prekanjenosti do zvitosti zmote;
Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya.
15 Nego da po resničnosti v ljubezni rastemo v vsem do njega, ki je glava, Kristus,
Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu.
16 Iz katerega vse telo združeno in zedinjeno po slehernem členovji podajanja, po kreposti v meri vsakega dela rast telesa vrši v izpodbujo svojo v ljubezni.
Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna.
17 To torej pravim in pričam v Gospodu, da ne hodite dalje, kakor tudi drugi pogani hodijo v ničemurnosti srca svojega,
Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani.
18 Otemnjeni v razumu, odtujeni življenju Božjemu, zaradi nevednosti bivajoče v njih, zaradi otrpnenosti srca svojega;
Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu.
19 Kateri so otrpneni vdali se razuzdanosti v doprinašanje sleherne nečistosti v lakomnosti.
Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari.
20 Vi pa se niste tako učil Kristusa,
Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba.
21 Ako ste ga slišali in ste bili poučeni v njem, kakor je resnica v Jezusu;
Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke.
22 Da slečete, po prejnšjem življenji, starega človeka, ki se kvari po sljah prevare;
Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri.
23 In se ponovite po duhu srca svojega,
Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku.
24 In oblečete novega človeka, vstvarjenega po Bogu, v pravičnosti in svetosti resnice.
Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya.
25 Zato iznebivši se laži govorite resnico vsak z bližnjim svojim, ker smo udje med seboj;
Saboda haka ku watsar da karya. “Fadi gaskiya ga makwabcin ka”, domin mu gabobin juna ne.
26 "Jezite se, in ne grešite!" Solnce naj ne zaide nad jezo vašo,
“Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi.” Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi.
27 In ne dajajte prostora hudiču.
Kada ku ba shaidan wata kofa.
28 Kdor krade, ne kradi več, temuč trúdi se, delajoč dobro z rokami, da ima kaj podeliti potrebnemu.
Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu.
29 Nobena gnjila beseda ne izidi iz vaših ust, nego če je katera dobra za izpodbujo po potrebi, da dá milost poslušajočim.
Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji.
30 In ne žalite svetega Duha Božjega, v katerem ste zapečateni za rešenja dan.
Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa.
31 Vsaka bridkost in srd in jeza in vpitje in preklinjanje izgini od vas z vso hudobijo;
Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta.
32 Bodite pa med seboj blagi, usmiljeni, odpuščajoč si, kakor je tudi Bog v Kristusu vam odpustil.
Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.

< Efežanom 4 >