< 1 Korinčanom 14 >
1 Hrepenite za ljubeznijo, a trudite se za duhovne stvari, bolje pa, da prerokujete.
Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci.
2 Kajti kdor govori v jeziku, ne govori ljudém, nego Bogu, ker nikdor ne sluša; z duhom pa govori skrivnosti;
Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu.
3 A kdor prerokuje ljudém, govori na zbujanje pobožnosti in na opominjanje in na tolažbo.
Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta'azantar dasu.
4 Kajti kdor v jeziku govori, sam sebe zbuja na pobožnost, kdor pa prerokuje, cerkev zbuja na pobožnost.
Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa.
5 Hočem pa, da vsi govorite jezike, bolje pa, da prerokujete, kajti veči je, kdor prerokuje, nego kdor govori jezike, razen če razklada, da bi se cerkev zbudila na pobožnost.
To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna ( sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu).
6 Sedaj pa, bratje, če pridem k vam jezike govoreč, kaj vam bom koristil, če vam ne bom govoril ali v razodetji, ali v znanji, ali v preroštvu, ali v nauku?
Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa.
7 Kakor brezdušne stvari, ktere glas dajo, bodi si piščal, ali gosli, če razločka v glasovih ne dajo, kako se bo umelo, kaj se piska ali gode?
Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa?
8 Ker če nerazločen glas trobenta dá, kdo se bo pripravil za boj?
Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma'ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki?
9 Tako tudi vi, če z jezikom razumljive besede ne daste, kako se bo umelo, kaj pravite? kajti v zrak boste govorili.
Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma'ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku.
10 Toliko vrst glasov, postavim, je na svetu, in nobeden izmed njih ni brez znamenovanja.
Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma'ana.
11 Če torej ne vem moči glasa, mutec bom govorečemu in govoreči bo meni mutec.
Amma idan ban san ma'anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni.
12 Tako tudi vi, ko se trudite za duhovne darí, glejte, da boste za pobožno zbujevanje cerkve bogati.
haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya.
13 Za to, kdor govori v jeziku, naj moli, da bi razkladal.
To wanda yake magana da harshe yayi addu'a domin ya iya fassarawa.
14 Kajti če molim v jeziku, duh moj moli, a um moj je brez sada.
Domin idan nayi addu'a da harshe, ruhuna yayi addu'a, amma fahimtata bata karu ba.
15 Kaj torej? molil bom z duhom, a molil bom tudi z umom; prepeval bom z duhom, a prepeval bom tudi z umom.
To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata.
16 Ker če blagosloviš z duhom, ta, kteri je nepodučen, kako poreče amen na tvoj blagoslov, ko ne ve, kaj govoriš?
In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, “Amin” a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba?
17 Ti se, res da, dobro zahvaljuješ, ali drugi se ne zbuja na pobožnost.
Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba.
18 Zahvaljujem se svojemu Bogu, da bolje od vseh vas jezike govorim.
Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka.
19 Toda v cerkvi rajši pet besed s svojim umom rečem, da tudi druge podučim, nego pa tisoč besed v jeziku.
Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe.
20 Bratje, ne bodite deca, nego v zlobi bodite deca, a v umu bodite popolni.
'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma.
21 V postavi je pisano: "Z drugimi jeziki in z drugimi ustnicami bom govoril temu ljudstvu, in tudi tako me ne bodo poslušali, govori Gospod."
A rubuce yake a shari'a cewa, “zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba”, in ji Ubangiji.
22 Tako so jeziki za znamenje ne tem, kteri verujejo, nego nevernim, in preroštvo ne nevernim, nego tem, kteri verujejo.
Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba.
23 Ko bi se torej sešla cerkev vsa na eno mesto, in bi vsi jezike govorili in vnišli bi tudi nepodučeni ali neverniki, je li ne porekó, da norite?
Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba?
24 Ko bi pa vsi prerokovali a vnišel bi kak nevernik ali nepodučen, ozmerjajo ga vsi, sodijo ga vsi.
In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar,
25 In tako se skrivnosti njegovega srca razodevajo, in tako padši na obraz molil bo Boga oznanjujoč, da je Bog za res v vas.
asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku.
26 Kaj je torej, bratje? Kedar se shajate, vsak vas ima psalm, ima nauk, jezik ima, razodetje ima, razkladanje ima: vse naj se zgodi na zbujevanje pobožnosti.
Sai me kuma 'yan'uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya.
27 Če v jeziku kdo govori, naj govorita po dva ali k večemu po trije in eden za drugim, in eden naj razklada.
Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada.
28 Ko bi pa ne bilo razkladalca, molči naj v cerkvi, a sebi naj govori in Bogu.
Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah.
29 Preroka naj pa govorita dva ali trije, drugi naj pa razsojajo.
Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada.
30 Če se pa drugemu, kteri sedí, kaj razodene, prvi naj molči.
Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru.
31 Kajti morete eden po eden vsi prerokovati, da se vsi učé in vsi opominjajo.
Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa.
32 In duhovi preroški podlagajo se prerokom.
Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa,
33 Ker Bog ni Bog punta, nego in mira, kakor po vseh cerkvah svetniških.
domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya.
34 Žene vaše naj v cerkvah molčé, kajti ni jim dopuščeno govoriti, nego podlagati se, kakor tudi postava pravi.
Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce.
35 A če se hočejo česa naučiti, doma naj svoje može prašajo; kajti grdo je ženam v cerkvi govoriti.
Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya.
36 Je li od vas beseda Božja izšla? je li k vam samim prišla?
Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso?
37 Če kdo misli, da je prerok ali duhoven, spozna naj, kar vam pišem, da so Gospodove zapovedi.
In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji.
38 Če pa kdo ne vé, naj ne vé.
In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi.
39 Tako, bratje, trudite se, da prerokujete in govoriti v jezikih nikar ne branite.
Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna.
40 Vse naj se spodobno in po redu godi.
Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.