< Псалтирь 127 >
1 Аще не Господь созиждет дом, всуе трудишася зиждущии: аще не Господь сохранит град, всуе бде стрегий.
Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.
2 Всуе вам есть утреневати: востанете по седении ядущии хлеб болезни, егда даст возлюбленным Своим сон.
Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
3 Се, достояние Господне сынове, мзда плода чревняго.
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.
4 Яко стрелы в руце сильнаго, тако сынове оттрясенных.
Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
5 Блажен, иже исполнит желание свое от них: не постыдятся, егда глаголют врагом своим во вратех.
Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.