< От Матфея святое благовествование 12 >
1 В то время иде Иисус в субботы сквозе сеяния: ученицы же Его взалкаша и начаша востерзати класы и ясти.
A wannan lokaci, Yesu ya tafi a ranar Asabaci, ya bi cikin gonar hatsi. Almajiransa na jin yunwa, sai suka fara zagar hatsi suna ci.
2 Фарисее же видевше реша Ему: се, ученицы Твои творят, егоже не достоит творити в субботу.
Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. “Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci.”
3 Он же рече им: несте ли чли, что сотвори Давид, егда взалка сам и сущии с ним?
Amma Yesu ya ce masu, “Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi?
4 Како вниде в храм Божий и хлебы предложения снеде, ихже не достойно бе ему ясти, ни сущым с ним, токмо иереем единым?
Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci?
5 Или несте чли в законе, яко в субботы священницы в церкви субботы сквернят и неповинни суть?
Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba?
6 Глаголю же вам, яко церкве боле есть зде:
Amma ina tabbatar maku da cewa, wani wanda ya fi haikali girma yana nan.
7 аще ли бысте ведали, что есть: милости хощу, а не жертвы, николиже убо бысте осуждали неповинных:
In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba.
8 господь бо есть и субботы Сын Человеческий.
Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci.”
9 И прешед оттуду, прииде на сонмище их.
Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su.
10 И се, человек бе ту, руку имый суху. И вопросиша Его, глаголюще: аще достоит в субботы целити? Да на Него возглаголют.
Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, “Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?” Domin su zarge shi a kan zunubi.
11 Он же рече им: кто есть от вас человек, иже имать овча едино, и аще впадет сие в субботы в яму, не имет ли е и измет?
Yesu ya ce masu, “Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba?
12 Кольми убо лучши есть человек овчате? Темже достоит в субботы добро творити.
Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci.”
13 Тогда глагола человеку: простри руку твою. И простре: и утвердися цела яко другая.
Sai Yesu ya ce wa mutumin nan “Mika hannun ka.” Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa.
14 Фарисее же шедше совет сотвориша на Него, како Его погубят. Иисус же разумев отиде оттуду.
Amma Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri domin sa. Su na neman hanyar da za su kashe shi.
15 И по Нем идоша народи мнози, и изцели их всех:
Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka.
16 и запрети им, да не яве Его творят:
Ya dokace su da kada su bayyana shi ga kowa,
17 яко да сбудется реченное Исаием пророком, глаголющим:
domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa,
18 се, Отрок Мой, Егоже изволих, Возлюбленный Мой, Наньже благоволи душа Моя: положу дух Мой на Нем, и суд языком возвестит:
“Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai.
19 не преречет, ни возопиет, ниже услышит кто на распутиих гласа Его:
Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku.
20 трости сокрушенны не преломит и лена внемшася не угасит, дондеже изведет в победу суд:
Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara.
21 и на имя Его языцы уповати имут.
Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa.
22 Тогда приведоша к Нему беснующася слепа и нема: и изцели его, яко слепому и немому глаголати и глядати.
Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana.
23 И дивляхуся вси народи глаголюще: еда Сей есть (Христос) сын Давидов?
Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, “Ko wannan ne Dan Dawuda?”
24 Фарисее же слышавше реша: Сей не изгонит бесы, токмо о веельзевуле князи бесовстем.
Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, “Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne.”
25 Ведый же Иисус мысли их, рече им: всякое царство раздельшееся на ся запустеет, и всяк град или дом разделивыйся на ся не станет.
Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. “Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe.
26 И аще сатана сатану изгонит, на ся разделился есть: како убо станет царство его?
Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya?
27 И аще Аз о веельзевуле изгоню бесы, сынове ваши о ком изгонят? Сего ради тии вам будут судии.
Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku.
28 Аще ли же Аз о Дусе Божии изгоню бесы, убо постиже на вас Царствие Божие.
Amma idan ina fitar da aljannu da Ruhun Allah ne, hakika mulkin Allah ya zo gare ku.
29 Или како может кто внити в дом крепкаго и сосуды его расхитити, аще не первее свяжет крепкаго, и тогда дом его расхитит?
Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa.
30 Иже несть со Мною, на Мя есть: и иже не собирает со Мною, расточает.
Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne.
31 Сего ради глаголю вам: всяк грех и хула отпустится человеком: а яже на Духа хула не отпустится человеком:
Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba.
32 и иже аще речет слово на Сына Человеческаго, отпустится ему: а иже речет на Духа Святаго, не отпустится ему ни в сей век, ни в будущий. (aiōn )
Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada. (aiōn )
33 Или сотворите древо добро и плод его добр: или сотворите древо зло и плод его зол: от плода бо древо познано будет.
Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa.
34 Порождения ехиднова, како можете добро глаголати, зли суще? От избытка бо сердца уста глаголют.
Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana.
35 Благий человек от благаго сокровища износит благая: и лукавый человек от лукаваго сокровища износит лукавая.
Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta.
36 Глаголю же вам, яко всяко слово праздное, еже аще рекут человецы, воздадят о нем слово в день судный:
Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi.
37 от словес бо своих оправдишися и от словес своих осудишися.
Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku.”
38 Тогда отвещаша нецыи от книжник и фарисей, глаголюще: Учителю, хощем от Тебе знамение видети.
Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, “Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
39 Он же отвещав рече им: род лукав и прелюбодей знамения ищет, и знамение не дастся ему, токмо знамение Ионы пророка:
Amma Yesu ya amsa ya ce masu, “Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa.
40 якоже бо бе Иона во чреве китове три дни и три нощы, тако будет и Сын Человеческий в сердцы земли три дни и три нощы.
Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa.
41 Мужие Ниневитстии востанут на суд с родом сим и осудят его, яко покаяшася проповедию Иониною: и се, боле Ионы зде.
Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan.
42 Царица южская востанет на суд с родом сим и осудит и, яко прииде от конец земли слышати премудрость Соломонову: и се, боле Соломона зде.
Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan.
43 Егда же нечистый дух изыдет от человека, преходит сквозе безводная места, ищя покоя, и не обретает:
Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba.
44 тогда речет: возвращуся в дом мой, отнюдуже изыдох. И пришед обрящет празден, пометен и украшен:
Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta.
45 тогда идет и поймет с собою седмь иных духов лютейших себе, и вшедше живут ту: и будут последняя человеку тому горша первых. Тако будет и роду сему лукавому.
Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani.
46 Еще же Ему глаголющу к народом, се, Мати (Его) и братия Его стояху вне, ищуще глаголати Ему.
Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi.
47 Рече же некий Ему: се, Мати Твоя и братия Твоя вне стоят, хотяще глаголати Тебе.
Sai wani ya ce masa, “Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai”.
48 Он же отвещав рече ко глаголющему Ему: кто есть Мати Моя, и кто суть братия Моя?
Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, “Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?”
49 И простер руку Свою на ученики Своя, рече: се, мати Моя и братия Моя:
Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, “Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana!
50 иже бо аще сотворит волю Отца Моего, Иже есть на небесех, той брат Мой, и сестра, и мати (Ми) есть.
Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata.”