< От Матфея святое благовествование 11 >

1 И бысть, егда соверши Иисус заповедая обеманадесяте ученикома Своима, прейде оттуду учити и проповедати во градех их.
Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi.
2 Иоанн же слышав во узилищи дела Христова, посла два от ученик своих,
Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa.
3 рече Ему: Ты ли еси Грядый, или иного чаем?
Ya ce masa. “Kai ne mai zuwa”? ko mu sa ido ga wani.
4 И отвещав Иисус рече има: шедша возвестита Иоаннови, яже слышита и видита:
Yesu ya amsa ya ce masu, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji.
5 слепии прозирают и хромии ходят, прокаженнии очищаются и глусии слышат, мертвии востают и нищии благовествуют:
Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara.
6 и блажен есть, иже аще не соблазнится о Мне.
Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni.
7 Тема же исходящема, начат Иисус народом глаголати о Иоанне: чесо изыдосте в пустыню видети? Трость ли ветром колеблему?
Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, “Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa?
8 Но чесо изыдосте видети? Человека ли в мягки ризы облеченна? Се, иже мягкая носящии, в домех царских суть.
Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna.
9 Но чесо изыдосте видети? Пророка ли? Ей, глаголю вам, и лишше пророка.
Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi.
10 Сей бо есть, о немже есть писано: се, Аз посылаю Ангела Моего пред лицем Твоим, иже уготовит путь Твой пред Тобою.
Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'.
11 Аминь глаголю вам, не воста в рожденных женами болий Иоанна Крестителя: мний же во Царствии Небеснем болий его есть.
Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma.
12 От дний же Иоанна Крестителя доселе Царствие Небесное нудится, и нуждницы восхищают е:
Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi.
13 вси бо пророцы и закон до Иоанна прорекоша.
Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya.
14 И аще хощете прияти, той есть Илиа хотяй приити:
kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo.
15 имеяй ушы слышати да слышит.
Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji.
16 Кому же уподоблю род сей? Подобен есть детем седящым на торжищих, и возглашающым другом своим
Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna
17 и глаголющым: пискахом вам, и не плясасте: плакахом вам, и не рыдасте.
suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba.
18 Прииде бо Иоанн ни ядый, ни пияй: и глаголют: беса имать.
Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, “Yana da aljannu”.
19 Прииде Сын Человеческий ядый и пияй: и глаголют: се, человек ядца и винопийца, мытарем друг и грешником. И оправдися премудрость от чад своих.
Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita.
20 Тогда начат Иисус поношати градовом, в нихже быша множайшыя силы Его, зане не покаяшася:
Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba.
21 горе тебе, Хоразине, горе тебе, Вифсаидо: яко аще в Тире и Сидоне быша силы были бывшыя в вас, древле убо во вретищи и пепеле покаялися быша:
“Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka.
22 обаче глаголю вам Тиру и Сидону отраднее будет в день судный, неже вам.
Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku.
23 И ты, Капернауме, иже до небес вознесыйся, до ада снидеши: зане аще в Содомех быша силы были бывшыя в тебе, пребыли убо быша до днешняго дне: (Hadēs g86)
Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. (Hadēs g86)
24 обаче глаголю вам, яко земли Содомстей отраднее будет в день судный, неже тебе.
Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku.”
25 В то время отвещав Иисус рече: исповедаютися, Отче, Господи небесе и земли, яко утаил еси сия от премудрых и разумных и открыл еси та младенцем:
A wannan lokaci Yesu ya ce, “Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara.
26 ей, Отче, яко тако бысть благоволение пред Тобою.
I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka.
27 Вся Мне предана суть Отцем Моим: и никтоже знает Сына, токмо Отец: ни Отца кто знает, токмо Сын, и емуже аще волит Сын открыти.
An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa.
28 Приидите ко Мне вси труждающиися и обремененнии, и Аз упокою вы:
Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa.
29 возмите иго Мое на себе и научитеся от Мене, яко кроток есмь и смирен сердцем: и обрящете покой душам вашым:
Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku.
30 иго бо Мое благо, и бремя Мое легко есть.
Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi.”

< От Матфея святое благовествование 11 >