< Послание Иуды 1 >
1 Иуда, Иисуса Христа раб, брат же Иакова, сущым о Бозе Отце освященным, Иисус Христом соблюденным званным:
Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
2 милость вам и мир и любы да умножится.
bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
3 Возлюбленнии, всяко тщание творя писати вам о общем спасении вашем, нужду возимех писати вам, моля подвизатися о преданнеи вере святым единою.
Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
4 Привнидоша бо нецыи человецы, древле предуставленнии на сие осуждение, нечестивии, Бога нашего благодать прелагающии в скверну, и единаго Владыки Бога и Господа нашего Иисуса Христа отметающиися.
Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
5 Воспомянути же вам хощу, ведущым и вам единою сие, яко Господь люди от земли Египетския спасе, последи неверовавшыя погуби:
Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
6 аггелы же не соблюдшыя своего начальства, но оставльшыя свое жилище, на суд великаго дне узами вечными под мраком соблюде. (aïdios )
Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. (aïdios )
7 Якоже Содома и Гоморра и окрестнии их грады, подобным им образом преблудивше и ходивше вслед плоти иныя, предлежат в показание, огня вечнаго суд подемше, (aiōnios )
Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. (aiōnios )
8 такожде убо и сии, сония видяще, плоть убо сквернят, господства же отметаются, славы же хуляще (не трепещут).
Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
9 Михаил же Архангел, егда со диаволом разсуждая глаголаше о Моисеове телеси, не смеяше суда навести хульна, но рече: да запретит тебе Господь.
Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
10 Сии же, елика убо не ведят, хулят: елика же по естеству яко безсловесная животная ведят, в сих сквернятся.
Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
11 Горе им. Яко в путь Каинов поидоша, и в лесть Валаамовы мзды устремишася, и в пререкании Корреове погибоша.
Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
12 Сии суть в любвах ваших сквернители, с вами ядуще, без боязни себе пасуще: облацы безводни, от ветр преносими: древеса есенна, безплодна, дважды умерша, искоренена.
Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
13 Волны свирепыя моря, воспеняющя своя стыдения: звезды прелестныя, имже мрак тьмы во веки блюдется. (aiōn )
Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. (aiōn )
14 Пророчествова же и о сих седмый от Адама Енох, глаголя: се приидет Господь во тьмах святых Ангел Своих,
Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
15 сотворити суд о всех и изобличити всех нечестивых о всех делех нечестия их, имиже нечествоваша, и о всех жестоких словесех их, яже глаголаша Нань грешницы нечестивии.
Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
16 Сии суть ропотницы, укорители, (часть порочна, ) в похотех своих ходяще нечестием и законопреступлением: и уста их глаголют прегордая: чудящеся лицам пользы ради.
Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
17 Вы же, возлюбленнии, поминайте глаголы преждереченныя от Апостол Господа нашего Иисуса Христа.
Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
18 Зане глаголаху вам, яко в последнее время будут ругатели, по своих похотех ходяще и нечестиих.
Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
19 Сии суть отделяюще себе (от единости веры, и суть) телесни, духа не имуще.
Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
20 Вы же, возлюбленнии, стою вашею верою назидающе себе, Духом Святым молящеся,
Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
21 сами себе в любви Божиеи соблюдайте, ждуще милости Господа нашего Иисуса Христа, в жизнь вечную. (aiōnios )
Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. (aiōnios )
22 И овех убо милуйте разсуждающе.
Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
23 Овех же страхом спасайте, от огня восхищающе. Обличайте же с боязнию, ненавидяще и яже от плоти оскверненую ризу.
Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
24 Могущему же сохранити вы без греха и без скверны и поставити пред славою Своею непорочных в радости,
Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
25 Единому Премудрому Богу и Спасу нашему, Иисусом Христом Господем нашим, слава и величие, держава и власть, прежде всего века, и ныне, и во вся веки. Аминь. (aiōn )
zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin. (aiōn )