< От Иоанна святое благовествование 11 >
1 Бе же некто боля Лазарь от Вифании, от веси Мариины и Марфы сестры ея.
To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta.
2 Бе же Мариа помазавшая Господа миром и отершая нозе Его власы своими, еяже брат Лазарь боляше.
Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya.
3 Посласте убо сестре к Нему, глаголюще: Господи, се, егоже любиши, болит.
'Yan'uwannan mata suka aika sako wurin yesu, cewa, “Ubangiji, duba, shi wanda kake kauna yana rashin lafiya”.
4 Слышав же Иисус рече: сия болезнь несть к смерти, но о славе Божии, да прославится Сын Божий ея ради.
Da Yesu ya ji, sai ya ce “Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta”.
5 Любляше же Иисус Марфу и сестру ея и Лазаря.
Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru.
6 Егда же услыша, яко болит, тогда пребысть на немже бе месте два дни.
Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
7 Потом же глагола учеником: идем во Иудею паки.
Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, “Bari mu je Yahudiya kuma.”
8 Глаголаша Ему ученицы: Равви, ныне искаху Тебе камением побити Иудее, и паки ли идеши тамо?
Sai almajiransa suka ce masa, “Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?”
9 Отвеща Иисус: не два ли надесяте часа еста во дни? Аще кто ходит во дни, не поткнется, яко свет мира сего видит:
Yesu ya amsa, “Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya.
10 аще же кто ходит в нощи, поткнется, яко несть света в нем.
Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi.
11 Сия рече и посем глагола им: Лазарь друг наш успе: но иду, да возбужу его.
Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, “Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci”.
12 Реша убо ученицы Его: Господи, аще успе, спасен будет.
Sai almajirai suka ce masa, “Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka.”
13 Рече же Иисус о смерти его: они же мнеша, яко о успении сна глаголет.
Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
14 Тогда рече им Иисус не обинуяся: Лазарь умре:
Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, “Li'azaru ya mutu.
15 и радуюся вас ради, да веруете, яко не бех тамо: но идем к нему.
Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa.”
16 Рече же Фома, глаголемый Близнец, учеником: идем и мы, да умрем с ним.
Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, “Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu.”
17 Пришед же Иисус, обрете его четыри дни уже имуща во гробе.
Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
18 Бе же Вифаниа близ Иерусалима, яко стадий пятьнадесять,
Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su.
19 и мнози от Иудей бяху пришли к Марфе и Марии, да утешат их о брате ею.
Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu.
20 Марфа убо егда услыша, яко Иисус грядет, срете Его: Мариа же дома седяше.
Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida.
21 Рече же Марфа ко Иисусу: Господи, аще бы еси зде был, не бы брат мой умерл:
Matta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba”.
22 но и ныне вем, яко елика аще просиши от Бога, даст Тебе Бог.
Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka.
23 Глагола ей Иисус: воскреснет брат твой.
Yesu ya ce mata, “Dan'uwanki za ya rayu kuma.
24 Глагола Ему Марфа: вем, яко воскреснет в воскрешение, в последний день.
Sai Matta ta ce masa, “Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe.”
25 Рече (же) ей Иисус: Аз есмь воскрешение и живот: веруяй в Мя, аще и умрет, оживет:
Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu;
26 и всяк живый и веруяй в Мя не умрет во веки. Емлеши ли веру сему? (aiōn )
Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?” (aiōn )
27 Глагола Ему: ей, Господи: аз веровах, яко Ты еси Христос Сын Божий, иже в мир грядый.
Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya.
28 И сия рекши, иде и пригласи Марию сестру свою тай, рекши: Учитель пришел есть и глашает тя.
Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, “mallam ya iso, kuma yana kiran ki.”
29 Она (же) яко услыша, воста скоро и иде к Нему.
Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
30 Не уже бо бе пришел Иисус в весь, но бе на месте, идеже срете Его Марфа.
Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
31 Иудее (же) убо сущии с нею в дому и утешающе ю, видевше Марию, яко скоро воста и изыде, по ней идоша, глаголюще, яко идет на гроб, да плачет тамо.
Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
32 Мариа же яко прииде, идеже бе Иисус, видевши Его, паде Ему на ногу, глаголющи Ему: Господи, аще бы еси был зде, не бы умерл мой брат.
Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33 Иисус убо, яко виде ю плачущуся и пришедшыя с нею Иудеи плачущя, запрети духу и возмутися Сам
Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34 и рече: где положисте его? Глаголаша Ему: Господи, прииди и виждь.
sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
36 Глаголаху убо Жидове: виждь, како любляше его.
Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
37 Нецыи же от них реша: не можаше ли Сей, отверзый очи слепому, сотворити, да и сей не умрет?
Amma wadansun su suka ce, “Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
38 Иисус же паки претя в себе, прииде ко гробу. Бе же пещера, и камень лежаше на ней.
Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
39 Глагола Иисус: возмите камень. Глагола Ему сестра умершаго Марфа: Господи, уже смердит: четверодневен бо есть.
Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
40 Глагола ей Иисус: не рех ли ти, яко аще веруеши, узриши славу Божию?
Yesu ya ce mata, “Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?”
41 Взяша убо камень, идеже бе умерый лежя. Иисус же возведе очи горе и рече: Отче, хвалу Тебе воздаю, яко услышал еси Мя:
Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, “Uba, na gode maka domin kana ji na.”
42 Аз же ведех, яко всегда Мя послушаеши: но народа ради стоящаго окрест рех, да веру имут, яко Ты Мя послал еси.
Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni.”
43 И сия рек, гласом великим воззва: Лазаре, гряди вон.
Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, “Li'azaru, ka fito!”
44 И изыде умерый, обязан рукама и ногама укроем, и лице его убрусом обязано. Глагола им Иисус: разрешите его и оставите ити.
Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, “Ku kwance shi, ya tafi”.
45 Мнози убо от Иудей пришедшии к Марии и видевше, яже сотвори Иисус, вероваша в Него:
To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi;
46 нецыи же от них идоша к фарисеом и рекоша им, яже сотвори Иисус.
amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
47 Собраша убо архиерее и фарисее сонм и глаголаху: что сотворим? Яко Человек Сей многа знамения творит:
Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, “menene za mu yi?” Mutumin nan yana alamu masu yawa.
48 аще оставим Его тако, вси уверуют в Него: и приидут Римляне и возмут место и язык наш.
Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu.
49 Един же некто от них Каиафа, архиерей сый лету тому, рече им: вы не весте ничесоже,
Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, “baku san komai ba”.
50 ни помышляете, яко уне есть нам, да един человек умрет за люди, а не весь язык погибнет.
Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka.”
51 Сего же о себе не рече, но архиерей сый лету тому, прорече, яко хотяше Иисус умрети за люди,
Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar;
52 и не токмо за люди, но да и чада Божия расточеная соберет во едино.
kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya.
53 От того убо дне совещаша, да убиют Его.
Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu.
54 Иисус же ктому не яве хождаше во Иудеех, но иде оттуду во страну близ пустыни, во Ефрем нарицаемый град, и ту хождаше со ученики Своими.
Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa.
55 Бе же близ Пасха Иудейска, и взыдоша мнози во Иерусалим от стран прежде Пасхи, да очистятся.
Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su.
56 Искаху убо Иисуса и глаголаху к себе, в церкви стояще: что мнится вам, яко не имать ли приити в праздник?
Suka shiga neman Yesu, suna magana da junan su yayin da suke tsaitsaye a haikali, cewa “me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?”
57 Даша же архиерее и фарисее заповедь, да аще кто ощутит (Его), где будет, повесть, яко да имут Его.
Babban firist da farisawa sun rigaya sun ba da umurni cewa duk inda aka ga Yesu a zo a shaida domin su kama shi.