< Книга пророка Осии 10 >
1 Виноград благолозен Израиль, плод обилен его: по множеству плодов его умножи требища, по благотам земли его возгради капища.
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da’ya’ya wa kansa. Yayinda’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
2 Разделиша сердца своя, ныне погибнут: Сам раскопает требища их, сокрушатся кумиры их.
Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
3 Темже ныне рекут: несть царя в нас, яко не бояхомся Господа: царь же что сотворит нам?
Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?”
4 Глаголяй словеса извинения ложная завещает завет: прозябнет суд аки троскот на лядине селней.
Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
5 У телца Дому Онова возобитают живущии в Самарии, яко плакашася людие его о нем: и якоже разгневаша его, порадуются о славе его, яко преселися от них.
Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
6 И связавше его, во Ассирию отведоша в дар царю Иариму: в дар Ефрем приимется, и усрамится Израиль о совете своем.
Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
7 Отверже Самариа царя своего, аки хврастие на лицы воды.
Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye.
8 Извергутся требища Онова согрешения Израилева, терние и волчец возникнут на требищих их: и рекут к горам: покрыйте ны: и холмом: падите на ны.
Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”
9 Отнележе холми, согреши Израиль: тамо сташа: не постигнет их на холме рать, на чада неправды.
“Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila, a can kuwa kuka ci gaba. Yaƙi bai cimma masu aikata mugunta a Gibeya ba?
10 Прииде наказати их по желанию Моему: и соберутся людие на ня, внегда наказатися им во двою неправдах своих.
Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su; al’ummai za su taru su yi gāba da su don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.
11 Ефрем юница наученая, еже любити прение: Аз же найду на доброту выи ея, наступлю на Ефрема, умолчу о Иуде, укрепится себе Иаков.
Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.
12 Сейте себе в правду, соберите плод живота, просветите себе свет ведения, дондеже время, взыщите Господа, дондеже приидут вам жита правды.
Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.
13 Вскую премолчасте нечестие, и неправды его оымасте, изядосте плод лжив? Яко уповал еси на оружие твое, во множестве силы твоея.
Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa,
14 И востанет пагуба в людех твоих, и вся ограды твоя погибнут, якоже (погибе) князь Саламан от дому Иеровоамля, во дни ратны матерь о чада разбиша:
hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku, saboda a ragargaza kagaranku, kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi, sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da’ya’yansu da ƙasa.
15 тако сотворю вам, Доме Израилев, от лица неправды злоб ваших.
Haka zai faru da kai, ya Betel, domin muguntarka ta yi yawa. Sa’ad da wannan rana ta zo, za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.