< Послание к Евреям 11 >

1 Есть же вера уповаемых извещение, вещей обличение невидимых.
Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al'amuran da idanu basu gani.
2 В сей бо свидетелствовани быша древнии.
Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah.
3 Верою разумеваем совершитися веком глаголголом Божиим, во еже от неявляемых видимым быти. (aiōn g165)
Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba. (aiōn g165)
4 Верою множайшую жертву Авель паче Каина принесе Богу, еюже свидетелствован бысть быти праведник, свидетелствующу о дарех его Богу: и тою умерый еще глаголет.
Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu.
5 Верою Енох преложен бысть не видети смерти: и не обреташеся, зане преложи его Бог: прежде бо преложения его свидетелствован бысть, яко угоди Богу.
Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. “Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi.” Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya.
6 Без веры же невозможно угодити (Богу): веровати же подобает приходящему к Богу, яко есть, и взыскающым Его мздовоздатель бывает.
Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa.
7 Верою ответ приим Ное о сих, яже не у виде, убоявся сотвори ковчег во спасение дому своего: еюже осуди (весь) мир, и правды, яже по вере, бысть наследник.
Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al'amuran da ba'a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya.
8 Верою зовом Авраам послуша изыти на место, еже хотяше прияти в наследие, и изыде не ведый, камо грядет.
Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba.
9 Верою прииде Авраам на землю обетования, якоже на чужду, в кровы вселися со Исааком и Иаковом снаследникома обетования тогожде:
Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi.
10 ждаше бо основания имущаго града, емуже художник и содетель Бог.
Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah.
11 Верою и сама Сарра неплоды силу во удержание семене прият и паче времене возраста роди, понеже верна непщева Обетовавшаго.
Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne.
12 Темже и от единаго родишася, да еще умерщвленнаго, якоже звезды небесныя множеством и яко песок вскрай моря безчисленный.
Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa.
13 По вере умроша сии вси, не приемше обетований, но издалеча видевше я, и целовавше, и исповедавше, яко страннии и пришелцы суть на земли:
Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya.
14 ибо таковая глаголющии являются, яко отечествия взыскуют.
Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu.
15 И аще бы убо оно помнили, из негоже изыдоша, имели бы время возвратитися:
Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa.
16 ныне же лучшаго желают, сиречь небеснаго: темже не стыдится сими Бог, Бог нарицатися их: уготова бо им град.
Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu.
17 Верою приведе Авраам Исаака искушаемь, и единороднаго приношаше, обетования приемый,
Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya.
18 к немуже глаголано бысть: яко о Исааце наречется тебе семя:
Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, “Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka.”
19 помыслив, яко и из мертвых воскресити силен (есть) Бог, темже того и в притче прият.
Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa.
20 Верою о грядущих благослови Исаак Иакова и Исава.
Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba.
21 Верою Иаков умирая коегождо сына Иосифова благослови и поклонися на верх жезла его.
Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa'adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci 'ya'yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa.
22 Верою Иосиф умирая о исхождении сынов Израилевых памятствова и о костех своих заповеда.
Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa'adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar 'ya'yan Isra'ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa.
23 Верою Моисей родився сокровен бысть три месяцы от отец своих, зане видеша красно отроча и не убояшася повеления царева.
Ta dalilin bangaskiya Musa, sa'adda aka haife shi, iyayensa suka 'boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba.
24 Верою Моисей, велик быв, отвержеся нарицатися сын дщере фараоновы:
Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa'adda ya girma, yaki a kira shi 'dan diyar Fir'auna.
25 паче (же) изволи страдати с людьми Божиими, нежели имети временную греха сладость,
A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama'ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci.
26 болшее богатство вменив Египетских сокровищ поношение Христово: взираше бо на мздовоздаяние.
Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba.
27 Верою остави Египет, не убоявся ярости царевы: Невидимаго бо яко видя, терпяше.
Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa
28 Верою сотвори Пасху и пролитие крове, да не погубляяй перворожденная коснется их.
Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka 'ya'yan fari ya taba 'ya'yan fari na Isra'ila.`
29 Верою преидоша Чермное море аки по сусе земли: егоже искушение приемше Египтяне истопишася.
Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa'adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su.
30 Верою стены Иерихонския падоша обхождением седмих дний.
Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai.
31 Верою Раав блудница не погибе с сопротивльшимися, приимши сходники с миром (и иным путем изведши).
Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya.
32 И что еще глаголю? Не достанет бо ми повествующу времене о Гедеоне, Вараце же и Сампсоне и Иеффаи, о Давиде же и Самуиле, и о (других) пророцех,
Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama'ila, da annabawa.
33 иже верою победиша царствия, содеяша правду, получиша обетования, заградиша уста львов,
Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa'annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna,
34 угасиша силу огненную, избегоша острея меча, возмогоша от немощи, быша крепцы во бранех, обратиша в бегство полки чуждих:
suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa'annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al'ummai.
35 прияша жены от воскресения мертвых своих: инии же избиени быша, не приемше избавления, да лучшее воскресение улучат:
Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu.
36 друзии же руганием и ранами искушение прияша, еще же и узами и темницею,
Wadansu kuwa suka sha ba'a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku.
37 камением побиени быша, претрени быша, искушени быша, убийством меча умроша, проидоша в милотех (и) в козиях кожах, лишени, скорбяще, озлоблени:
A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu.
38 ихже не бе достоин (весь) мир, в пустынех скитающеся и в горах и в вертепах и в пропастех земных.
Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka.
39 И сии вси послушествани бывше верою, не прияша обетования,
Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna.
40 Богу лучшее что о нас предзревшу, да не без нас совершенство приимут.
Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.

< Послание к Евреям 11 >