< Деяния святых апостолов 4 >

1 Глаголющым же им к людем, наидоша на них священницы и воевода церковный и саддукее,
Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu.
2 жаляще си, за еже учити им люди и возвещати о Иисусе воскресение мертвых:
Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu.
3 и возложиша на них руки и положиша их в соблюдение до утрия: бе бо вечер уже.
Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi.
4 Мнози же от слышавших слово вероваша: и бысть число мужей яко тысящ пять.
Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya.
5 Бысть же наутрие собратися князем их и старцем и книжником во Иерусалим,
Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima.
6 и Анне архиерею и Каиафе и Иоанну и Александру, и елицы беша от рода архиерейска:
Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist
7 и поставльше их посреде, вопрошаху: коею силою или коим именем сотвористе сие вы?
Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, “Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?”
8 Тогда Петр, исполнився Духа Свята, рече к ним: князи людстии и старцы Израилевы,
Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jama'a,
9 аще мы днесь истязуеми есмы о благодеянии человека немощна, о чесом сей спасеся,
idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya?
10 разумно буди всем вам и всем людем Израилевым, яко во имя Иисуса Христа Назореа, Егоже вы распясте, Егоже Бог воскреси от мертвых, о Сем сей стоит пред вами здрав:
Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye.
11 Сей есть камень укореный от вас зиждущих, бывый во главу угла, и несть ни о единем же инем спасения:
Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini.
12 несть бо иного имене под небесем, даннаго в человецех, о немже подобает спастися нам.
Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.''
13 Видяще же Петрово дерзновение и Иоанново и разумевше, яко человека некнижна еста и проста, дивляхуся, знаху же их, яко со Иисусом беста:
Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu.
14 видяще же исцелевшаго человека с нима стояща, ничтоже имяху противу рещи.
Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi.
15 Повелевше же има вон из сонмища изыти, стязахуся друг со другом,
Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu.
16 глаголюще: что сотворим человекома сима? Яко убо нарочитое знамение бысть има, всем живущым во Иерусалиме яве, и не можем отврещися:
Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka.
17 но да не более прострется в людех, прещением да запретим има ктому не глаголати о имени сем ни единому от человек.
Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.''
18 И призвавше их, заповедаша има отнюд не провещавати ниже учити о имени Иисусове.
Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu.
19 Петр же и Иоанн отвещавша к ним реста: аще праведно есть пред Богом вас послушати паче, нежели Бога, судите:
Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, ''Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta.
20 не можем бо мы, яже видехом и слышахом, не глаголати.
Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.''
21 Они же призапрещше има, пустиша я, ничтоже обретше како мучити их, людий ради, яко вси прославляху Бога о бывшем:
Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22 лет бо бяше множае четыредесяти человек той, на немже бысть чудо сие исцеления.
Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in.
23 Отпущена же бывша приидоста ко своим и возвестиста, елика к нима архиерее и старцы реша.
Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu.
24 Они же слышавше единодушно воздвигоша глас к Богу и рекоша: Владыко, ты, Боже, сотворивый небо и землю и море и вся, яже в них,
Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, ''Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu,
25 иже Духом Святым усты отца нашего Давида отрока Твоего рекл еси: вскую шаташася языцы, и людие поучишася тщетным?
kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza?
26 Предсташа царие земстии, и князи собрашася вкупе на Господа и на Христа Его.
Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.'
27 Собрашася бо воистинну во граде сем на Святаго Отрока Твоего Иисуса, Егоже помазал еси, Ирод же и Понтийский Пилат с языки и людьми Израилевыми,
Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe.
28 сотворити, елика рука Твоя и совет Твой преднарече быти:
Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru.
29 и ныне, Господи, призри на прещения их и даждь рабом Твоим со всяким дерзновением глаголати слово Твое,
Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi.
30 внегда руку Твою прострети Ти во исцеления, и знамением и чудесем бывати именем Святым Отрока Твоего Иисуса.
Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31 И помолившымся им, подвижеся место, идеже бяху собрани, и исполнишася вси Духа Свята и глаголаху слово Божие со дерзновением.
Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi.
32 Народу же веровавшему бе сердце и душа едина, и ни един же что от имений своих глаголаше свое быти, но бяху им вся обща.
Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne.
33 И велиею силою воздаяху свидетелство Апостоли воскресению Господа Иисуса Христа, благодать же бе велия на всех их.
Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu.
34 Не бяше бо нищь ни един в них: елицы бо господие селом или домовом бяху, продающе приношаху цены продаемых
Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar
35 и полагаху при ногах Апостол: даяшеся же коемуждо, егоже аще кто требоваше.
sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa.
36 Иосиа же, нареченный Варнава от Апостол, еже есть сказаемо сын утешения, левит, Кипрянин родом,
Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya).
37 имея село, продав принесе цену и положи пред ногами Апостол.
Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.

< Деяния святых апостолов 4 >