< Jovanu 12 >

1 A Isus prije pashe na šest dana doðe u Vitaniju gdje bješe Lazar što umrije, koga podiže iz mrtvijeh.
Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu.
2 Ondje mu pak zgotoviše veèeru, i Marta služaše, a i Lazar sjeðaše s njim za trpezom;
Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu.
3 A Marija uzevši litru pravoga nardova mnogocjenoga mira pomaza noge Isusove, i otr kosom svojom noge njegove; a kuæa se napuni mirisa od mira.
Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren.
4 Onda reèe jedan od uèenika njegovijeh, Juda Simonov Iskariotski, koji ga poslije izdade:
Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, “
5 Zašto se ovo miro ne prodade za trista groša i ne dade siromasima?
“Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?”
6 A ovo ne reèe što se staraše za siromahe, nego što bješe lupež, i imaše kovèežiæ, i nošaše što se metaše u nj.
Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi.
7 A Isus reèe: ne dirajte u nju; ona je to dohranila za dan mojega pogreba;
Yesu ya ce, “Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta.
8 Jer siromahe svagda imate sa sobom, a mene nemate svagda.
Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba.
9 Razumje pak mnogi narod iz Judeje da je ondje i doðoše ne samo Isusa radi nego i da vide Lazara kojega podiže iz mrtvijeh.
To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu.
10 A glavari sveštenièki dogovoriše se da i Lazara ubiju;
Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima;
11 Jer mnogi njega radi iðahu iz Judeje i vjerovahu Isusa.
domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu.
12 A sjutradan mnogi od naroda koji bješe došao na praznik, èuvši da Isus ide u Jerusalim
Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima,
13 Uzeše grane od finika i iziðoše mu na susret, i vikahu govoreæi: osana! blagosloven koji ide u ime Gospodnje, car Izrailjev.
Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, “Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila.
14 A Isus našavši magare usjede na nj, kao što je pisano:
Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta,
15 Ne boj se kæeri Sionova, evo car tvoj ide sjedeæi na magaretu.
“Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki”.
16 Ali ovo uèenici njegovi ne razumješe prije: nego kad se proslavi Isus onda se opomenuše da ovo bješe za njega pisano, i ovo mu uèiniše.
Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa.
17 A narod svjedoèaše koji bješe prije s njim kad Lazara izazva iz groba i podiže ga iz mrtvijeh.
Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida.
18 Zato ga i srete narod, jer èuše da on uèini ovo èudo.
Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama.
19 A fariseji govorahu meðu sobom: vidite da ništa ne pomaže? gle, svijet ide za njim.
Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa “Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa.
20 A bijahu neki Grci meðu onima koji bijahu došli na praznik da se mole Bogu.
Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin.
21 Oni dakle pristupiše k Filipu, koji bješe iz Vitsaide Galilejske, i moljahu ga govoreæi: gospodine! mi bismo htjeli da vidimo Isusa.
Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, “Mallam, muna so mu ga Yesu.
22 Doðe Filip i kaza Andriji, a Andrija i Filip opet kazaše Isusu.
Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu.
23 A Isus odgovori im govoreæi: doðe èas da se proslavi sin èovjeèij.
Yesu ya amsa masu ya ce, “sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum.
24 Zaista, zaista vam kažem: ako zrno pšenièno padnuvši na zemlju ne umre, onda jedno ostane; ako li umre mnogo roda rodi:
Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa.
25 Koji ljubi dušu svoju izgubiæe je, a ko mrzi na dušu svoju na ovom svijetu, saèuvaæe je za život vjeèni. (aiōnios g166)
Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada. (aiōnios g166)
26 Ko meni služi, za mnom nek ide, i gdje sam ja ondje i sluga moj neka bude; i ko meni služi onoga æe poštovati otac moj.
Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi.
27 Sad je duša moja žalosna; i šta da kažem? Oèe! saèuvaj me od ovoga èasa; ali zato doðoh na èas ovaj.
Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a.
28 Oèe! proslavi ime svoje! Tada glas doðe s neba: i proslavio sam, i opet æu proslaviti.
Uba, ka daukaka sunanka”. Sai wata murya daga sama ta ce, “Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi.
29 A kad èu narod koji stajaše, govorahu: grom zagrmi; a drugi govorahu: anðeo mu govori.
Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, “Mala'ika ya yi magana da shi”.
30 Isus odgovori i reèe: ovaj glas ne bi mene radi nego naroda radi.
Yesu ya amsa ya ce, “wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku.”
31 Sad je sud ovome svijetu; sad æe biti istjeran knez ovoga svijeta napolje.
Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan.
32 I kad ja budem podignut od zemlje, sve æu privuæi k sebi.
Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni”.
33 A ovo govoraše da pokaže kakvom æe smrti umrijeti.
Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi.
34 Narod mu odgovori: mi èusmo iz zakona da æe Hristos ostati vavijek; kako ti govoriš da se sinu èovjeèijemu valja podignuti? Ko je taj sin èovjeèij? (aiōn g165)
Taro suka amsa masa cewa, “Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?” (aiōn g165)
35 A Isus im reèe: još je malo vremena vidjelo s vama; hodite dok vidjelo imate da vas tama ne obuzme; jer ko hodi po tami ne zna kuda ide.
Yesu ya ce masu, “Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba.
36 Dok vidjelo imate vjerujte vidjelo, da budete sinovi vidjela. Rekavši ovo Isus otide i sakri se od njih.
Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske”. Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu.
37 Ako je i èinio tolika èudesa pred njima, opet ga ne vjerovahu;
Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba.
38 Da se zbude rijeè Isaije proroka koji reèe: Gospode! ko vjerova govorenju našemu? i ruka Gospodnja kome se otkri?
Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
39 Zato ne mogahu vjerovati, jer opet reèe Isaija:
Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa,
40 Zaslijepio je oèi njihove i okamenio srca njihova, da ne vide oèima ni srcem razumiju, i ne obrate se da ih iscijelim.
ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su.
41 Ovo reèe Isaija kad vidje slavu njegovu i govori za njega.
Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi.
42 Ali opet i od knezova mnogi ga vjerovaše; nego radi fariseja ne priznavahu, da ne bi bili izgnani iz zbornice;
Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a.
43 Jer im veæma omilje slava ljudska nego slava Božija.
Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah.
44 A Isus povika i reèe: ko mene vjeruje ne vjeruje mene, nego onoga koji me posla;
Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, “Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni,
45 I ko vidi mene vidi onoga koji me posla.
kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni.
46 Ja doðoh vidjelo na svijet, da nijedan koji me vjeruje ne ostane u tami.
Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba.
47 I ko èuje moje rijeèi i ne vjeruje, ja mu neæu suditi; jer ja ne doðoh da sudim svijetu, nego da spasem svijet.
Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya.
48 Koji se odrièe mene, i ne prima rijeèi mojijeh, ima sebi sudiju: rijeè koju ja govorih ona æe mu suditi u pošljednji dan;
Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe.
49 Jer ja od sebe ne govorih, nego otac koji me posla on mi dade zapovijest šta æu kazati i šta æu govoriti.
Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi.
50 I znam da je zapovijest njegova život vjeèni. Što ja dakle govorim onako govorim kao što mi reèe otac. (aiōnios g166)
Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi.” (aiōnios g166)

< Jovanu 12 >