< 2 Solunjanima 3 >

1 Dalje, braæo, molite se Bogu za nas da rijeè Gospodnja trèi, i da se slavi kao i meðu vama;
Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku.
2 I da se izbavimo od besputnijeh i zlijeh ljudi; jer vjera nije sviju,
Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba.
3 A Gospod je vjeran, koji æe vas utvrditi i saèuvati oda zla.
Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun.
4 A uzdamo se u Gospoda za vas da ono što vam zapovijedamo i èinite i èiniæete.
Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta.
5 A Gospod da upravi srca vaša na ljubav Božiju i na trpljenje Hristovo.
Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu.
6 Zapovijedamo vam pak, braæo, u ime Gospoda našega Isusa Hrista, da se odvojite od svakoga brata koji živi neuredno, a ne po uredbi koju primiše od nas.
Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba.
7 Jer sami znate kako treba da se ugledate na nas, jer ne življesmo neuredno meðu vama,
Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba.
8 Niti zabadava hljeb jedosmo u koga, nego u trudu i u poslu, dan i noæ radeæi, da ne budemo na dosadu nikome od vas.
Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi.
9 Ne kao da nemamo vlasti, nego da sebe damo vama za ugled, da budete kao i mi.
Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu.
10 Jer kad bijasmo u vas, ovo vam zapovijedasmo da ako ko neæe da radi da i ne jede.
Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, “Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci.”
11 Jer èujemo da neki neuredno žive meðu vama, ništa ne radeæi, nego okrajèe i miješaju se u tuðe poslove.
Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu.
12 Takovima zapovijedamo i molimo ih u Gospodu našemu Isusu Hristu da mirno radeæi svoj hljeb jedu.
Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su.
13 A vama, braæo, da ne dotuži dobro èiniti.
Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai.
14 A ako ko ne posluša rijeèi naše, onoga poslanicom naznaèite, i ne miješajte se s njim, da se posrami.
In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya.
15 Ali ga ne držite kao neprijatelja, nego ga svjetujte kao brata.
Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa.
16 A sam Gospod mira da vam da mir svagda u svakom dogaðaju. Gospod sa svima vama.
Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.
17 Pozdrav mojom rukom Pavlovom, koje je znak u svakoj poslanici, ovako pišem:
Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu.
18 Blagodat Gospoda našega Isusa Hrista sa svima vama. Amin.
Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.

< 2 Solunjanima 3 >