< 1 Samuelova 2 >

1 I Ana se pomoli i reèe: razveseli se srce moje u Gospodu; podiže se rog moj u Gospodu; otvoriše se usta moja na neprijatelje moje, jer sam radosna radi spasenja tvojega.
Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce, “Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji; a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai. Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya. Kai! Ina murna domin ka cece ni!
2 Nema svetoga kao što je Gospod; jer nema drugoga osim tebe; i nema stijene kao što je Bog naš.
“Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji babu wani, in ban da kai; babu wani dutse kamar Allahnmu.
3 Ne govorite više ponosito, i neka ne izlaze iz usta vaših rijeèi ohole; jer je Gospod Bog koji sve zna, i on udešava namjere.
“Ka daina maganganu na girman kai ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai; gama Ubangiji Allah ne masani daga gare shi kuma ana auna ayyuka.
4 Luk junacima slomi se, i iznemogli opasaše se snagom.
“An kakkarya bakkuna masu yaƙi, amma su da ka raunana an ba su makaman ƙarfi.
5 Koji bijahu siti, naimaju se za hljeb; a koji bijahu gladni, nijesu više; i nerotkinja rodi sedmoro, a koja imaše djece, iznemože.
Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci, masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Ita da take bakararriya, ta haifi’ya’ya bakwai amma ita da tana da’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki.
6 Gospod ubija, i oživljuje; spušta u grob, i izvlaèi. (Sheol h7585)
“Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da. (Sheol h7585)
7 Gospod siromaši, i bogati; ponižuje, i uzvišuje.
Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.
8 Siromaha podiže iz praha, i iz bunjišta uzvišuje ubogoga da ga posadi s knezovima, i daje im da naslijede prijesto slave; jer su Gospodnji temelji zemaljski, i na njima je osnovao vasiljenu.
Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.
9 Saèuvaæe noge milijeh svojih, a bezbožnici æe umuknuti u mraku; jer svojom snagom neæe èovjek nadjaèati.
Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;
10 Koji se suprote Gospodu, satræe se; na njih æe zagrmjeti s neba; Gospod æe suditi krajevima zemaljskim, i daæe snagu caru svojemu, i uzvisiæe rog pomazaniku svojemu.
waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka. Zai yi musu tsawa daga sama, Ubangiji zai hukunta dukan duniya. “Zai ba wa sarkinsa ƙarfi, yă kuma ɗaukaka shafaffensa.”
11 Potom otide Elkana u Ramat kuæi svojoj, a dijete služaše Gospodu pred Ilijem sveštenikom.
Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist.
12 A sinovi Ilijevi bijahu nevaljali, i ne znadijahu za Gospoda.
’Ya’yan Eli firist, mutane ne masu mugunta. Ba su ɗauki Ubangiji a bakin kome ba.
13 Jer u tijeh sveštenika bješe obièaj prema narodu: kad ko prinošaše žrtvu, dolažaše momak sveštenikov dok se kuhaše meso s viljuškama trokrakim u ruci,
Al’ada ce ga firistoci da mutane cewa in wani ya miƙa hadaya, yayinda nama yake kan wuta, bawan firist zai zo da babban cokali mai yatsu,
14 I zabadaše u sud, ili u kotao, ili u tavu, ili u lonac, i što se god nabode na viljuške uzimaše sveštenik. Tako èinjahu svemu Izrailju koji dolažaše u Silom.
zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo.
15 Tako i prije nego bi zapalili salo, došao bi momak sveštenikov, te bi rekao èovjeku koji prinošaše žrtvu: daj meso da ispeèem svešteniku, jer ti neæu primiti mesa kuhana, nego sirovo.
Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.”
16 Ako bi mu tada èovjek odgovorio: neka se prvo zapali salo, pa onda uzmi što ti god duša želi; on bi rekao: ne, nego daj sada, ako li ne daš, uzeæu silom.
In kuwa mutumin ya ce masa, “Bari kitse yă ƙone tukuna, sa’an nan ka ɗiba duk abin da kake so.” Sai bawan yă ce masa, “A’a, ka ba ni yanzu, in ka ƙi kuwa zan ɗiba ƙarfi da yaji.”
17 I grijeh onijeh mladiæa bijaše vrlo velik pred Gospodom, jer ljudi ne marahu za prinos Gospodnji.
Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske.
18 A Samuilo služaše pred Gospodom još dijete u opleæku lanenom.
Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin.
19 A mati mu naèini mali plašt i donese mu, i tako èinjaše svake godine dolazeæi s mužem svojim da prinese žrtvu godišnju.
Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara.
20 A Ilije blagoslovi Elkanu i ženu njegovu govoreæi: Gospod da ti da poroda od te žene za ovoga kojega je dala Gospodu! I otidoše u svoje mjesto.
Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida.
21 I Gospod pohodi Anu, i ona zatrudnje i rodi tri sina i dvije kæeri. A dijete Samuilo rastijaše pred Gospodom.
Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.
22 A Ilije bijaše vrlo star, i èu sve što èinjahu sinovi njegovi svemu Izrailju, i kako spavahu sa ženama koje dolažahu gomilama na vrata šatora od sastanka.
To, Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin labari duk abin da’ya’yansa suke yi wa dukan Isra’ila, da yadda suke lalata da matan da suke hidima a bakin ƙofar Tentin Sujada.
23 I govoraše im: zašto to radite? jer èujem zle rijeèi o vama od svega naroda.
Saboda haka ya ce musu, “Don me kuke yin waɗannan abubuwa? Na sami labari daga wurin mutane a kan duk ayyukan muguntanku.
24 Nemojte, djeco moja; jer nije dobro što èujem; otpaðujete narod Gospodnji.
A’a,’ya’yana ba labari mai kyau nake ji cikin mutanen Ubangiji ba.
25 Kad èovjek zgriješi èovjeku, sudiæe mu sudija; ali kad ko zgriješi Gospodu, ko æe moliti za nj? Ali ne poslušaše oca svojega, jer Gospod šæaše da ih ubije.
In mutum ya yi wa wani laifi Allah yakan kāre shi; amma in mutum ya yi wa Ubangiji zunubi wa zai kāre shi?” Duk da haka,’ya’yansa ba su kula da gargaɗin mahaifinsu ba, domin nufin Ubangiji ne yă hallaka su.
26 A dijete Samuilo rastijaše i bijaše mio i Gospodu i ljudima.
Yaron nan Sama’ila ya dinga girma cikin kwarjini da cikin tagomashi a gaba Ubangiji da mutane.
27 Tada doðe èovjek Božji k Iliju, i reèe mu: ovako veli Gospod: ne javih li se domu oca tvojega, kad bijahu u Misiru u kuæi Faraonovoj?
Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?
28 I izabrah ga izmeðu svijeh plemena Izrailjevijeh sebi za sveštenika da prinosi žrtve na oltaru mojem i da kadi kadom i nosi opleæak preda mnom, i dadoh domu oca tvojega sve žrtve ognjene sinova Izrailjevijeh?
Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.
29 Zašto gazite žrtvu moju i prinos moj, koje sam zapovjedio da se prinose u šatoru? i paziš sinove svoje veæma nego mene, da se gojite prvinama svijeh prinosa Izrailja naroda mojega?
Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’
30 Zato Gospod Bog Izrailjev kaže: rekao sam doista: dom tvoj i dom oca tvojega služiæe preda mnom dovijeka; ali kaže Gospod: neæe biti tako, jer one æu poštovati koji mene poštuju, a koji mene preziru, biæe prezreni.
“Saboda haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na yi alkawari cewa gidanka da gidan mahaifinka za su yi mini hidima a gabana har abada.’ Amma, yanzu Allah ya ce, ba zai yiwu ba; waɗanda suke girmama ni; Ni ma zan girmama su. Amma waɗanda suke ƙasƙantar da ni, haka za a ƙasƙantar da su.
31 Gle, idu dani, kad æu odsjeæi tebi ruku i ruku domu oca tvojega, da ne bude starca u domu tvojem.
Lokaci yana zuwa sa’ad da zan rage ƙarfinka da ƙarfin iyalin gidan mahaifinka. Domin kada a sāke samun tsohon mutum a zuriyarka.
32 I vidjeæeš nevolju u šatoru mjesto svega dobra što je Gospod èinio Izrailju; neæe biti starca u domu tvojem dovijeka.
Za ka zama da ɓacin rai a mazaunina ko da yake za a yi wa Isra’ila alheri. A zuriyarka ba za a taɓa samun tsohon mutum ba.
33 A koga od tvojih ne istrijebim ispred oltara svojega, onaj æe ostati da ti èile oèi i da ti se cvijeli duša; i sav podmladak doma tvojega umiraæe u najboljim godinama.
Kowannenku da ban kashe daga hidima a bagadena ba, za a bar shi don yă cika idanunka da hawaye da kuma baƙin ciki, dukan sauran zuriyarka kuwa za su mutu a ƙuruciyarsu.
34 I ovo da ti je znak što æe doæi na oba sina tvoja, na Ofnija i Finesa: u jedan dan poginuæe obojica.
“‘Abin da kuma ya faru da’ya’yanka biyu Hofni da Finehas zai zama alama a gare ka; saboda mutuwarsu za tă zama a rana ɗaya.
35 A sebi æu podignuti sveštenika vjerna, on æe raditi po srcu mojemu i po duši mojoj; i sazidaæu mu tvrd dom, i on æe hoditi pred pomazanikom mojim vazda.
Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.
36 I ko ostane od doma tvojega, doæi æe da mu se pokloni za srebrn novac i za komad hljeba, i govoriæe: primi me u kaku službu sveštenièku da imam komad hljeba.
Sa’an nan duk wanda ya rage a zuriyarka zai zo yă durƙusa a gabansa yă roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa yă taimaki firistoci da aiki domin yă sami abin da zai ci.’”

< 1 Samuelova 2 >