< པྲཀཱཤིཏཾ 11 >

1 ཨནནྟརཾ པརིམཱཎདཎྜཝད྄ ཨེཀོ ནལོ མཧྱམདཱཡི, ས ཙ དཱུཏ ཨུཔཏིཥྛན྄ མཱམ྄ ཨཝདཏ྄, ཨུཏྠཱཡེཤྭརསྱ མནྡིརཾ ཝེདཱིཾ ཏཏྲཏྱསེཝཀཱཾཤྩ མིམཱིཥྭ།
Aka bani sanda in yi amfani da ita kamar sandar awo. Aka ce mani, “Tashi ka auna haikalin Allah da bagadi, da wadanda ke sujada a cikinsa.
2 ཀིནྟུ མནྡིརསྱ བཧིཿཔྲཱངྒཎཾ ཏྱཛ ན མིམཱིཥྭ ཡཏསྟད྄ ཨནྱཛཱཏཱིཡེབྷྱོ དཏྟཾ, པཝིཏྲཾ ནགརཉྩ དྭིཙཏྭཱརིཾཤནྨཱསཱན྄ ཡཱཝཏ྄ ཏེཥཱཾ ཙརཎཻ རྨརྡྡིཥྱཏེ།
Amma kada ka auna harabar haikalin, domin an ba da shi ga Al'ummai. Za su tattake birnin mai tsarki har wata arba'in da biyu.
3 པཤྩཱཏ྄ མམ དྭཱབྷྱཱཾ སཱཀྵིབྷྱཱཾ མཡཱ སཱམརྠྱཾ དཱཡིཥྱཏེ ཏཱཝུཥྚྲལོམཛཝསྟྲཔརིཧིཏཽ ཥཥྛྱདྷིཀདྭིཤཏཱདྷིཀསཧསྲདིནཱནི ཡཱཝད྄ བྷཝིཥྱདྭཱཀྱཱནི ཝདིཥྱཏཿ།
Zan ba shaidu na biyu iko su yi anabci na kwanaki dubu daya da dari biyu da sittin, sanye da tsummoki.
4 ཏཱཝེཝ ཛགདཱིཤྭརསྱཱནྟིཀེ ཏིཥྛནྟཽ ཛིཏཝྲྀཀྵཽ དཱིཔཝྲྀཀྵཽ ཙ།
Wadannan shaidu sune itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya.
5 ཡདི ཀེཙིཏ྄ ཏཽ ཧིཾསིཏུཾ ཙེཥྚནྟེ ཏརྷི ཏཡོ ཪྻདནཱབྷྱཱམ྄ ཨགྣི རྣིརྒཏྱ ཏཡོཿ ཤཏྲཱུན྄ བྷསྨཱིཀརིཥྱཏི། ཡཿ ཀཤྩིཏ྄ ཏཽ ཧིཾསིཏུཾ ཙེཥྚཏེ ཏེནཻཝམེཝ ཝིནཥྚཝྱཾ།
Idan wani ya yi niyyar cutar da su, wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu. Duk mai son cutar da su, dole a kashe shi ta wannan hanya.
6 ཏཡོ རྦྷཝིཥྱདྭཱཀྱཀཐནདིནེཥུ ཡཐཱ ཝྲྀཥྚི རྣ ཛཱཡཏེ ཏཐཱ གགནཾ རོདྡྷུཾ ཏཡོཿ སཱམརྠྱམ྄ ཨསྟི, ཨཔརཾ ཏོཡཱནི ཤོཎིཏརཱུཔཱཎི ཀརྟྟུཾ ནིཛཱབྷིལཱཥཱཏ྄ མུཧུརྨུཧུཿ སཪྻྭཝིདྷདཎྜཻཿ པྲྀཐིཝཱིམ྄ ཨཱཧནྟུཉྩ ཏཡོཿ སཱམརྠྱམསྟི།
Wadannan shaidu suna da iko su kulle sama domin kada a yi ruwa a lokacin da suke anabci. Suna da iko su juya ruwaye su zama jini, su kuma bugi duniya da kowacce irin annoba duk lokacin da suka ga dama.
7 ཨཔརཾ ཏཡོཿ སཱཀྵྱེ སམཱཔྟེ སཏི རསཱཏལཱད྄ ཡེནོཏྠིཏཝྱཾ ས པཤུསྟཱབྷྱཱཾ སཧ ཡུདྡྷྭཱ ཏཽ ཛེཥྱཏི ཧནིཥྱཏི ཙ། (Abyssos g12)
Sa'adda suka gama shaidarsu, dabban da ke fitowa daga rami marar iyaka zai yi yaki da su. Zai ci nasara da su ya kashe su. (Abyssos g12)
8 ཏཏསྟཡོཿ པྲབྷུརཔི ཡསྱཱཾ མཧཱཔུཪྻྱཱཾ ཀྲུཤེ ཧཏོ ྅རྠཏོ ཡསྱཱཿ པཱརམཱརྠིཀནཱམནཱི སིདོམཾ མིསརཤྩེཏི ཏསྱཱ མཧཱཔུཪྻྱཱཾཿ སནྣིཝེཤེ ཏཡོཿ ཀུཎཔེ སྠཱསྱཏཿ།
Gawawwakinsu zasu kwanta kan hanyar babban birnin nan (wanda ma'anar sa ake kira Saduma da Masar) inda aka gicciye Ubangijinsu.
9 ཏཏོ ནཱནཱཛཱཏཱིཡཱ ནཱནཱཝཾཤཱིཡཱ ནཱནཱབྷཱཥཱཝཱདིནོ ནཱནཱདེཤཱིཡཱཤྩ བཧཝོ མཱནཝཱཿ སཱརྡྡྷདིནཏྲཡཾ ཏཡོཿ ཀུཎཔེ ནིརཱིཀྵིཥྱནྟེ, ཏཡོཿ ཀུཎཔཡོཿ ཤྨཤཱནེ སྠཱཔནཾ ནཱནུཛྙཱསྱནྟི།
Wajen kwana uku da rabi wadansu daga dukan mutane, da kabila, da harshe, da al'umma za su yi kallon gawawwakinsu. Za su ki yarda a sa su cikin kabari.
10 པྲྀཐིཝཱིནིཝཱསིནཤྩ ཏཡོ རྷེཏོརཱནནྡིཥྱནྟི སུཁབྷོགཾ ཀུཪྻྭནྟཿ པརསྤརཾ དཱནཱནི པྲེཥཡིཥྱནྟི ཙ ཡཏསྟཱབྷྱཱཾ བྷཝིཥྱདྭཱདིབྷྱཱཾ པྲྀཐིཝཱིནིཝཱསིནོ ཡཱཏནཱཾ པྲཱཔྟཱཿ།
Mazaunan duniya zasu yi murna da biki a kansu. Har za su aika wa juna kyautai saboda annabawan nan biyu da suka azabtar da mazaunan duniya.
11 ཏསྨཱཏ྄ སཱརྡྡྷདིནཏྲཡཱཏ྄ པརམ྄ ཨཱིཤྭརཱཏ྄ ཛཱིཝནདཱཡཀ ཨཱཏྨནི ཏཽ པྲཝིཥྚེ ཏཽ ཙརཎཻརུདཏིཥྛཏཱཾ, ཏེན ཡཱཝནྟསྟཱཝཔཤྱན྄ ཏེ ྅ཏཱིཝ ཏྲཱསཡུཀྟཱ ཨབྷཝན྄།
Amma bayan kwana uku da rabi, numfanshin rai daga wurin Allah zai shiga cikinsu sa'annan za su tsaya a kan kafafunsu. Matsanancin tsoro zata fado kan wadanda za su gansu.
12 ཏཏཿ པརཾ ཏཽ སྭརྒཱད྄ ཨུཙྩཻརིདཾ ཀཐཡནྟཾ རཝམ྄ ཨཤྲྀཎུཏཱཾ ཡུཝཱཾ སྠཱནམ྄ ཨེཏད྄ ཨཱརོཧཏཱཾ ཏཏསྟཡོཿ ཤཏྲུཥུ ནིརཱིཀྵམཱཎེཥུ ཏཽ མེགྷེན སྭརྒམ྄ ཨཱརཱུཌྷཝནྟཽ།
Sa'annan zasu ji murya mai kara daga sama tana ce masu, “Ku hauro nan!” Sa'annan za su tafi sama cikin gajimarai, makiyansu suna kallo.
13 ཏདྡཎྜེ མཧཱབྷཱུམིཀམྤེ ཛཱཏེ པུཪྻྱཱ དཤམཱཾཤཿ པཏིཏཿ སཔྟསཧསྲཱཎི མཱནུཥཱཤྩ ཏེན བྷཱུམིཀམྤེན ཧཏཱཿ, ཨཝཤིཥྚཱཤྩ བྷཡཾ གཏྭཱ སྭརྒཱིཡེཤྭརསྱ པྲཤཾསཱམ྄ ཨཀཱིརྟྟཡན྄།
A waccan sa'a za a yi babbar girgizar kasa, sai kashi daya cikin goma na garin ya fadi. Mutane dubu bakwai za su mutu a girgizar kasar, wadanda suka tsira kuwa za su tsorata su ba da daukaka ga Allah na sama.
14 དྭིཏཱིཡཿ སནྟཱཔོ གཏཿ པཤྱ ཏྲྀཏཱིཡཿ སནྟཱཔསྟཱུརྞམ྄ ཨཱགཙྪཏི།
Annoba ta biyu ta wuce. Duba! Annoba ta uku tana zuwa nan da nan.
15 ཨནནྟརཾ སཔྟདཱུཏེན ཏཱུཪྻྱཱཾ ཝཱདིཏཱཡཱཾ སྭརྒ ཨུཙྩཻཿ སྭརཻཪྻཱགིཡཾ ཀཱིརྟྟིཏཱ, རཱཛཏྭཾ ཛགཏོ ཡདྱད྄ རཱཛྱཾ ཏདདྷུནཱབྷཝཏ྄། ཨསྨཏྤྲབྷོསྟདཱིཡཱབྷིཥིཀྟསྱ ཏཱརཀསྱ ཙ། ཏེན ཙཱནནྟཀཱལཱིཡཾ རཱཛཏྭཾ པྲཀརིཥྱཏེ༎ (aiōn g165)
Sa'annan mala'ika na bakwai ya busa kahonsa, sai muryoyi masu kara suka yi magana cikin sama cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa. Zai yi mulki har abada abadin.” (aiōn g165)
16 ཨཔརམ྄ ཨཱིཤྭརསྱཱནྟིཀེ སྭཀཱིཡསིཾཧཱསནེཥཱུཔཝིཥྚཱཤྩཏུཪྻིཾཤཏིཔྲཱཙཱིནཱ བྷུཝི ནྱངྦྷཱུཁཱ བྷཱུཏྭེཤྭརཾ པྲཎམྱཱཝདན྄,
Sa'annan dattawan nan ashirin da hudu da ke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fadi fuskokinsu na kasa. Suka yi wa Allah sujada.
17 ཧེ བྷཱུཏ ཝརྟྟམཱནཱཔི བྷཝིཥྱཾཤྩ པརེཤྭར། ཧེ སཪྻྭཤཀྟིམན྄ སྭཱམིན྄ ཝཡཾ ཏེ ཀུརྨྨཧེ སྟཝཾ། ཡཏ྄ ཏྭཡཱ ཀྲིཡཏེ རཱཛྱཾ གྲྀཧཱིཏྭཱ ཏེ མཧཱབལཾ།
Suka ce, “Mun yi maka godiya, Ubangiji Allah, Madaukaki, wanda yake yanzu da wanda yake a da, saboda ka dauki ikonka mai girma ka fara mulki.
18 ཝིཛཱཏཱིཡེཥུ ཀུཔྱཏྶུ པྲཱདུརྦྷཱུཏཱ ཏཝ ཀྲུདྷཱ། མྲྀཏཱནཱམཔི ཀཱལོ ྅སཽ ཝིཙཱརོ བྷཝིཏཱ ཡདཱ། བྷྲྀཏྱཱཤྩ ཏཝ ཡཱཝནྟོ བྷཝིཥྱདྭཱདིསཱདྷཝཿ། ཡེ ཙ ཀྵུདྲཱ མཧཱནྟོ ཝཱ ནཱམཏསྟེ ཧི བིབྷྱཏི། ཡདཱ སཪྻྭེབྷྱ ཨེཏེབྷྱོ ཝེཏནཾ ཝིཏརིཥྱཏེ། གནྟཝྱཤྩ ཡདཱ ནཱཤོ ཝསུདྷཱཡཱ ཝིནཱཤཀཻཿ༎
Al'ummai suka fusata, amma hasalar ka ta zo. Lokaci ya zo da za a yi wa mattatu sharia, da zaka ba da sakamako ga bayinka annabawa, da masu ba da gaskiya, da wadanda suka ji tsoron sunanka, karami da babba. Lokaci kuma ya yi da za ka hallaka wadanda ke hallakar da duniya.”
19 ཨནནྟརམ྄ ཨཱིཤྭརསྱ སྭརྒསྠམནྡིརསྱ དྭཱརཾ མུཀྟཾ ཏནྨནྡིརམདྷྱེ ཙ ནིཡམམཉྫཱུཥཱ དྲྀཤྱཱབྷཝཏ྄, ཏེན ཏཌིཏོ རཝཱཿ སྟནིཏཱནི བྷཱུམིཀམྤོ གུརུཏརཤིལཱཝྲྀཥྚིཤྩཻཏཱནི སམབྷཝན྄།
Sa'annan aka bude haikalin Allah da ke sama, sai aka ga akwatin alkawarinsa a cikin haikalinsa. Sai ga hasken walkiya, da rugugi, da aradu, da girgizar kasa, da manyan duwatsun kankara.

< པྲཀཱཤིཏཾ 11 >