< མཐིཿ 3 >

1 ཏདཱནོཾ ཡོཧྣྣཱམཱ མཛྫཡིཏཱ ཡིཧཱུདཱིཡདེཤསྱ པྲཱནྟརམ྄ ཨུཔསྠཱཡ པྲཙཱརཡན྄ ཀཐཡཱམཱས,
A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa,
2 མནཱཾསི པརཱཝརྟྟཡཏ, སྭརྒཱིཡརཱཛཏྭཾ སམཱིཔམཱགཏམ྄།
“Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.”
3 པརམེཤསྱ པནྠཱནཾ པརིཥྐུརུཏ སཪྻྭཏཿ། ཏསྱ རཱཛཔཐཱཾཤྩཻཝ སམཱིཀུརུཏ སཪྻྭཐཱ། ཨིཏྱེཏཏ྄ པྲཱནྟརེ ཝཱཀྱཾ ཝདཏཿ ཀསྱཙིད྄ རཝཿ༎
Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa.''
4 ཨེཏདྭཙནཾ ཡིཤཡིཡབྷཝིཥྱདྭཱདིནཱ ཡོཧནམུདྡིཤྱ བྷཱཥིཏམ྄། ཡོཧནོ ཝསནཾ མཧཱངྒརོམཛཾ ཏསྱ ཀཊཽ ཙརྨྨཀཊིབནྡྷནཾ; ས ཙ ཤཱུཀཀཱིཊཱན྄ མདྷུ ཙ བྷུཀྟཝཱན྄།
Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji.
5 ཏདཱནཱིཾ ཡིརཱུཤཱལམྣགརནིཝཱསིནཿ སཪྻྭེ ཡིཧཱུདིདེཤཱིཡཱ ཡརྡྡནྟཊིནྱཱ ཨུབྷཡཏཊསྠཱཤྩ མཱནཝཱ བཧིརཱགཏྱ ཏསྱ སམཱིཔེ
Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa.
6 སྭཱིཡཾ སྭཱིཡཾ དུརིཏམ྄ ཨངྒཱིཀྲྀཏྱ ཏསྱཱཾ ཡརྡྡནི ཏེན མཛྫིཏཱ བབྷཱུཝུཿ།
Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu.
7 ཨཔརཾ བཧཱུན྄ ཕིརཱུཤིནཿ སིདཱུཀིནཤྩ མནུཛཱན྄ མཾཀྟུཾ སྭསམཱིཔམ྄ ཨཱགཙྪྟོ ཝིལོཀྱ ས ཏཱན྄ ཨབྷིདདྷཽ, རེ རེ བྷུཛགཝཾཤཱ ཨཱགཱམཱིནཿ ཀོཔཱཏ྄ པལཱཡིཏུཾ ཡུཥྨཱན྄ ཀཤྩེཏིཏཝཱན྄?
Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa?
8 མནཿཔརཱཝརྟྟནསྱ སམུཙིཏཾ ཕལཾ ཕལཏ།
Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku.
9 ཀིནྟྭསྨཱཀཾ ཏཱཏ ཨིབྲཱཧཱིམ྄ ཨསྟཱིཏི སྭེཥུ མནཿསུ ཙཱིནྟཡནྟོ མཱ ཝྱཱཧརཏ། ཡཏོ ཡུཥྨཱན྄ ཨཧཾ ཝདཱམི, ཨཱིཤྭར ཨེཏེབྷྱཿ པཱཥཱཎེབྷྱ ཨིབྲཱཧཱིམཿ སནྟཱནཱན྄ ཨུཏྤཱདཡིཏུཾ ཤཀྣོཏི།
Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan.
10 ཨཔརཾ པཱདཔཱནཱཾ མཱུལེ ཀུཋཱར ཨིདཱནཱིམཔི ལགན྄ ཨཱསྟེ, ཏསྨཱད྄ ཡསྨིན྄ པཱདཔེ ཨུཏྟམཾ ཕལཾ ན བྷཝཏི, ས ཀྲྀཏྟོ མདྷྱེ྅གྣིཾ ནིཀྵེཔྶྱཏེ།
Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
11 ཨཔརམ྄ ཨཧཾ མནཿཔརཱཝརྟྟནསཱུཙཀེན མཛྫནེན ཡུཥྨཱན྄ མཛྫཡཱམཱིཏི སཏྱཾ, ཀིནྟུ མམ པཤྩཱད྄ ཡ ཨཱགཙྪཏི, ས མཏྟོཔི མཧཱན྄, ཨཧཾ ཏདཱིཡོཔཱནཧཽ ཝོཌྷུམཔི ནཧི ཡོགྱོསྨི, ས ཡུཥྨཱན྄ ཝཧྣིརཱུཔེ པཝིཏྲ ཨཱཏྨནི སཾམཛྫཡིཥྱཏི།
Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
12 ཏསྱ ཀཱརེ སཱུརྤ ཨཱསྟེ, ས སྭཱིཡཤསྱཱནི སམྱཀ྄ པྲསྥོཊྱ ནིཛཱན྄ སཀལགོདྷཱུམཱན྄ སཾགྲྀཧྱ བྷཱཎྜཱགཱརེ སྠཱཔཡིཥྱཏི, ཀིཾནྟུ སཪྻྭཱཎི ཝུཥཱཎྱནིཪྻྭཱཎཝཧྣིནཱ དཱཧཡིཥྱཏི།
Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba.”
13 ཨནནྟརཾ ཡཱིཤུ ཪྻོཧནཱ མཛྫིཏོ བྷཝིཏུཾ གཱལཱིལྤྲདེཤཱད྄ ཡརྡྡནི ཏསྱ སམཱིཔམ྄ ཨཱཛགཱམ།
Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma.
14 ཀིནྟུ ཡོཧན྄ ཏཾ ནིཥིདྷྱ བབྷཱཥེ, ཏྭཾ ཀིཾ མམ སམཱིཔམ྄ ཨཱགཙྪསི? ཝརཾ ཏྭཡཱ མཛྫནཾ མམ པྲཡོཛནམ྄ ཨཱསྟེ།
Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, “Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?”
15 ཏདཱནཱིཾ ཡཱིཤུཿ པྲཏྱཝོཙཏ྄; ཨཱིདཱནཱིམ྄ ཨནུམནྱསྭ, ཡཏ ཨིཏྠཾ སཪྻྭདྷརྨྨསཱདྷནམ྄ ཨསྨཱཀཾ ཀརྟྟཝྱཾ, ཏཏཿ སོ྅ནྭམནྱཏ།
Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci.” Sai Yahaya ya yarje masa.
16 ཨནནྟརཾ ཡཱིཤུརམྨསི མཛྫིཏུཿ སན྄ ཏཏྐྵཎཱཏ྄ ཏོཡམདྷྱཱད྄ ཨུཏྠཱཡ ཛགཱམ, ཏདཱ ཛཱིམཱུཏདྭཱརེ མུཀྟེ ཛཱཏེ, ས ཨཱིཤྭརསྱཱཏྨཱནཾ ཀཔོཏཝད྄ ཨཝརུཧྱ སྭོཔཪྻྱཱགཙྪནྟཾ ཝཱིཀྵཱཉྩཀྲེ།
Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa.
17 ཨཔརམ྄ ཨེཥ མམ པྲིཡཿ པུཏྲ ཨེཏསྨིནྣེཝ མམ མཧཱསནྟོཥ ཨེཏཱདྲྀཤཱི ཝྱོམཛཱ ཝཱག྄ བབྷཱུཝ།
Duba, wata murya daga sammai tana cewa, ''Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai.''

< མཐིཿ 3 >