< ཡོཧནཿ 19 >

1 པཱིལཱཏོ ཡཱིཤུམ྄ ཨཱནཱིཡ ཀཤཡཱ པྲཱཧཱརཡཏ྄།
Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala.
2 པཤྩཱཏ྄ སེནཱགཎཿ ཀཎྚཀནིརྨྨིཏཾ མུཀུཊཾ ཏསྱ མསྟཀེ སམརྤྱ ཝཱརྟྟཱཀཱིཝརྞཾ རཱཛཔརིཙྪདཾ པརིདྷཱཔྱ,
Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata.
3 ཧེ ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ རཱཛན྄ ནམསྐཱར ཨིཏྱུཀྟྭཱ ཏཾ ཙཔེཊེནཱཧནྟུམ྄ ཨཱརབྷཏ།
Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
4 ཏདཱ པཱིལཱཏཿ པུནརཔི བཧིརྒཏྭཱ ལོཀཱན྄ ཨཝདཏ྄, ཨསྱ ཀམཔྱཔརཱདྷཾ ན ལབྷེ྅ཧཾ, པཤྱཏ ཏད྄ ཡུཥྨཱན྄ ཛྙཱཔཡིཏུཾ ཡུཥྨཱཀཾ སནྣིདྷཽ བཧིརེནམ྄ ཨཱནཡཱམི།
Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”,
5 ཏཏཿ པརཾ ཡཱིཤུཿ ཀཎྚཀམུཀུཊཝཱན྄ ཝཱརྟྟཱཀཱིཝརྞཝསནཝཱཾཤྩ བཧིརཱགཙྪཏ྄། ཏཏཿ པཱིལཱཏ ཨུཀྟཝཱན྄ ཨེནཾ མནུཥྱཾ པཤྱཏ།
Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace “Ga mutumin nan”.
6 ཏདཱ པྲདྷཱནཡཱཛཀཱཿ པདཱཏཡཤྩ ཏཾ དྲྀཥྚྭཱ, ཨེནཾ ཀྲུཤེ ཝིདྷ, ཨེནཾ ཀྲུཤེ ཝིདྷ, ཨིཏྱུཀྟྭཱ རཝིཏུཾ ཨཱརབྷནྟ། ཏཏཿ པཱིལཱཏཿ ཀཐིཏཝཱན྄ ཡཱུཡཾ སྭཡམ྄ ཨེནཾ ནཱིཏྭཱ ཀྲུཤེ ཝིདྷཏ, ཨཧམ྄ ཨེཏསྱ ཀམཔྱཔརཱདྷཾ ན པྲཱཔྟཝཱན྄།
Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa “A gicciye shi, A gicciye shi” Sai Bilatus yace masu, “ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba”.
7 ཡིཧཱུདཱིཡཱཿ པྲཏྱཝདན྄ ཨསྨཱཀཾ ཡཱ ཝྱཝསྠཱསྟེ ཏདནུསཱརེཎཱསྱ པྲཱཎཧནནམ྄ ཨུཙིཏཾ ཡཏོཡཾ སྭམ྄ ཨཱིཤྭརསྱ པུཏྲམཝདཏ྄།
Sai Yahudawan sukace mashi, “Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah”.
8 པཱིལཱཏ ཨིམཱཾ ཀཐཱཾ ཤྲུཏྭཱ མཧཱཏྲཱསཡུཀྟཿ
Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai.
9 སན྄ པུནརཔི རཱཛགྲྀཧ ཨཱགཏྱ ཡཱིཤུཾ པྲྀཥྚཝཱན྄ ཏྭཾ ཀུཏྲཏྱོ ལོཀཿ? ཀིནྟུ ཡཱིཤསྟསྱ ཀིམཔི པྲཏྱུཏྟརཾ ནཱཝདཏ྄།
Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, “Daga ina ka fito?” amma Yesu bai amsa mashi ba.
10 ༡ ཏཏཿ པཱིལཱཏ྄ ཀཐིཏཝཱན ཏྭཾ ཀིཾ མཡཱ སཱརྡྡྷཾ ན སཾལཔིཥྱསི? ཏྭཱཾ ཀྲུཤེ ཝེདྷིཏུཾ ཝཱ མོཙཡིཏུཾ ཤཀྟི རྨམཱསྟེ ཨིཏི ཀིཾ ཏྭཾ ན ཛཱནཱསི? ཏདཱ ཡཱིཤུཿ པྲཏྱཝདད྄ ཨཱིཤྭརེཎཱདཾ མམོཔརི ཏཝ ཀིམཔྱདྷིཔཏིཏྭཾ ན ཝིདྱཏེ, ཏཐཱཔི ཡོ ཛནོ མཱཾ ཏཝ ཧསྟེ སམཱརྤཡཏ྄ ཏསྱ མཧཱཔཱཏཀཾ ཛཱཏམ྄།
Sai Bilatus yace masa “Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka?
11 ཏདཱ ཡཱིཤུཿ པྲཏྱཝདད྄ ཨཱིཤྭརེཎཱདཏྟཾ མམོཔརི ཏཝ ཀིམཔྱདྷིཔཏིཏྭཾ ན ཝིདྱཏེ, ཏཐཱཔི ཡོ ཛནོ མཱཾ ཏཝ ཧསྟེ སམཱརྤཡཏ྄ ཏསྱ མཧཱཔཱཏཀཾ ཛཱཏམ྄།
Yesu ya amsa masa, “Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi”.
12 ཏདཱརབྷྱ པཱིལཱཏསྟཾ མོཙཡིཏུཾ ཙེཥྚིཏཝཱན྄ ཀིནྟུ ཡིཧཱུདཱིཡཱ རུཝནྟོ ཝྱཱཧརན྄ ཡདཱིམཾ མཱནཝཾ ཏྱཛསི ཏརྷི ཏྭཾ ཀཻསརསྱ མིཏྲཾ ན བྷཝསི, ཡོ ཛནཿ སྭཾ རཱཛཱནཾ ཝཀྟི སཨེཝ ཀཻམརསྱ ཝིརུདྡྷཱཾ ཀཐཱཾ ཀཐཡཏི།
Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, “In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar”.
13 ཨེཏཱཾ ཀཐཱཾ ཤྲུཏྭཱ པཱིལཱཏོ ཡཱིཤུཾ བཧིརཱནཱིཡ ནིསྟཱརོཏྶཝསྱ ཨཱསཱདནདིནསྱ དྭིཏཱིཡཔྲཧརཱཏ྄ པཱུཪྻྭཾ པྲསྟརབནྡྷནནཱམྣི སྠཱནེ ྅རྠཱཏ྄ ཨིབྲཱིཡབྷཱཥཡཱ ཡད྄ གབྦིཐཱ ཀཐྱཏེ ཏསྨིན྄ སྠཱནེ ཝིཙཱརཱསན ཨུཔཱཝིཤཏ྄།
Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira “Dakalin shari'a,” a Yahudanci kuma, “Gabbata.”
14 ཨནནྟརཾ པཱིལཱཏོ ཡིཧཱུདཱིཡཱན྄ ཨཝདཏ྄, ཡུཥྨཱཀཾ རཱཛཱནཾ པཤྱཏ།
To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan “Ga sarkin ku!”
15 ཀིནྟུ ཨེནཾ དཱུརཱིཀུརུ, ཨེནཾ དཱུརཱིཀུརུ, ཨེནཾ ཀྲུཤེ ཝིདྷ, ཨིཏི ཀཐཱཾ ཀཐཡིཏྭཱ ཏེ རཝིཏུམ྄ ཨཱརབྷནྟ; ཏདཱ པཱིལཱཏཿ ཀཐིཏཝཱན྄ ཡུཥྨཱཀཾ རཱཛཱནཾ ཀིཾ ཀྲུཤེ ཝེདྷིཥྱཱམི? པྲདྷཱནཡཱཛཀཱ ཨུཏྟརམ྄ ཨཝདན྄ ཀཻསརཾ ཝིནཱ ཀོཔི རཱཛཱསྨཱཀཾ ནཱསྟི།
Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu “In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace “Ba mu da wani sarki sai Kaisar”.
16 ཏཏཿ པཱིལཱཏོ ཡཱིཤུཾ ཀྲུཤེ ཝེདྷིཏུཾ ཏེཥཱཾ ཧསྟེཥུ སམཱརྤཡཏ྄, ཏཏསྟེ ཏཾ དྷྲྀཏྭཱ ནཱིཏཝནྟཿ།
Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi.
17 ཏཏཿ པརཾ ཡཱིཤུཿ ཀྲུཤཾ ཝཧན྄ ཤིརཿཀཔཱལམ྄ ཨརྠཱད྄ ཡད྄ ཨིབྲཱིཡབྷཱཥཡཱ གུལྒལྟཱཾ ཝདནྟི ཏསྨིན྄ སྠཱན ཨུཔསྠིཏཿ།
Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira “Wurin kwalluwa” da Yahudanci kuma “Golgota”.
18 ཏཏསྟེ མདྷྱསྠཱནེ ཏཾ ཏསྱོབྷཡཔཱརྴྭེ དྭཱཝཔརཽ ཀྲུཤེ྅ཝིདྷན྄།
Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya.
19 ཨཔརམ྄ ཨེཥ ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ རཱཛཱ ནཱསརཏཱིཡཡཱིཤུཿ, ཨིཏི ཝིཛྙཱཔནཾ ལིཁིཏྭཱ པཱིལཱཏསྟསྱ ཀྲུཤོཔརི སམཡོཛཡཏ྄།
Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA”.
20 སཱ ལིཔིཿ ཨིབྲཱིཡཡཱུནཱནཱིཡརོམཱིཡབྷཱཥཱབྷི རླིཁིཏཱ; ཡཱིཤོཿ ཀྲུཤཝེདྷནསྠཱནཾ ནགརསྱ སམཱིཔཾ, ཏསྨཱད྄ བཧཝོ ཡིཧཱུདཱིཡཱསྟཱཾ པཋིཏུམ྄ ཨཱརབྷནྟ།
Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci.
21 ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ པྲདྷཱནཡཱཛཀཱཿ པཱིལཱཏམིཏི ནྱཝེདཡན྄ ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ རཱཛེཏི ཝཱཀྱཾ ན ཀིནྟུ ཨེཥ སྭཾ ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ རཱཛཱནམ྄ ཨཝདད྄ ཨིཏྠཾ ལིཁཏུ།
Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace “Ni ne sarkin Yahudawa”'.
22 ཏཏཿ པཱིལཱཏ ཨུཏྟརཾ དཏྟཝཱན྄ ཡལླེཁནཱིཡཾ ཏལླིཁིཏཝཱན྄།
Bilatus kuwa ya amsa, “Abinda na rubuta na rubuta kenan.”
23 ཨིཏྠཾ སེནཱགཎོ ཡཱིཤུཾ ཀྲུཤེ ཝིདྷིཏྭཱ ཏསྱ པརིདྷེཡཝསྟྲཾ ཙཏུརོ བྷཱགཱན྄ ཀྲྀཏྭཱ ཨེཀཻཀསེནཱ ཨེཀཻཀབྷཱགམ྄ ཨགྲྀཧླཏ྄ ཏསྱོཏྟརཱིཡཝསྟྲཉྩཱགྲྀཧླཏ྄། ཀིནྟཱུཏྟརཱིཡཝསྟྲཾ སཱུཙིསེཝནཾ ཝིནཱ སཪྻྭམ྄ ཨཱུཏཾ།
Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa.
24 ཏསྨཱཏྟེ ཝྱཱཧརན྄ ཨེཏཏ྄ ཀཿ པྲཱཔྶྱཏི? ཏནྣ ཁཎྜཡིཏྭཱ ཏཏྲ གུཊིཀཱཔཱཏཾ ཀརཝཱམ། ཝིབྷཛནྟེ྅དྷརཱིཡཾ མེ ཝསནཾ ཏེ པརསྤརཾ། མམོཏྟརཱིཡཝསྟྲཱརྠཾ གུཊིཀཱཾ པཱཏཡནྟི ཙ། ཨིཏི ཡདྭཱཀྱཾ དྷརྨྨཔུསྟཀེ ལིཁིཏམཱསྟེ ཏཏ྄ སེནཱགཎེནེཏྠཾ ཝྱཝཧརཎཱཏ྄ སིདྡྷམབྷཝཏ྄།
Sai sukace wa junansu, “Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa “Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata.
25 ཏདཱནཱིཾ ཡཱིཤོ རྨཱཏཱ མཱཏུ རྦྷགིནཱི ཙ ཡཱ ཀླིཡཔཱ བྷཱཪྻྱཱ མརིཡམ྄ མགྡལཱིནཱི མརིཡམ྄ ཙ ཨེཏཱསྟསྱ ཀྲུཤསྱ སནྣིདྷཽ སམཏིཥྛན྄།
Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu.
26 ཏཏོ ཡཱིཤུཿ སྭམཱཏརཾ པྲིཡཏམཤིཥྱཉྩ སམཱིཔེ དཎྜཱཡམཱནཽ ཝིལོཀྱ མཱཏརམ྄ ཨཝདཏ྄, ཧེ ཡོཥིད྄ ཨེནཾ ཏཝ པུཏྲཾ པཤྱ,
Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, “Mace, dubi, dan ki!”
27 ཤིཥྱནྟྭཝདཏ྄, ཨེནཱཾ ཏཝ མཱཏརཾ པཤྱ། ཏཏཿ ས ཤིཥྱསྟདྒྷཊིཀཱཡཱཾ ཏཱཾ ནིཛགྲྀཧཾ ནཱིཏཝཱན྄།
Sai yace wa almajirin, “Dubi, mahaifiyarka!” Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa.
28 ཨནནྟརཾ སཪྻྭཾ ཀརྨྨཱདྷུནཱ སམྤནྣམབྷཱུཏ྄ ཡཱིཤུརིཏི ཛྙཱཏྭཱ དྷརྨྨཔུསྟཀསྱ ཝཙནཾ ཡཐཱ སིདྡྷཾ བྷཝཏི ཏདརྠམ྄ ཨཀཐཡཏ྄ མམ པིཔཱསཱ ཛཱཏཱ།
Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace “Ina jin kishi.
29 ཏཏསྟསྨིན྄ སྠཱནེ ཨམླརསེན པཱུརྞཔཱཏྲསྠིཏྱཱ ཏེ སྤཉྫམེཀཾ ཏདམླརསེནཱརྡྲཱིཀྲྀཏྱ ཨེསོབྣལེ ཏད྄ ཡོཛཡིཏྭཱ ཏསྱ མུཁསྱ སནྣིདྷཱཝསྠཱཔཡན྄།
A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki.
30 ཏདཱ ཡཱིཤུརམླརསཾ གྲྀཧཱིཏྭཱ སཪྻྭཾ སིདྡྷམ྄ ཨིཏི ཀཐཱཾ ཀཐཡིཏྭཱ མསྟཀཾ ནམཡན྄ པྲཱཎཱན྄ པཪྻྱཏྱཛཏ྄།
Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace “An gama” Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa.
31 ཏདྭིནམ྄ ཨཱསཱདནདིནཾ ཏསྨཱཏ྄ པརེ྅ཧནི ཝིཤྲཱམཝཱརེ དེཧཱ ཡཐཱ ཀྲུཤོཔརི ན ཏིཥྛནྟི, ཡཏཿ ས ཝིཤྲཱམཝཱརོ མཧཱདིནམཱསཱིཏ྄, ཏསྨཱད྄ ཡིཧཱུདཱིཡཱཿ པཱིལཱཏནིཀཊཾ གཏྭཱ ཏེཥཱཾ པཱདབྷཉྫནསྱ སྠཱནཱནྟརནཡནསྱ ཙཱནུམཏིཾ པྲཱརྠཡནྟ།
Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su.
32 ཨཏཿ སེནཱ ཨཱགཏྱ ཡཱིཤུནཱ སཧ ཀྲུཤེ ཧཏཡོཿ པྲཐམདྭིཏཱིཡཙོརཡོཿ པཱདཱན྄ ཨབྷཉྫན྄;
Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu.
33 ཀིནྟུ ཡཱིཤོཿ སནྣིདྷིཾ གཏྭཱ ས མྲྀཏ ཨིཏི དྲྀཥྚྭཱ ཏསྱ པཱདཽ ནཱབྷཉྫན྄།
Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba.
34 པཤྩཱད྄ ཨེཀོ ཡོདྡྷཱ ཤཱུལཱགྷཱཏེན ཏསྱ ཀུཀྵིམ྄ ཨཝིདྷཏ྄ ཏཏྐྵཎཱཏ྄ ཏསྨཱད྄ རཀྟཾ ཛལཉྩ ནིརགཙྪཏ྄།
Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito.
35 ཡོ ཛནོ྅སྱ སཱཀྵྱཾ དདཱཏི ས སྭཡཾ དྲྀཥྚཝཱན྄ ཏསྱེདཾ སཱཀྵྱཾ སཏྱཾ ཏསྱ ཀཐཱ ཡུཥྨཱཀཾ ཝིཤྭཱསཾ ཛནཡིཏུཾ ཡོགྱཱ ཏཏ྄ ས ཛཱནཱཏི།
Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata.
36 ཏསྱཻཀམ྄ ཨསྡྷྱཔི ན བྷཾཀྵྱཏེ,
Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, “Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya”.
37 ཏདྭད྄ ཨནྱཤཱསྟྲེཔི ལིཁྱཏེ, ཡཐཱ, "དྲྀཥྚིཔཱཏཾ ཀརིཥྱནྟི ཏེ྅ཝིདྷན྄ ཡནྟུ ཏམྤྲཏི། "
Kuma wani nassin yace, “Zasu dube shi wanda suka soka.”
38 ཨརིམཐཱིཡནགརསྱ ཡཱུཥཕྣཱམཱ ཤིཥྱ ཨེཀ ཨཱསཱིཏ྄ ཀིནྟུ ཡིཧཱུདཱིཡེབྷྱོ བྷཡཱཏ྄ པྲཀཱཤིཏོ ན བྷཝཏི; ས ཡཱིཤོ རྡེཧཾ ནེཏུཾ པཱིལཱཏསྱཱནུམཏིཾ པྲཱརྠཡཏ, ཏཏཿ པཱིལཱཏེནཱནུམཏེ སཏི ས གཏྭཱ ཡཱིཤོ རྡེཧམ྄ ཨནཡཏ྄།
Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin.
39 ཨཔརཾ ཡོ ནིཀདཱིམོ རཱཏྲཽ ཡཱིཤོཿ སམཱིཔམ྄ ཨགཙྪཏ྄ སོཔི གནྡྷརསེན མིཤྲིཏཾ པྲཱཡེཎ པཉྩཱཤཏྶེཊཀམགུརུཾ གྲྀཧཱིཏྭཱགཙྪཏ྄།
Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari.
40 ཏཏསྟེ ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱཾ ཤྨཤཱནེ སྠཱཔནརཱིཏྱནུསཱརེཎ ཏཏྶུགནྡྷིདྲཝྱེཎ སཧིཏཾ ཏསྱ དེཧཾ ཝསྟྲེཎཱཝེཥྚཡན྄།
Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa.
41 ཨཔརཉྩ ཡཏྲ སྠཱནེ ཏཾ ཀྲུཤེ྅ཝིདྷན྄ ཏསྱ ནིཀཊསྠོདྱཱནེ ཡཏྲ ཀིམཔི མྲྀཏདེཧཾ ཀདཱཔི ནཱསྠཱཔྱཏ ཏཱདྲྀཤམ྄ ཨེཀཾ ནཱུཏནཾ ཤྨཤཱནམ྄ ཨཱསཱིཏ྄།
To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba.
42 ཡིཧཱུདཱིཡཱནཱམ྄ ཨཱསཱདནདིནཱགམནཱཏ྄ ཏེ ཏསྨིན྄ སམཱིཔསྠཤྨཤཱནེ ཡཱིཤུམ྄ ཨཤཱཡཡན྄།
Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.

< ཡོཧནཿ 19 >