< К Римлянам 15 >
1 Мы, сильные, должны сносить немощи бессильных и не себе угождать.
Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba.
2 Каждый из нас должен угождать ближнему, во благо, к назиданию.
Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi.
3 Ибо и Христос не Себе угождал, но, как написано: злословия злословящих Тебя пали на Меня.
Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, “zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina.”
4 А все, что писано было прежде, написано нам в наставление, чтобы мы терпением и утешением из Писаний сохраняли надежду.
Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi.
5 Бог же терпения и утешения да дарует вам быть в единомыслии между собою, по учению Христа Иисуса,
Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu.
6 дабы вы единодушно, едиными устами славили Бога и Отца Господа нашего Иисуса Христа.
Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya.
7 Посему принимайте друг друга, как и Христос принял вас в славу Божию.
Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
8 Разумею то, что Иисус Христос сделался служителем для обрезанных - ради истины Божией, чтобы исполнить обещанное отцам,
Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
9 а для язычников - из милости, чтобы славили Бога, как написано: за то буду славить Тебя Господи между язычниками, и буду петь имени Твоему.
Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.”
10 И еще сказано: возвеселитесь, язычники, с народом Его.
Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.”
11 И еще: хвалите Господа, все язычники, и прославляйте Его, все народы.
Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.”
12 Исаия также говорит: будет корень Иессеев, и восстанет владеть народами; на Него язычники надеяться будут.
Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.”
13 Бог же надежды да исполнит вас всякой радости и мира в вере, дабы вы, силою Духа Святаго, обогатились надеждою.
Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14 И сам я уверен о вас, братия мои, что и вы полны благости, исполнены всякого познания и можете наставлять друг друга;
Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna.
15 но писал вам, братия, с некоторою смелостью, отчасти как бы в напоминание вам, по данной мне от Бога благодати
Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah.
16 быть служителем Иисуса Христа у язычников и совершать священнодействие благовествования Божия, дабы сие приношение язычников, будучи освящено Духом Святым, было благоприятно Богу.
Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
17 Итак я могу похвалиться в Иисусе Христе в том, что относится к Богу,
Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah.
18 ибо не осмелюсь сказать что-нибудь такое, чего не совершил Христос через меня, в покорении язычников вере, словом и делом,
Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki.
19 силою знамений и чудес, силою Духа Божия, так что благовествование Христово распространено мною от Иерусалима и окрестности до Иллирика.
Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka.
20 Притом я старался благовествовать не там, где уже было известно имя Христово, дабы не созидать на чужом основании,
A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani.
21 но как написано: не имевшие о Нем известия увидят, и не слышавшие узнают.
Kamar yadda yake a rubuce.”Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta.”
22 Сие-то много раз и препятствовало мне придти к вам.
Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama.
23 Ныне же, не имея такого места в сих странах, а с давних лет имея желание придти к вам,
Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku.
24 как только предприму путь в Испанию, приду к вам. Ибо надеюсь, что, проходя, увижусь с вами и что вы проводите меня туда, как скоро наслажусь общением с вами, хотя отчасти.
Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci.
25 А теперь я иду в Иерусалим, чтобы послужить святым,
Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima.
26 ибо Македония и Ахаия усердствуют некоторым подаянием для бедных между святыми в Иерусалиме.
Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima.
27 Усердствуют, да и должники они перед ними. Ибо если язычники сделались участниками в их духовном, то должны и им послужить в телесном.
Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa.
28 Исполнив это и верно доставив им сей плод усердия, я отправлюсь через ваши места в Испанию,
Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya.
29 и уверен, что когда приду к вам, то приду с полным благословением благовествования Христова.
Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu.
30 Между тем умоляю вас, братия, Господом нашим Иисусом Христом и любовью Духа, подвизаться со мною в молитвах за меня к Богу,
Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni.
31 чтобы избавиться мне от неверующих в Иудее и чтобы служение мое для Иерусалима было благоприятно святым,
Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya.
32 дабы мне в радости, если Богу угодно, придти к вам и успокоиться с вами.
Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu.
33 Бог же мира да будет со всеми вами, аминь.
Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.