< К Римлянам 11 >

1 Итак спрашиваю: неужели Бог отверг народ Свой? Никак. Ибо и я Израильтянин, от семени Авраамова, из колена Вениаминова.
Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu.
2 Не отверг Бог народа Своего, который Он наперед знал. Или не знаете, что говорит Писание в повествовании об Илии? Как он жалуется Богу на Израиля, говоря:
Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah?
3 Господи! пророков Твоих убили, жертвенники Твои разрушили; остался я один, и моей души ищут.
Ya ce, ''Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni.''
4 Что же говорит ему Божеский ответ? Я соблюл Себе семь тысяч человек, которые не преклонили колени перед Ваалом.
Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, ''Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba.''
5 Так и в нынешнее время, по избранию благодати, сохранился остаток.
Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri.
6 Но если по благодати, то не по делам; иначе благодать не была бы уже благодатью. А если по делам, то это уже не благодать; иначе дело не есть уже дело.
Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan.
7 Что же? Израиль, чего искал, того не получил; избранные же получили, а прочие ожесточились,
Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare.
8 как написано: Бог дал им дух усыпления, глаза, которыми не видят, и уши, которыми не слышат, даже до сего дня.
Kamar yadda yake a rubuce, ''Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana.''
9 И Давид говорит: да будет трапеза их сетью, тенетами и петлею в возмездие им;
Dauda kuma ya ce, ''bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su.
10 да помрачатся глаза их, чтобы не видеть, и хребет их да будет согбен навсегда.
Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum.''
11 Итак спрашиваю: неужели они преткнулись, чтобы совсем пасть? Никак. Но от их падения спасение язычникам, чтобы возбудить в них ревность.
Na ce, ''sun yi tuntube domin su fadi ne?'' Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi.
12 Если же падение их - богатство миру, и оскудение их - богатство язычникам, то тем более полнота их.
Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala?
13 Вам говорю, язычникам. Как Апостол язычников, я прославляю служение мое.
Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata.
14 Не возбужу ли ревность в сродниках моих по плоти и не спасу ли некоторых из них?
Yana yiwuwa in sa ''yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su.
15 Ибо если отвержение их - примирение мира, то что будет принятие, как не жизнь из мертвых?
Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa.
16 Если начаток свят, то и целое; и если корень свят, то и ветви.
'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama.
17 Если же некоторые из ветвей отломились, а ты, дикая маслина, привился на место их и стал общником корня и сока маслины,
Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din.
18 то не превозносись перед ветвями. Если же превозносишься, то вспомни, что не ты корень держишь, но корень тебя.
Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku.
19 Скажешь: “Ветви отломились, чтобы мне привиться”
Kana iya cewa, ''An karye rassan domin a same ni a ciki.''
20 Хорошо. Они отломились неверием, а ты держишься верою: не гордись, но бойся.
Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro.
21 Ибо если Бог не пощадил природных ветвей, то смотри, пощадит ли и тебя.
Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba.
22 Итак, видишь благость и строгость Божию: строгость к отпадшим, а благость к тебе, если пребудешь в благости Божией; иначе и ты будешь отсечен.
Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku.
23 Но и те, если не пребудут в неверии, привьются, потому что Бог силен опять привить их.
Hakanan, idan ba su ci gaba cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a maida su cikin itacen. Domin Allah zai iya sake maida su.
24 Ибо если ты отсечен от дикой по природе маслины и не по природе привился к хорошей маслине, то тем более сии природные привьются к своей маслине.
Idan an yanke ka daga itacen zaitun da ke na jeji, har ya yiwu an hada ka cikin itacen zaitun na ainihi, yaya kuma wadannan Yahudawa wadanda sune ainihin rassan, da za'a maido cikin zaitun da ke na ainihi?
25 Ибо не хочу оставить вас, братия, в неведении о тайне сей, - чтобы вы не мечтали о себе, что ожесточение произошло в Израиле отчасти, до времени, пока войдет полное число язычников;
Yan'uwa, ba na so ku kasance cikin duhu a game da wannan asirin, domin kada ku zama da hikima cikin tunaninku. Wannan asirin shine cewa wannan taurarewa ta faru a Isra'ila, har sai da Al'ummai suka shigo ciki.
26 и так весь Израиль спасется, как написано: придет от Сиона Избавитель, и отвратит нечестие от Иакова.
Ta haka dukan Isra'ila za su tsira, kamar yadda yake a rubuce: ''Daga cikin Sihiyona mai Kubutarwa zai fito; Zai kawar da kazanta daga cikin Yakubu.
27 И сей завет им от Меня, когда сниму с них грехи их.
Wannan zai zama alkawarina da su, sa'adda na kawar da zunubansu.''
28 В отношении к благовестию они враги ради вас; а в отношении к избранию - возлюбленные Божии ради отцов.
A wani bangaren kuma game da bishara, su makiya ne amamadinku, ta wani fannin kuma bisa ga zabin Allah su kaunattatu ne saboda ubanni.
29 Ибо дары и призвание Божие непреложны.
Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa.
30 Как и вы некогда были непослушны Богу, а ныне помилованы, по непослушанию их,
Domin ku ma da ba ku yin biyayya ga Allah, amma yanzu kun sami jinkai saboda rashin biyayyarsu.
31 так и они теперь непослушны для помилования вас, чтобы и сами они были помилованы.
Ta wannan hanyar dai, wadannan Yahudawan sun zama marasa biyayya. Sakamakon haka shine ta wurin jinkan da aka nuna maku, suma su samu jikai yanzu.
32 Ибо всех заключил Бог в непослушание, чтобы всех помиловать. (eleēsē g1653)
Domin Allah ya rufe kowa ga rashin biyayya, domin ya nuna jinkai ga kowa. (eleēsē g1653)
33 О, бездна богатства и премудрости и ведения Божия! Как непостижимы судьбы Его и неисследимы пути Его!
Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa!
34 Ибо кто познал ум Господень? Или кто был советником Ему?
Don wanene ya san tunanin Ubangiji? Wanene kuma ya zama mai bashi shawara?
35 Или кто дал Ему наперед, чтобы Он должен был воздать?
Ko kuma, wanene ya fara ba Allah wani abu, domin a biya shi?''
36 Ибо все из Него, Им и к Нему. Ему слава во веки, аминь. (aiōn g165)
Daga wurinsa ne, ta wurinsa ne kuma, a gare shi ne kuma dukan abu suka fito. A gare shi daukaka ta tabbata har abada. Amin. (aiōn g165)

< К Римлянам 11 >