< От Матфея 8 >

1 Когда же сошел Он с горы, за Ним последовало множество народа.
Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi.
2 И вот подошел прокаженный и, кланяясь Ему, сказал: Господи! если хочешь, можешь меня очистить.
Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
3 Иисус, простерши руку, коснулся его и сказал: хочу, очистись. И он тотчас очистился от проказы.
Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa.
4 И говорит ему Иисус: смотри, никому не сказывай, но пойди, покажи себя священнику и принеси дар, какой повелел Моисей, во свидетельство им.
Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu?
5 Когда же вошел Иисус в Капернаум, к Нему подошел сотник и просил Его:
Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi,
6 Господи! слуга мой лежит дома в расслаблении и жестоко страдает.
Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.”
7 Иисус говорит ему: Я приду и исцелю его.
Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”
8 Сотник же, отвечая, сказал: Господи! я недостоин, чтобы Ты вошел под кров мой, но скажи только слово, и выздоровеет слуга мой;
Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke.
9 ибо я и подвластный человек, но, имея у себя в подчинении воинов, говорю одному: пойди, и идет; и другому: приди, и приходит; и слуге моему: сделай то, и делает.
Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,”
10 Услышав сие, Иисус удивился и сказал идущим за Ним: истинно говорю вам, и в Израиле не нашел Я такой веры.
Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba.
11 Говорю же вам, что многие придут с востока и запада и возлягут с Авраамом, Исааком и Иаковом в Царстве Небесном;
Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama.
12 а сыны царства извержены будут во тьму внешнюю: там будет плач и скрежет зубов.
Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.”
13 И сказал Иисус сотнику: иди, и, как ты веровал, да будет тебе. И выздоровел слуга его в тот час.
Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke.
14 Придя в дом Петров, Иисус увидел тещу его, лежащую в горячке,
Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi.
15 и коснулся руки ее, и горячка оставила ее; и она встала и служила им.
Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima.
16 Когда же настал вечер, к Нему привели многих бесноватых, и Он изгнал духов словом и исцелил всех больных,
Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
17 да сбудется реченное через пророка Исаию, который говорит: Он взял на Себя наши немощи и понес болезни.
Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.”
18 Увидев же Иисус вокруг Себя множество народа, велел ученикам отплыть на другую сторону.
Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili.
19 Тогда один книжник, подойдя, сказал Ему: Учитель! я пойду за Тобою, куда бы Ты ни пошел.
Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
20 И говорит ему Иисус: лисицы имеют норы и птицы небесные - гнезда, а Сын Человеческий не имеет, где приклонить голову.
Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.”
21 Другой же из учеников Его сказал Ему: Господи! позволь мне прежде пойти и похоронить отца моего.
Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.”
22 Но Иисус сказал ему: иди за Мною и предоставь мертвым погребать своих мертвецов.
Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.”
23 И когда вошел Он в лодку, за Ним последовали ученики Его.
Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.
24 И вот, сделалось великое волнение на море, так что лодка покрывалась волнами; а Он спал.
Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
25 Тогда ученики Его, подойдя к Нему, разбудили Его и сказали: Господи! спаси нас, погибаем.
Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”
26 И говорит им: что вы так боязливы, маловерные? потом, встав, запретил ветрам и морю, и сделалась великая тишина.
Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit.
27 Люди же, удивляясь, говорили: Кто это, что и ветры и море повинуются Ему?
Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”.
28 И когда Он прибыл на другой берег в страну Гергесинскую, Его встретили два бесноватые, вышедшие из гробов, весьма свирепые, так что никто не смел проходить тем путем.
Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya.
29 И вот, они закричали: что Тебе до нас, Иисус, Сын Божий? пришел Ты сюда прежде времени мучить нас.
Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
30 Вдали же от них паслось большое стадо свиней.
To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su.
31 И бесы просили Его: если выгонишь нас, то пошли нас в стадо свиней.
Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
32 И Он сказал им: идите. И они, выйдя, пошли в стадо свиное. И вот, все стадо свиней бросилось с крутизны в море и погибло в воде.
“Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa.
33 Пастухи же побежали и, придя в город, рассказали обо всем и о том, что было с бесноватыми.
Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun.
34 И вот, весь город вышел навстречу Иисусу; и, увидев Его, просили, чтобы Он отошел от пределов их.
Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.

< От Матфея 8 >