< Книга Судей 8 >
1 И сказали ему Ефремляне: зачем ты это сделал, что не позвал нас, когда шел воевать с Мадианитянами? И сильно ссорились с ним.
To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.
2 Гедеон отвечал им: сделал ли я что такое, как вы ныне? Не счастливее ли Ефрем добирал виноград, нежели Авиезер обирал?
Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?
3 В ваши руки предал Бог князей Мадиамских Орива и Зива, и что мог сделать я такое, как вы? Тогда успокоился дух их против него, когда сказал он им такие слова.
Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”
4 И пришел Гедеон к Иордану, и перешел сам и триста человек, бывшие с ним. Они были утомлены и голодны, преследуя врагов.
Gideyon da mutanensa ɗari uku, sun gaji, duk da haka suka yi ta fafarar, suka zo Urdun suka haye shi.
5 И сказал он жителям Сокхофа: дайте хлеба народу, который идет за мною; они утомились, а я преследую Зевея и Салмана, царей Мадиамских.
Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”
6 Князья Сокхофа сказали: разве рука Зевея и Салмана уже в твоей руке, чтобы нам войску твоему давать хлеб?
Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?”
7 И сказал Гедеон: за это, когда предаст Господь Зевея и Салмана в руки мои, я растерзаю тело ваше терновником пустынным и молотильными зубчатыми досками.
Sai Gideyon ya ce, “Haka ko? To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayyuwan jeji.”
8 Оттуда пошел он в Пенуэл и то же сказал жителям его, и жители Пенуэла отвечали ему то же, что отвечали жители Сокхофа.
Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi.
9 Он сказал и жителям Пенуэла: когда я возвращусь в мире, разрушу башню сию.
Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.”
10 Зевей же и Салман были в Каркоре и с ними их ополчение до пятнадцати тысяч, все, что осталось из всего ополчения жителей востока; пало же сто двадцать тысяч человек, обнажающих меч.
To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu.
11 Гедеон пошел к живущим в шатрах на восток от Новы и Иогбеги и поразил стан, когда стан стоял беспечно.
Gideyon ya haura ta hanyar makiyaya, gabas da Noba, da kuma Yogbeha, ya fāɗa wa mayaƙan ta yadda ba su zata ba.
12 Зевей и Салман побежали; он погнался за ними и схватил обоих царей Мадиамских, Зевея и Салмана, и весь стан привел в замешательство.
Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu.
13 И возвратился Гедеон, сын Иоаса, с войны от возвышенности Хереса.
Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres.
14 И захватил юношу из жителей Сокхофа и выспросил у него; и он написал ему князей и старейшин Сокхофских семьдесят семь человек.
Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin.
15 И пришел он к жителям Сокхофским, и сказал: вот Зевей и Салман, за которых вы посмеялись надо мною, говоря: разве рука Зевея и Салмана уже в твоей руке, чтобы нам давать хлеб утомившимся людям твоим?
Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’”
16 И взял старейшин города и терновник пустынный и зубчатые молотильные доски и наказал ими жителей Сокхофа;
Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada.
17 и башню Пенуэльскую разрушил, и перебил жителей города.
Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.
18 И сказал Зевею и Салману: каковы были те, которых вы убили на Фаворе? Они сказали: они были такие, как ты, каждый имел вид сынов царских.
Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.” Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.”
19 Гедеон сказал: это были братья мои, сыны матери моей. Жив Господь! если бы вы оставили их в живых, я не убил бы вас.
Gideyon ya ce, “Waɗannan’yan’uwana ne,’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.”
20 И сказал Иеферу, первенцу своему: встань, убей их. Но юноша не извлек меча своего, потому что боялся, так как был еще молод.
Da ya juya wajen Yeter, ɗan farinsa, sai ya ce, “Ka kashe su!” Amma Yeter bai zāre takobinsa ba, domin shi yaro ne kawai kuma yana tsoro.
21 И сказали Зевей и Салман: встань сам и порази нас, потому что по человеку и сила его. И встал Гедеон, и убил Зевея и Салмана, и взял пряжки, бывшие на шеях верблюдов их.
Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.
22 И сказали Израильтяне Гедеону: владей нами ты и сын твой и сын сына твоего, ибо ты спас нас из руки Мадианитян.
Isra’ilawa suka ce wa Gideyon, “Ka yi mulkinmu, kai, ɗanka da jikanka, domin ka cece mu daga hannun Midiyawa.”
23 Гедеон сказал им: ни я не буду владеть вами, ни мой сын не будет владеть вами; Господь да владеет вами.
Amma Gideyon ya ce musu, “Ni, ko ɗana, ba za mu yi mulkinku ba. Ubangiji ne zai yi mulkinku.”
24 И сказал им Гедеон: прошу у вас одного, дайте мне каждый по серьге из добычи своей. Ибо у неприятелей много было золотых серег, потому что они были Измаильтяне.
Kuma ya ce, “Ina da roƙo guda ɗaya, cewa kowannenku ya ba ni’yan kunne daga rabon ganima.” (Al’adar mutanen Ishmayel ce su sa’yan kunnen zinariya.)
25 Они сказали: дадим. И разостлали одежду и бросали туда каждый по серьге из добычи своей.
Suka ce, “Za mu yi farin cikin ba ka su.” Saboda haka suka shimfiɗa mayafi, kowanne ya sa ɗan kunne ɗaya daga ganimar.
26 Весу в золотых серьгах, которые он выпросил, было тысяча семьсот золотых сиклей, кроме пряжек, пуговиц и пурпуровых одежд, которые были на царях Мадиамских, и кроме золотых цепочек, которые были на шее у верблюдов их.
Nauyin’yan kunnen zinariyar ya kai shekel ɗari goma sha bakwai, ban da kayan ado, abin wuya da tufafin shunayya waɗanda sarakuna Midiyawa suke sawa ko sarƙoƙin da suke wuyar raƙumansu.
27 Из этого сделал Гедеон ефод и положил его в своем городе, в Офре, и стали все Израильтяне блудно ходить туда за ним, и был он сетью Гедеону и всему дому его.
Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko.
28 Так смирились Мадианитяне пред сынами Израиля и не стали уже поднимать головы своей, и покоилась земля сорок лет во дни Гедеона.
Da haka Isra’ilawa suka mallaki Midiyawa ba su kuma sāke tā da kai ba. A zamanin Gideyon ƙasar ta sami zaman lafiya har shekara arba’in.
29 И пошел Иероваал, сын Иоасов, и жил в доме своем.
Yerub-Ba’al ɗan Yowash ya koma gida don yă zauna.
30 У Гедеона было семьдесят сыновей, происшедших от чресл его, потому что у него много было жен.
Yana da’ya’ya saba’in maza da ya haifa, gama yana da mata da yawa.
31 Также и наложница, жившая в Сихеме, родила ему сына, и он дал ему имя Авимелех.
Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek.
32 И умер Гедеон, сын Иоасов, в глубокой старости, и погребен во гробе отца своего Иоаса, в Офре Авиезеровой.
Gideyon ɗan Yowash ya rasu da kyakkyawan tsufa aka kuma binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa a Ofra na mutanen Abiyezer.
33 Когда умер Гедеон, сыны Израилевы опять стали блудно ходить вслед Ваалов и поставили себе богом Ваалверифа;
Ba a daɗe da rasuwar Gideyon ba, sai Isra’ila ta sāke shiga karuwanci suna bauta wa Ba’al. Suka kafa Ba’al-Berit yă zama musu allahnsu ba kuma
34 и не вспомнили сыны Израилевы Господа Бога своего, Который избавлял их из руки всех врагов, окружавших их;
tuna da Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga hannuwan abokan gābansu a kowane gefe ba.
35 и дому Иероваалову, или Гедеонову, не сделали милости за все благодеяния, какие он сделал Израилю.
Suka kāsa nuna alheri ga gidan Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) saboda abubuwa masu alherin da ya yi musu.