< Исаия 18 >
1 Горе земле, осеняющей крыльями по ту сторону рек Ефиопских,
Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush,
2 посылающей послов по морю, и в папировых суднах по водам! Идите, быстрые послы, к народу крепкому и бодрому, к народу страшному от начала и доныне, к народу рослому и все попирающему, которого землю разрезывают реки.
wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba.
3 Все вы, населяющие вселенную и живущие на земле! смотрите, когда знамя поднимется на горах, и, когда загремит труба, слушайте!
Ku dukan mutanen duniya, ku da kuke zama a duniya, sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu, za ku gan shi, sa’ad da kuma aka busa ƙaho, za ku ji shi.
4 Ибо так Господь сказал мне: Я спокойно смотрю из жилища Моего, как светлая теплота после дождя, как облако росы во время жатвенного зноя.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina, kamar ƙuna mai zafi a hasken rana, kamar girgijen raba a lokacin girbi.”
5 Ибо прежде собирания винограда, когда он отцветет, и грозд начнет созревать, Он отрежет ножом ветви и отнимет, и отрубит отрасли.
Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe furanni kuma suka zama’ya’yan inabin da suka nuna, zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa, ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.
6 И оставят все хищным птицам на горах и зверям полевым; и птицы будут проводить там лето, а все звери полевые будут зимовать там.
Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci da kuma namun jeji; tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu, namun jeji kuma za su yi damina a kansu.
7 В то время будет принесен дар Господу Саваофу от народа крепкого и бодрого, от народа страшного от начала и доныне, от народа рослого и все попирающего, которого землю разрезывают реки, - к месту имени Господа Саваофа, на гору Сион.
A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki daga dogayen mutane masu sulɓin jiki, daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba. Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake.