< К Галатам 5 >

1 Итак стойте в свободе, которую даровал нам Христос, и не подвергайтесь опять игу рабства.
Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta.
2 Вот, я, Павел, говорю вам: если вы обрезываетесь, не будет вам никакой пользы от Христа.
Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya.
3 Еще свидетельствую всякому человеку обрезывающемуся, что он должен исполнить весь закон.
Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a.
4 Вы, оправдывающие себя законом, остались без Христа, отпали от благодати,
Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka “baratar” ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri.
5 а мы духом ожидаем и надеемся праведности от веры.
Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci.
6 Ибо во Христе Иисусе не имеет силы ни обрезание, ни необрезание, но вера, действующая любовью.
A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci.
7 Вы шли хорошо: кто остановил вас, чтобы вы не покорялись истине?
Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya?
8 Такое убеждение не от Призывающего вас.
Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne
9 Малая закваска заквашивает все тесто.
Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura.
10 Я уверен о вас в Господе, что вы не будете мыслить иначе; а смущающий вас, кто бы он ни был, понесет на себе осуждение.
Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi.
11 За что же гонят меня, братия, если я и теперь проповедую обрезание? Тогда соблазн креста прекратился бы.
'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje.
12 О, если бы удалены были возмущающие вас!
Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani.
13 К свободе призваны вы, братия, только бы свобода ваша не была поводом к угождению плоти, но любовью служите друг другу.
'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima.
14 Ибо весь закон в одном слове заключается: люби ближнего твоего, как самого себя.
Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; “Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.”
15 Если же друг друга угрызаете и съедаете, берегитесь, чтобы вы не были истреблены друг другом.
Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku.
16 Я говорю: поступайте по духу, и вы не будете исполнять вожделений плоти,
Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba.
17 ибо плоть желает противного духу, а дух - противного плоти: они друг другу противятся, так что вы не то делаете, что хотели бы.
Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba.
18 Если же вы духом водитесь, то вы не под законом.
Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a.
19 Дела плоти известны; они суть: прелюбодеяние, блуд, нечистота, непотребство,
Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi,
20 идолослужение, волшебство, вражда, ссоры, зависть, гнев, распри, разногласия, соблазны, ереси,
bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya,
21 ненависть, убийства, пьянство, бесчинство и тому подобное. Предваряю вас, как и прежде предварял, что поступающие так Царствия Божия не наследуют.
hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba.
22 Плод же духа: любовь, радость, мир, долготерпение, благость, милосердие, вера,
Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya,
23 кротость, воздержание. На таковых нет закона.
tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa.
24 Но те, которые Христовы, распяли плоть со страстями и похотями.
Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi.
25 Если мы живем духом, то по духу и поступать должны.
Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu.
26 Не будем тщеславиться, друг друга раздражать, друг другу завидовать.
Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.

< К Галатам 5 >