< 2-е Коринфянам 4 >
1 Посему, имея по милости Божией такое служение, мы не унываем;
Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba.
2 но, отвергнув скрытные постыдные дела, не прибегая к хитрости и не искажая слова Божия, а открывая истину, представляем себя совести всякого человека пред Богом.
Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah.
3 Если же и закрыто благовествование наше, то закрыто для погибающих,
Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka.
4 для неверующих, у которых бог века сего ослепил умы, чтобы для них не воссиял свет благовествования о славе Христа, Который есть образ Бога невидимого. (aiōn )
A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah. (aiōn )
5 Ибо мы не себя проповедуем, но Христа Иисуса, Господа; а мы - рабы ваши для Иисуса,
Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
6 потому что Бог, повелевший из тьмы воссиять свету, озарил наши сердца, дабы просветить нас познанием славы Божией в лице Иисуса Христа.
Gama Allah shine wanda ya ce, “Haske zai haskaka daga cikin duhu.” Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu.
7 Но сокровище сие мы носим в глиняных сосудах, чтобы преизбыточная сила была приписываема Богу, а не нам.
Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.
8 Мы отовсюду притесняемы, но не стеснены; мы в отчаянных обстоятельствах, но не отчаиваемся;
Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba.
9 мы гонимы, но не оставлены; низлагаемы, но не погибаем.
Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba.
10 Всегда носим в теле мертвость Господа Иисуса, чтобы и жизнь Иисусова открылась в теле нашем.
Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma.
11 Ибо мы живые непрестанно предаемся на смерть ради Иисуса, чтобы и жизнь Иисусова открылась в смертной плоти нашей,
Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka.
12 так что смерть действует в нас, а жизнь в вас.
Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku.
13 Но, имея тот же дух веры, как написано: я веровал и потому говорил, и мы веруем, потому и говорим,
Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: “Na gaskata, saboda haka na furta.” Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada.
14 зная, что Воскресивший Господа Иисуса воскресит через Иисуса и нас и поставит перед Собою с вами.
Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa.
15 Ибо все для вас, дабы обилие благодати тем большую во многих произвело благодарность во славу Божию.
Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah.
16 Посему мы не унываем; но если внешний наш человек и тлеет, то внутренний со дня на день обновляется.
Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin.
17 Ибо кратковременное легкое страдание наше производит в безмерном преизбытке вечную славу, (aiōnios )
Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa. (aiōnios )
18 когда мы смотрим не на видимое, но на невидимое: ибо видимое временно, а невидимое вечно. (aiōnios )
Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne. (aiōnios )