< 1-е Коринфянам 4 >
1 Итак каждый должен разуметь нас, как служителей Христовых и домостроителей таин Божиих.
Ga yadda za ku dauke mu, kamar bayin Almasihu da kuma masu rikon asiran Allah.
2 От домостроителей же требуется, чтобы каждый оказался верным.
Hade da wannan, ana bukatar wakilai su zama amintattu.
3 Для меня очень мало значит, как судите обо мне вы или как судят другие люди; я и сам не сужу о себе.
Amma a gare ni, karamin abu ne ku yi mani shari'a, ko a wata kotu irin ta mutane. Gama bani yi wa kaina shari'a.
4 Ибо хотя я ничего не знаю за собою, но тем не оправдываюсь; судия же мне Господь.
Ban sani ko akwai wani zargi a kaina ba, amma wannan bai nuna cewa bani da laifi ba. Ubangiji ne mai yi mani shari'a.
5 Посему не судите никак прежде времени, пока не придет Господь, Который и осветит скрытое во мраке и обнаружит сердечные намерения, и тогда каждому будет похвала от Бога.
Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah.
6 Это, братия, приложил я к себе и Аполлосу ради вас, чтобы вы научились от нас не мудрствовать сверх того, что написано, и не превозносились один перед другим.
Yan'uwa, ina dora wadannan ka'idoji a kaina da Afollos domin ku, yadda ta wurin mu za ku koyi ma'anar maganar nan cewa, “kada ku zarce abin da aka rubuta.” Ya zama haka domin kada waninku ya kumbura yana nuna fifiko ga wani akan wani.
7 Ибо кто отличает тебя? Что ты имеешь, чего бы не получил? А если получил, что хвалишься, как будто не получил?
Gama wa yaga bambanci tsakanin ku da wasu? Me kuke da shi da ba kyauta kuka karba ba? Idan kyauta kuka karba, don me kuke fahariya kamar ba haka ba ne?
8 Вы уже пресытились, вы уже обогатились, вы стали царствовать без нас. О, если бы вы и в самом деле царствовали, чтобы и нам с вами царствовать!
Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku.
9 Ибо я думаю, что нам, последним посланникам, Бог судил быть как бы приговоренными к смерти, потому что мы сделались позорищем для мира, для Ангелов и человеков.
A tunanina, mu manzanni, Allah ya sa mu a jerin karshe kamar mutanen da aka zartar wa hukuncin mutuwa. Mun zama abin kallo ga duniya, ga mala'iku, ga mutane kuma.
10 Мы безумны Христа ради, а вы мудры во Христе; мы немощны, а вы крепки; вы в славе, а мы в бесчестии.
Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ganin mu marasa daraja, ku kuwa masu daraja.
11 Даже доныне терпим голод и жажду, и наготу и побои, и скитаемся,
Har zuwa wannan sa'a, muna masu yunwa da kishi, marasa tufafi masu kyau, mun sha kazamin duka, kuma mun zama marasa gidaje.
12 и трудимся, работая своими руками. Злословят нас, мы благословляем; гонят нас, мы терпим;
Mun yi fama sosai, muna aiki da hanuwanmu. Sa'adda an aibata mu, muna sa albarka. Sa'adda an tsananta mana, muna jurewa.
13 хулят нас, мы молим; мы как сор для мира, как прах, всеми попираемый доныне.
Sa'adda an zage mu, muna magana da nasiha. Mun zama, kuma har yanzu an dauke mu a matsayin kayan shara na duniya da abubuwa mafi kazamta duka.
14 Не к постыжению вашему пишу сие, но вразумляю вас, как возлюбленных детей моих.
Ban rubuta wadannan abubuwa domin in kunyata ku ba, amma domin in yi maku gyara kamar kaunatattun yayana.
15 Ибо, хотя у вас тысячи наставников во Христе, но не много отцов; я родил вас во Христе Иисусе благовествованием.
Ko da kuna da masu riko dubu goma a cikin Almasihu, ba ku da ubanni da yawa. Gama ni na zama ubanku cikin Almasihu Yesu ta wurin bishara.
16 Посему умоляю вас: подражайте мне, как я Христу.
Don haka, ina kira gare ku da ku zama masu koyi da ni.
17 Для сего я послал к вам Тимофея, моего возлюбленного и верного в Господе сына, который напомнит вам о путях моих во Христе, как я учу везде во всякой церкви.
Shiyasa na aiko Timoti wurin ku, kaunatacce da amintaccen dana cikin Ubangiji. Zai tunashe ku hanyoyina cikin Almasihu, kamar yadda nake koyar da su ko'ina da kowace Ikilisiya.
18 Как я не иду к вам, то некоторые у вас возгордились;
Amma yanzu, wadansun ku sun zama masu fahariya, suna yin kamar ba zan zo wurinku ba.
19 но я скоро приду к вам, если угодно будет Господу, и испытаю не слова возгордившихся, а силу,
Amma zan zo gare ku ba da dadewa ba, idan Ubangiji ya nufa. Sannan zan san fiye da maganar masu fahariya, amma kuma zan ga ikonsu.
20 ибо Царство Божие не в слове, а в силе.
Gama Mulkin Allah ba magana kadai ya kunsa ba, amma ya kunshi iko.
21 Чего вы хотите? c жезлом придти к вам или с любовью и духом кротости?
Me kuke so? In zo wurin ku da sanda ne ko kuwa da kauna da ruhun nasiha?