< João 18 >
1 Havendo Jesus dito estas coisas, saiu com seus discípulos para além do ribeiro de Cedrom, onde havia um jardim, em que ele entrou ele, e seus discípulos.
Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa.
2 E também Judas, o que o traía, conhecia aquele lugar; porque muitas vezes se juntara ali Jesus com seus discípulos.
Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa.
3 Tendo Judas, pois, tomado a tropa e [alguns dos] oficiais dos sacerdotes e dos fariseus, veio ali com lanternas, tochas, e armas.
Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai.
4 Sabendo pois Jesus todas as coisas que viriam sobre ele, adiantou-se, e disse-lhes: A quem buscais?
Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, ''Wa kuke nema''
5 Responderam-lhe: A Jesus Nazareno. Disse-lhes Jesus: Eu sou. E Judas, o que o traía, também estava com eles.
Suka amsa masa su ka ce, ''Yesu Banazare'' Yesu yace masu, Ni ne'' Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin.
6 Quando pois lhes disse: Eu sou, voltaram para trás, e caíram em terra.
Sa'adda ya ce masu, ''Ni ne'', suka koma da baya, suka fadi a kasa.
7 Voltou pois a lhes perguntar: A quem buscais? E eles disseram: A Jesus Nazareno.
Ya sake tambayarsu kuma, ''Wa ku ke nema?'' su ka ce, ''Yesu Banazare.''
8 Respondeu Jesus: Já vos disse que eu sou. Portanto se buscais a mim, deixai a estes irem.
Yesu ya amsa, ''Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;''
9 Para que se cumprisse a palavra, que tinha dito: Dos que me deste, a nenhum deles perdi.
Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.''
10 Simão Pedro, pois, que tinha espada, puxou dela, e feriu ao servo do sacerdote, e cortou a sua orelha direita. E era o nome do servo Malco.
Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne.
11 Disse pois Jesus a Pedro: Põe tua espada na bainha; não beberei eu o copo que o Pai tem me dado?
Yesu ya ce wa Bitrus, ''Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'?
12 O grupo de soldados pois, e o comandante, e os oficiais dos judeus juntamente tomaram a Jesus, e o amarraram.
Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi.
13 E o levaram primeiramente a Anás, porque era sogro de Caifás, o qual era o sumo sacerdote daquele ano.
Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan.
14 E era Caifás o que havia aconselhado aos judeus de que convinha que um homem morresse pelo povo.
Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane.
15 E Simão Pedro seguia a Jesus com outro discípulo. E este discípulo era conhecido do sacerdote, e entrou com Jesus no pátio do sumo sacerdote.
Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu;
16 E Pedro estava fora à porta. Saiu pois o outro discípulo, que era conhecido do sacerdote, e falou à porteira, e pôs dentro a Pedro.
Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
17 Disse pois a serva porteira a Pedro: Não és tu também dos discípulos deste homem? Disse ele: Não sou.
Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, ''kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?'' Yace ''bani ba.''
18 E estavam [ali] os servos, e os oficiais, que haviam feito [uma fogueira de] brasas, porque fazia frio, e se esquentavam. Estava Pedro com eles, e se esquentava.
To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin.
19 Perguntou pois o sacerdote a Jesus sobre seus discípulos, e sobre sua doutrina.
babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma.
20 Jesus lhe respondeu: Eu abertamente falei ao mundo; eu sempre ensinei na sinagoga e no Templo, onde os Judeus de todos os lugares se juntam, e nada falei em oculto.
Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba.
21 Por que perguntas a mim? Pergunta aos que o ouviram, que é o que lhes falei. Eis que estes sabem que é o que tenho dito.
Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada.
22 E dizendo ele isto, um dos oficiais, que ali estava, deu a Jesus uma bofetada, dizendo: Assim respondes ao sumo sacerdote?
Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, ''Kana amsa wa babban firist haka.''
23 Respondeu-lhe Jesus: Se falei mal, dá testemunho do mal; e se bem, por que me feres?
Yesu ya amsa masa yace, ''Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?''
24 (Pois Anás o mandara amarrado ao sumo sacerdote Caifás.)
Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist.
25 E Simão Pedro estava ali, e se esquentava; disseram-lhe pois: Não és tu também de seus discípulos? Ele negou, e disse: Não sou.
To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, ''Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?'' Sai yayi musu yace, ''A'a, ba na ciki.''
26 Disse um dos servos do sacerdote, parente daquele a quem Pedro cortara a orelha: Eu não te vi no jardim com ele?
Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, ''Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?
27 Pedro negou pois outra vez, e logo cantou o galo.
Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara.
28 Levaram pois a Jesus de Caifás para o tribunal. E era pela manhã; e não entraram no tribunal, para que não se contaminassem, mas que pudessem comer a Páscoa.
Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa.
29 Saiu pois Pilatos até eles fora, e disse: Que acusação trazeis contra este homem?
Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, 'Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan?'
30 Responderam, e disseram-lhe: Se este não fosse malfeitor, não o entregaríamos a ti.
''Sai suka amsa suka ce, ''idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka''
31 Disse-lhes pois Pilatos: Tomai-o vós, e julgai-o segundo vossa lei. Disseram-lhe pois os Judeus: Não nos é lícito matar a alguém.
bilatus yace masu, ''Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!'' Sai Yahudawa su kace masa, ''Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa.''
32 Para que se cumprisse a palavra de Jesus, que tinha dito, dando a entender de que morte havia de morrer.
Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33 Então Pilatos voltou a entrar no tribunal, e chamou a Jesus, e disse-lhe: És tu o Rei dos Judeus?
Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, ''kai sarkin Yahudawa ne?''
34 Respondeu-lhe Jesus: Tu dizes isso de ti mesmo, ou outros te disseram de mim?
Yesu ya amsa, '' wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?''
35 Pilatos respondeu: Por acaso eu sou Judeu? Tua gente e os chefes dos sacerdotes te entregaram a mim; que fizeste?
Bilatus ya amsa “Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?'' Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. ''Me ka yi?''
36 Respondeu Jesus: Meu Reino não é deste mundo; se meu Reino fosse deste mundo, meus trabalhadores lutariam, para que eu não fosse entregue aos Judeus; mas agora meu Reino não é daqui.
Yesu ya amsa, ''Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba.''
37 Disse-lhe pois Pilatos: Logo tu és Rei? Respondeu Jesus: Tu dizes que eu sou Rei. Para isto eu nasci, e para isto vim ao mundo: para dar testemunho à verdade. Todo aquele que é da verdade ouve minha voz.
Sai Bilatus yace masa, ''Wato ashe, sarki ne kai?'' Yesu ya amsa, ''Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata.''
38 Disse-lhe Pilatos: O que é a verdade? E havendo dito isto, voltou a sair aos Judeus, e disse-lhes: Nenhum crime acho nele.
Bilatus yace masa, ''Menene gaskiya?'' Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, ''Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba.
39 Mas vós tendes por costume que eu vos solte um pela páscoa. Quereis pois que vos solte ao Rei dos Judeus?
Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?''
40 Voltaram pois todos a clamar, dizendo: Não a este, mas a Barrabás! E Barrabás era um ladrão.
Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, ''A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas.'' Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.