< Gálatas 3 >

1 Ó insensatos Gálatas! quem vos fascinou para não obedecerdes à verdade, vós, perante os olhos de quem Jesus Cristo foi já representado, como crucificado entre vós?
Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba?
2 Só quizera saber isto de vós: recebestes o espírito pelas obras da lei ou pela pregação da fé?
Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji?
3 Sois vós tão insensatos que, tendo começado pelo espírito, acabeis agora pela carne?
Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki?
4 Será em vão que tenhais padecido tanto? Se é que também foi em vão.
Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne?
5 Aquele pois que vos dá o espírito, e que obra maravilhas entre vós, fa-lo pelas obras da lei, ou pela pregação da fé?
To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya?
6 Assim como Abraão creu em Deus, e isso lhe foi imputado como justiça.
Ibrahim ''ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci.''
7 Sabei pois que os que são da fé são filhos de Abraão.
Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne.
8 Ora, tendo a escritura previsto que Deus havia de justificar pela fé os gentios, anunciou primeiro o evangelho a Abraão, dizendo: Todas as nações serão benditas em ti.
Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: ''A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka.''
9 De sorte que os que são da fé são benditos com o crente Abraão.
Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya.
10 Todos aqueles pois que são das obras da lei estão debaixo da maldição; porque escrito está: Maldito todo aquele que não permanecer em todas as coisas que estão escritas no livro da lei, para fazê-las.
La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, ''La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka.”'
11 E é evidente que pela lei ninguém será justificado diante de Deus, porque o justo viverá pela fé
Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin ''Mai adalci zai rayu ta bangaskiya.''
12 Ora a lei não é da fé; mas o homem que fizer estas coisas por elas viverá.
Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, “Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a.''
13 Cristo nos resgatou da maldição da lei, fazendo-se maldição por nós; porque está escrito: Maldito todo aquele que for pendurado no madeiro;
Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, ''La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace.''
14 Para que a benção de Abraão chegasse aos gentios por Jesus Cristo, e para que pela fé nós recebamos a promessa do espírito.
Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya.
15 Irmãos, como homem falo; se o concerto de um homem for confirmado, ninguém o anula nem lhe acrescenta.
'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi.
16 Ora as promessas foram feitas a Abraão e à sua posteridade. Não diz: E às posteridades, como falando de muitas, mas como de uma só: E à tua posteridade; a qual é Cristo.
Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, ''ga zuriya ba'' da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, ''ga zuriyar ka,'' wanda shine Almasihu.
17 Mas digo isto: Que o concerto, anteriormente confirmado por Deus em Cristo, a lei, que veio quatrocentos e trinta anos depois, não inválida, de forma a abolir a promessa.
Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya.
18 Porque, se a herança provém da lei, logo não provém já da promessa: porém Deus pela promessa a deu gratuitamente a Abraão.
Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari.
19 Logo, para que é a lei? Foi ordenada por causa das transgressões, até que viesse a posteridade a quem a promessa tinha sido feita; e foi posta pelos anjos na mão de um medianeiro.
Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici.
20 Ora o medianeiro não é de um, mas Deus é um
Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne.
21 Logo, a lei é contra as promessas de Deus? De nenhuma sorte; porque, se dada fosse uma lei que pudesse vivificar, a justiça, na verdade, seria pela lei.
Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a.
22 Mas a escritura encerrou tudo debaixo do pecado, para que a promessa pela fé em Jesus Cristo fosse dada aos crentes.
A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta.
23 Porém, antes que a fé viesse, estávamos guardados debaixo da lei, e encerrados para aquela fé que se havia de manifestar.
Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya.
24 De maneira que a lei nos serviu de aio, para nos conduzir a Cristo, para que pela fé fossemos justificados.
Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya.
25 Mas, depois que a fé veio, já não estamos debaixo de aio.
Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora.
26 Porque todos sois filhos de Deus pela fé em Cristo Jesus.
Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu.
27 Porque todos quantos fostes batizados em Cristo já vos revestistes de Cristo.
Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu.
28 Nisto não há judeu nem grego; não há servo nem livre; não há macho nem fêmea; porque todos vós sois um em Cristo Jesus.
Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu.
29 E, se sois de Cristo, logo sois descendência de Abraão, e herdeiros conforme a promessa.
Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.

< Gálatas 3 >