< Marcos 16 >

1 E, passado o sabbado, Maria Magdalena, e Maria, mãe de Thiago, e Salomé, compraram aromas para irem ungil-o.
Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza.
2 E, no primeiro dia da semana, foram ao sepulchro, de manhã cedo, ao nascer do sol;
Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana.
3 E diziam umas ás outras: Quem nos revolverá a pedra da porta do sepulchro?
Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?”
4 E, olhando, viram que já a pedra estava revolvida; porque era muito grande.
Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma.
5 E, entrando no sepulchro, viram um mancebo assentado á direita, vestido de uma roupa comprida, branca; e ficaram espantadas.
Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki.
6 Porém elle disse-lhes: Não vos assusteis; buscaes a Jesus Nazareno, que foi crucificado; já resuscitou, não está aqui; eis aqui o logar onde o pozeram.
Sai ya ce masu, “Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi.
7 Porém ide, dizei a seus discipulos, e a Pedro, que elle vae adiante de vós para a Galilea; ali o vereis, como elle vos disse.
Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku.”
8 E, saindo ellas apressadamente, fugiram do sepulchro, porque estavam possuidas de temor e assombro; e nada diziam a ninguem, porque temiam.
Suka fita daga cikin kabarin da gudu suna rawar jiki da mamaki, ba su cewa kowa komai ba domin suna jin tsoro.
9 (note: The most reliable and earliest manuscripts do not include Mark 16:9-20.) E Jesus, tendo resuscitado na manhã do primeiro dia da semana, appareceu primeiramente a Maria Magdalena, da qual tinha expulsado sete demonios.
(note: The most reliable and earliest manuscripts do not include Mark 16:9-20.) Da safiyar ranar farko ta mako ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magadaliya wadda ya kori aljannu guda bakwai daga cikinta.
10 E, partindo ella, annunciou-o áquelles que tinham estado com elle, os quaes estavam tristes, e chorando.
Sai ta tafi ta shaida wadanda suke tare da shi suke makoki da kuka.
11 E, ouvindo elles que vivia, e que tinha sido visto por ella, não o creram.
Sai suka ji cewa ya tashi kuma ta ganshi, amma basu gaskata ba.
12 E depois manifestou-se n'outra fórma a dois d'elles, que iam de caminho para o campo.
Bayan wadannan al'amura ya bayana kansa ta wata siffa ga mutum biyu sa'ilin da suke tafiya akan hanya.
13 E, indo estes, annunciaram-n'o aos outros, mas nem ainda estes creram.
Sai suka tafi suka gaya wa sauran almajiransa, duk da haka basu gaskata ba.
14 Finalmente appareceu aos onze, estando elles assentados juntamente, e lançou-lhes em rosto a sua incredulidade e dureza de coração, por não haverem crido nos que o tinham visto já resuscitado.
Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu.
15 E disse-lhes: Ide por todo o mundo, prégae o evangelho a toda a creatura:
Sai ya umarcesu cewa “Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta.
16 Quem crêr e fôr baptizado será salvo; mas quem não crêr será condemnado.
Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka.
17 E estes signaes seguirão aos que crêrem: Em meu nome expulsarão os demonios; fallarão novas linguas:
Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna.
18 Pegarão nas serpentes; e, se beberem alguma coisa mortifera, não lhes fará damno algum; e porão as mãos sobre os enfermos, e os sararão.
Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa.”
19 Ora o Senhor, depois de lhes ter fallado, foi recebido acima no céu, e assentou-se á direita de Deus.
Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah.
20 E elles, tendo partido, prégaram por todas as partes, cooperando com elles o Senhor, e confirmando a palavra com os signaes que se seguiram. Amen.
Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.

< Marcos 16 >