< 2 Coríntios 10 >
1 Além d'isto, eu, Paulo, vos rogo, pela mansidão e benignidade de Christo, eu que, na verdade, quando presente entre vós, sou humilde, porém, ausente, ousado para comvosco;
Ni, Bulus, da kaina nake rokon ku, ta wurin tawali'u da nasihar Almasihu. Ina da saukin kai yayinda nake gaban ku, amma ina da gabagadi a gare ku yayinda ba na tare da ku.
2 Rogo-vos pois que, quando estiver presente, não me veja obrigado a usar com confiança da ousadia que se me attribue ter com alguns, que nos julgam, como se andassemos segundo a carne.
Ina rokon ku, yayinda nake gabanku, ba ni so in zama mai tsaurin hali. Amma ina ganin zan bukaci zama mai gabagadi sa'adda nake tsayayya da su wadanda ke zaton muna zama bisa ga jiki.
3 Porque, andando na carne, não militamos segundo a carne.
Kodashike dai muna tafiya bisa jiki, ba ma yin yaki bisa jiki.
4 Porque as armas da nossa milicia não são carnaes, mas sim poderosas em Deus, para destruição das fortalezas;
Domin makaman da muke yaki da su ba na jiki ba ne. Maimakon haka, makamai ne na Allah da ke da ikon rushe ikokin shaidan. Suna kawar da dukan gardandamin da ke kawo kaucewa.
5 Destruindo os conselhos, e toda a altivez que se levanta contra o conhecimento de Deus, e levando captivo todo o entendimento á obediencia de Christo.
Muna kuma rushe duk wani abinda ke gaba da sanin Allah. Muna kuma kama kowanne tunani zuwa biyayya ga Almasihu.
6 E estando promptos para vingar toda a desobediencia, quando fôr cumprida a vossa obediencia.
Muna kuma shirye mu hukunta kowanne irin aiki na rashin biyayya, da zarar biyayyarku ta tabbata.
7 Olhaes para as coisas segundo a apparencia? Se alguem confia de si mesmo que é de Christo, pense outra vez isto comsigo, que, assim como elle é de Christo, tambem nós somos de Christo.
Dubi abin da aka sa a bayyane a gaban ku. In har wani ya tabbata shi na Almasihu ne, bari fa ya tunatar da kansa cewa kamar yadda shi na Almasihu ne, hakanan muma muke.
8 Porque, ainda que eu me glorie mais alguma coisa do nosso poder, o qual o Senhor nos deu para edificação, e não para vossa destruição, não me envergonharei,
Ko da zan yi fahariya da ikon da muke dashi, wanda Ubangiji ya ba mu domin mu inganta ku, ba domin mu rushe ku ba, ba zan ji kunya ba.
9 Para que não pareça como se quizera intimidar-vos por cartas.
Ba na so ya zama kamar ina firgita ku ne da wasikuna.
10 Porque as cartas, dizem, são graves e fortes, mas a presença do corpo é fraca, e a palavra desprezivel.
Domin wadansu mutane na cewa, “Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne. Kalmominsa ba abin saurare ba ne.”
11 Pense o tal isto, que, quaes somos na palavra por cartas, estando ausentes, taes seremos tambem por obra, estando presentes.
Bari wadannan mutane su sani cewa abinda muke fadi a kalmomin wasikunmu lokacin da ba mu nan, haka za mu yi in muna nan.
12 Porque não ousamos juntar-nos, ou comparar-nos com alguns, que se louvam a si mesmos; porém estes que por si mesmos se medem a si mesmos, e se comparam comsigo mesmos, estão sem entendimento.
Mu dai ba mu hada kanmu da kowa, ko kuma mu kwatanta kanmu da wadanda ke yabon kansu. Amma yayin da suke gwada kansu da junansu, suke kuma kwatanta kansu da junansu, ba su da ganewa.
13 Porém não nos gloriaremos fóra de medida, mas conforme a medida da regra, medida que Deus nos deu, para chegarmos até vós
Saidai, ba za mu yi fahariya fiye da yadda ya kamata ba. Maimakon haka, za mu yi haka ne gwalgwadon iyakar abinda Allah ya sa muyi, iyakar da takai gareku.
14 Porque não nos estendemos além do que convém, como se não houvessemos de chegar até vós, pois já chegámos tambem até vós no evangelho de Christo:
Gama bamu yi zarbabi ba sa'adda muka kai gareku. Mune na farko da muka kai gare ku da bisharar Almasihu.
15 Não nos gloriando fóra de medida nos trabalhos alheios; antes tendo esperança de que, crescendo a vossa fé, seremos abundantemente engrandecidos entre vós, conforme a nossa regra;
Ba mu yi fahariya fiye da kima game da aikin wasu ba. Maimakon haka, muna fatan bangaskiyar ku ta karu domin bangaren aikin mu ya kara fadada kwarai, kuma a daidai iyakarsa.
16 Para annunciar o evangelho nos logares que estão além de vós, e não em campo de outrem, para nos não gloriarmos no que estava já preparado.
Muna fatan haka, domin mu kai bishara zuwa yankunan da ke gaba da naku. Ba za mu yi fahariya akan aikin da aka yi a yankin wani ba.
17 Porém aquelle que se gloría glorie-se no Senhor.
“Amma bari duk wanda zai yi fahariya, ya yi ta cikin Ubangiji.”
18 Porque não é approvado quem a si mesmo se louva, mas sim aquelle a quem o Senhor louva.
Domin ba wanda ya ke shaidar kansa shine yardajje ba. Maimakon haka, sai dai wanda Ubangiji ke shaidarsa.