< I Koryntian 9 >

1 Izalim nie jest Apostołem? Izalim nie jest wolnym? Izalim Jezusa Chrystusa, Pana naszego nie widział? Izali wy nie jesteście pracą moją w Panu?
Ba ni da’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba?
2 Choćbym innym nie był Apostołem, alem wam jest; albowiem pieczęcią apostolstwa mego wy jesteście w Panu.
Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.
3 Tać jest obrona moja przeciwko tym, którzy mię sądzą.
Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina.
4 Izali nie mamy wolności jeść i pić?
Ba mu da’yancin ci da sha ne?
5 Izali nie mamy wolności wodzić z sobą siostry żony, jako i drudzy Apostołowie i bracia Pańscy, i Kiefas?
Ba mu da’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi?
6 Izali ja tylko i Barnabasz nie mamy wolności, abyśmy nie pracowali?
Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai?
7 Któż kiedy służy żołnierkę swoim kosztem? Któż sadzi winnicę, a owocu jej nie pożywa? Albo któż trzodę pasie, a mleka trzody nie pożywa?
Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa?
8 Izali to obyczajem ludzkim mówię? Izali i zakon tegoż nie mówi?
Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba?
9 Albowiem w zakonie Mojżeszowym napisano: Nie zawiążesz gęby wołowi młócącemu; izali się Bóg o woły stara?
Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka?
10 Czyli zgoła dla nas to mówi? Albowiem dla nas to napisano; gdyż w nadziei ma orać ten, co orze, a kto młóci w nadziei, nadziei swojej ma być uczestnikiem.
Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin.
11 Ponieważeśmy my wam duchowne dobra siali, wielkaż to, gdybyśmy wasze cielesne żęli?
In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba?
12 Jeźliż insi tej wolności nad wami używają, czemuż nie raczej my? A wszakżeśmy tej wolności nie używali, ale wszystko znaszamy, abyśmy jakiego wstrętu Ewangielii Chrystusowej nie uczynili.
In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
13 Azaż nie wiecie, iż ci, którzy około rzeczy świętych pracują, z świętych rzeczy jadają? a którzy ołtarza pilnują, spólną cząstkę z ołtarzem mają?
Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne?
14 Tak też Pan postanowił tym, którzy Ewangieliję opowiadają, aby z Ewangielii żyli.
Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.
15 Alem ja nic z tych rzeczy nie używał. I nie pisałem tego, aby się tak przy mnie działo; bo mnie daleko lepiej umrzeć, niżby kto przechwalanie moje miał próżnem uczynić.
Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama.
16 Bo jeźli Ewangieliję opowiadam, nie mam się czem chlubić, gdyż ta powinność na mnie leży; a biada mnie, jeźlibym Ewangielii nie opowiadał.
Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!
17 Albowiem jeźli to dobrowolnie czynię, mam zapłatę; jeźli poniewolnie, szafarstwa mi powierzono.
In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne.
18 Jakąż tedy mam zapłatę? Abym Ewangieliję opowiadając, bez nakładu wystawił Ewangieliję Chrystusową, na to, żebym źle nie używał wolności mojej przy Ewangielii.
To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da’yancina cikin wa’azin ba.
19 Albowiem będąc wolnym od wszystkich, samegom siebie uczynił niewolnikiem wszystkim, abym ich więcej pozyskał.
Ko da yake ina da’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa.
20 I stałem się Żydom jako Żyd, abym Żydów pozyskał; a tym, którzy są pod zakonem, jakobym był pod zakonem, abym tych, którzy są pod zakonem, pozyskał;
Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka.
21 Tym, którzy są bez zakonu, jakobym bez zakonu, (nie będąc bez zakonu Bogu, ale będąc pod zakonem Chrystusowi), abym pozyskał tych, którzy są bez zakonu.
Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.
22 Stałem się mdłym jako mdły, abym mdłych pozyskał. Wszystkim stałem się wszystko, abym przecię niektórych zbawił.
Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.
23 A to czynię dla Ewangielii, abym się jej stał uczestnikiem.
Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
24 Azaż nie wiecie, iż ci, którzy w zawód bieżą, wszyscyć więc bieżą, lecz jeden zakład bierze? Także bieżcie, abyście otrzymali.
Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada.
25 A każdy, który się potyka, we wszystkiem się powściąga, onić wprawdzie, aby wzięli koronę skazitelną, ale my nieskazitelną.
Duk’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.
26 Ja tedy tak bieżę, nie jako na niepewne; tak szermuję, nie jako wiatr bijąc.
To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba.
27 Ale karzę ciało moje i w niewolę podbijam, abym snać inszym każąc, sam nie był odrzucony.
A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

< I Koryntian 9 >